ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

    ▶3⃣7⃣

ina so nayi amfani da wannan ‘yar damar wajen miqa jinjinar ban girma tare da ddu’o’i na fatan alkahairi wajen jajirtaccen dan kishin qasa da al’ummarsa BARRISTER ABDU BULAMA BAKARTI duk da cewa ban masa sanin ido da ido ba saidai tarin gaskiya amana taimakonsa da jajircewa kan qasarshi da garinsa ya kewaye kunnuwanmu,ina tare da duk wani jajirtacce mai gaskiya da amana dan kishin qasa da al’ummarsa,ubangiji yayi maka jagora ya tsare gabanka da bayanka,ya qara yawaita mana irinku cikin wannan alumma tamu dake fagamniya cikin wani irin hali,Allah yayi ruqo da hannayenka ya dorar da kai kan gaskiya har abada ameen suma ameen

Kanta bisa kafadar mamin tana rabza kuka tamkar wadda zasuyi rabuwar har ABADA,sai yanzu take kuma jin zugin rabuwa da mamin,tabbas sabo turken wawa ne,ita kata mamin zuciyarta a karye take ta kasa cewa komai,tanajin zatayi asarar diyarta ne guda zata rabu da ita,da qyar tayi,conrtolling kanta kafin,su tsaya suyi sallama
”naso a gudanar da komai da ni maryam,saidai ga yadda lamarin Allah ya kasance,date din bikinku da abdallah yazo daya,kinga ma ko a yanzun gidan ya fara cika da mutane wasu ma rabonsu da gidan nan an jima,kinga bazan iya tsallakesu ba na fita wani guri ba,amma nayi miki alqawarin bayan komai ya lafa wuni guda zanzo nayi a gidanki,hakanan zan dinga dubaki akai akai da yardar Allah”

kafin tace komai muryar abdallah ta ratso falon yana kiran mamin
”gani nan abdallah”
da azamarsa ya shigo hannunshi daya riqe da leda baqa mai kauri mai dauke da tambarin wani gurin saida kayan maza na ado,daya hannun kuma rafar yan dubu dubu ce dauri biyu,cikin shigar qana nan kaya yake,sai ya sake wani dan banzan kyau,farar fatar nan tayi luf da ita tamkar rainon larabawa,ko dama can yafi yanayi da su din sam sai ka rantse babu abinda ya hadashi da nijeria ,sai ya danyi turus yna dubansu
”qaraso mana abdallah,ya ake ciki?”
ya qaraso ya zauna gefanta
”mami duka guest house din guda biyu sunyi kadan,yanzun dai hisham ya samar ma ragowar mutanen hotel”
”yayi kyau hakan,sai ayi total abiya kudin kwanakin da zasuyi da abincin da zasu ci basai an yi jigilar kai musu daga nan ba”
‘to”yace yana dora mata daurin kudaden kan cinyarta
”wannan fa na meye?”
”wani abokin aikina ne ya bani gudun mawarshi…….”yayi maganar yana qiqarin zaro wayarshi daga aljihu wadda keta faman ringing,ya kara a kunnenshi kana ya niqe tsaye yana fadin
”gani nan zuwa”yadan dubi nami yana yin gaba
”mami ina zuwa”
”uhm,yanzu haka abincin na da nasa aka kaima baka ciba,kadai kula da cikinka abdallah”
”ok mami”ya fada yana mata murmushi gami da qarasa ficewa a gurguje

nasiha ta mata sosai irin ta ‘ya da mahaifiya kafin ta saka driver ya kaita zuwa gidan cikin kuka da kewar rabuwa da juna
ita ta ruqota suka dinga tsallake mutanen da suka fara cika gidan ta rakata har bakin motar sai da suka fice kana ta juya ta koma ciki

????????????????????????

Tun lokacin da idanunsu sukayi tozali da katin daurin auren abdallan hankalinsu yayi qololuwar tashi
”wacce irin hasara nuke shirin tafkawa haka,me kuke tunanin zai faru matuqar muka bar abdallah yayi auren nan,cikin watanni tara ko goma da yin surensu matarshi kan iya haihuwa,zata iya kasancewa ta haifi namiji ma,wannan shike nuna munyi bankwana da cikae burinmu?”

cewar nene dake faman safa da marwa,can cikin dakinsu zahariyya da zubaida kuwa kowa da abinda ya dameshi,zahariyya irin tunanin nene take,ba qaramin tashin hankali take ciki ba,burin da take da shi ya girme mata,yau idan abdallah yayi aure daidai yake da nisanta da dukiyar da suke kwadayin zareta daga hannun mamallakanta su su amfana da roman nata.

Afusace ta kalli zubaida dake zaune a cure can quryar gadon tana ta faman surfafa kuka wanda tunda labarin auren ya isa kunnenta itama ta hana kanta sukuni,kuka take tuquru kamar ba gobe,udanunta duka akumbure suke sun ui luhu luhu sosai daga jiya zuwa yau
”dalla malama ki wa mutane shiru,banza shashasha mara kishin kanta bare yan uwanta,yasan dake din ai ya zabi ya auri wata ba’a gabanshi kike amma ke kin quntata rayuwarki saboda shi”

dama a fusace take maganar zahariyyan sai ta qara tunzurata
”anqi ayi shirun bazanyi shiru ba,kece babbar shashsha da bakison so na haqiqa ba,babu ruwanki da sha’ani na ehe”sai kuwa zahariyyan tayo kanta a zqbure tana cewa
”ni kike gayawa haka,yau zan nuna miki baya ga shekaru da na fiki na fiki iya rashin mutunci”dambe ne ya sarqe tsakaninsu har nene dak samanta ta jiyo hayaniyarsu ta sauko,da qyar ta iya rabasu tana fadin
”sai ku kashe kanku ai,yan iskan yara marasa hankali da tumani,mazq ku raba abun fada cikin taron mutane”

sai sukayi tsit suna maida numfashi kowacce zuciya iya wuya,nene ta kalli zahariyya tace ”ki sameni a sama”ta juya ta fice ita kuma ta rufa mata baya,gware suka kusa yi da adnan wanda ke qoqarin hawa saman da gaggawa
”lafiyanka kuwa?”nenen ta tambayeshi bayan ta danja baya tana qare masa kallo
”muje sama nene akwai magana”ba tare da kowa ya sake tankawa ba suka duru saman gaba daya

”barin yarinyar gidan nan babban abun farinciki ne a garemu,mun riga da mun gama magana da malam na hayi ya tabbatar min da cewa zai mana aiki ammafa matuqar tana cikin gidan nan babu lallai yayi tasiri,tana da wani irin dafa’i a jikinta tun na kakanni da iyayen kakanninta,tunanin da nake yanzu kenan ta yadda zamu gabatar da aikinmu don auren abdallah ba qaramar barazana bace da faduwa garemu sai ga kuma kyakkyawan labarin da na jima banji irinsa ba,mun gode Allah faduwa tazo mana daidai da zama,yau din nan ba sai gobe ba zamu isa vurin,malam na hayi,kwana daya zamuyi a hanya zuwa jibi zamu dawo ya kama ranar daurin aure kenan ko ana gobe daurin aure?”
ta tambayi,adman,sai da ya danyi tunani kadan sannan yace
”ana gobe daurin aure ne”
”to yayi,kai adnan ka zauna muje da,zahariyya,ka shiga ayi duk wata hidima da kai,banason a fahimci komai,zan sanar da haj bintu qanwar ubanku ce ba lafiya zamuje dubota”

a nan suka gama dukkan wani shiri da tsarinsu kana suka shirya ta gayawa mami abinda ta shirya gaya matan,cikin tausayawa mami tace ayi mata sannu Allah ya qara sauqi,idan sun isa zata kira su sai ta bata ta mata sannu

????????????????????????

tun daga qofar gidan ta soma ganin alamun cika,mutanene maza da mata keta kai kawo,a haka ma ba’afara gudanar da bikin ba kenan ina ga kuma an fara,gefe driver din ya samu yayi parking,akwai sabo tsakaninsu da mutunci da girmama juna duk dacewa ya kusa shekaru hamsin dattijon mutum ne mai hankali da nutsuwa,malam baaba direba ya kalleta bayan ya fito
”to malama meramu(haka yake kiranta sunan diyarahi ce ta fari data rasu),Allah ya sanya alkahairi yasa ayi a sa’a,ayita haquri da rayuwa,mu sai ranar daurin aure idan mun dawo daga na mai gida abdullahi”
kanta a sunkuye tace”na gode sosai baaba,Allah ya nuna mana”ya bude boot din motqr yana cewa
”bari in shigar miki da kayan ko”da sauri ta amshi jakar da ya fara fitowa da ita
”a’ah baaba,ka barshi ga yara zansa su shigar min da su”tayi kirqn yaran maqotan dake zaune can gefe da su wadanda da wasan qasa suke tayi da yan guje gje ganinta yasa suka bar abinda suke suka tsaya kallonta,kiransu tayi kunsan amarya da farinjini a guje suka taho dukkansu har ana rige rigen zuwa,kqn ta qarasa mqganar ma sun fara zundumar kqyqn,nata suna shige mata da su cikin gida,dubu biyar ta qirgo cikin dubu dari biyun da mami ta bata tace ta riqe a hannunta tasan amarya kudi basa zama a hannunta,da fqri qin karba malam baaba yayi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button