ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

an karbo daga abu hurairah Allah ya qara yadda da shi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace: kalmomi guda biyu,masu sauqi akan harshe,mafiya soyuwa agurin ubangij,masu nauyi akan mizanin auna ayyuka SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI,SUBHANALLAHIL AZIM

su biyu cikin falon misalin qarfe goma na dare,mami na bisa computer dinta tana tsara wata saminer da zasu gabatar yayin da maryam ke zaune gefanta tana tayata hira
”abdallah shiru bai dawo ba,halan yau aiki ne ya tasaahi gaba”cewar mami lokacin da take ci gaba da typing
”da alama”maryam tace
mami tadan bar abunda take ta juyo da hanklainta ga maryam
”wai ni kam maryam meye matakin karatunki ne?”
murmushi ta danyi
”degre ce”
”ta daya ko ta biyu?”
dan bude baki tayi alamun mamaki
”a’ah mami,ta dayan dai”
”mai zai hana in maida ke makaranta ki samu wata degree din kan fannin kasuwanci?,na fuskanci kina da amfani matuqa atattare da mu,sa’annan ina buqatar mai kula da kamfanonin abdallah mai amana kamar ke,kamfanoni wadanda ya gada da kuma wadanda ya bude daga baya,ya kike gani maryam zaki iya?”

shiru ta danyi cikin shakku,bata son ta fiya zura kanta cikin harkokin masu hannu da shuni, tana gudun wulaqanci,duk da tayi amanna cewa mami sam ba haka take ba,ta yarda da karamci da kuma son jama’a irin nata,to amma shi uban tafiyar fa wanda sam tasu batazo daya ba?
”yaya ne maryam naji kinyi shiru ko baki da sha’awa?”
girgiza kanta tayi
”a’ah mami,duka abunda kika yanke mami dai dai ne,amma zanso na fara sanar da baba da mama naji me zasu ce akai”
”gaskiyarki,wannan dai dai ne,amma duk da haka ki fara hada min takardunki nasan bazasu qi ba,babu wanda zaiqi ilimi wa dansa,ina da qawa a jami’ar b u k sanate ce so insha Allau babu matsala”

”to mami na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara girma”
”no maryam,diya ta nayiwa kinga babu buqatar godiya”gyada kai tayi fuskarta qunshe da murmushi
sallamar nene ce ta maida hankalinsu bakin qofar,nenen ce kiwa cikin doguwar riga mai zubin buba mai taushi saidai wannan nada hannaye gajeru da alamu shigar barci ce tayi
”maraba da nene”
”yauwa…mami”ta fada tana zama cikin daya daga cikin kujerun falon dake,daura da inda mami da maryam din ke zaune,a mutunce suka gaisa
”zuwa nayi na diba yarona abdallah kwana biyu banjin duriyarsa”nene ta fada tana murmushi

mami ta rufe computer tana cewa
”abdallah na nan qalau aiki ne ya sashi gaba,da wuri yake fita kuma bai shigowa da wuri,yanzun na zancanshi muka gama da maryam”
ta juya ta dubi maryam sai a lokacin ta gaidatakanta na sunkuye a qasa,sam batason kallon idanun natar,haka nan sai taji fargaba ta kamata,second talatin idanunta na kan maryam din tana saqa a kanta kafin ta dauke kabta ta maida ga mami
”lafiyanshi dai qalau ko?”
”lafiya qalau yake”mami ta bata amsa cikin jin dadin tambayar tata,wadda har ga Allah tayi tsammanin ta mata ita ne da zuciya daya

ta miqe tsaye tana cewa
”tiw,ni zan wuce dama abunda na shigo naki kenan,sai da safenku”
”Allah ya bamu alkhairi nene an gode ki gaidamin su zubaidan kwana biyu ma bata leqo min ba,zahariyya dama sai wani abun ya kawota”murmushin yaqe nenen tayi cijin zuciyarta tana cewa
”bintu ki guji ranar gamuwar mu dake,gamon mu dake bazai ma rayuwarki daidai ba”

”abdallah na bani kunya wlh,dubi yadda baiwar Allahn nan ke sonshi take damuwa da shi,amma shi bashi da abun wulaqantawa sai diyarta,idan baiyi wasa ba na kusa masa auren dole”
‘yar qaramar dariya ce ta subucewa maryam
”ai mami ba’a yiwa namiji auren dole”
itama dariyar ta tayata
”to za’a fara kan abdallah”

mintina ashirin basu cika da fitar nene ba abdallan ya shigo,ya sauya shiga ba wadda ya fita da ita bace,indai mami taga hakan to a gajiye ya dawo ya fara shiga sashensa yayi wanka ne
kan table maryam ke serving nashi yayin da shi da mami ke hira jifa jifa,ta kammala tana shirin sauka ta basu guri taji yace
”ke…mene wannan din?”ya fada yana nuna abincin da ido,kafin ta bashi amsa mami ta karbe zancan
”dambun shinkafa ne mana”
ya bata fuska kamar yadda yara keyi ya dubi mami
”gaskiya mami ni bazanci wani abu dambu ba”maryam ta kalli farantin don sake gano aibun dake tattare da dambun da ta bata lokaci a kitchen tana girkawa,dambun shinkafa ne da aka masa hadin vegtables sosai saboda ta sonshi da son gayayyaki,cabbage ne carrot zogale green beans harda gyada da wadatacciyar albasa sai dafaffen nama data yankashi qananu ta zuba a ciki,mamaki tayi cikin zuciyarta duk da bata nuna ba kan fuskarta,ta lura tsirfar da ya tsuro da ita kenan cikin yan kwanakin nan

”amma kaifa dazun kace shi kake sha’awar ci ayi maka?”
”am sorry mami na,dambu ayanzu is too heavy na cishi na kwanta ai sai ya kashe miki ni”
dariya ma ya bata,bata zaci konai ba don yaune ya fara wa marya din a gaban idonta
”is ok,maryam yi haquri kinji taimaka ki sama mishi wani abun mai sauqi da sauri”
”no mami,ni zan zaba akwai abunda nake sha’awar ci”
”uhmm”ta fadi tana kallonshi
”sakwara nakeso miyan agushi”bata fuska mami tayi
”kai lokaci fa ya qure gaskiya ba zata girka ma sakwara a yanzu ba saidai ka barwa gobe”
”tunda kin roqa mata shikenan tamin jallop din supaghetti with serdine”bai qarasa ba ma ta sauka tayi kitchen

girki ba baqonta bane cikin minti ashirin ta kammala ta,tun kafin ta fito qamshi ya soma cika qofofin hancin abdallah amma sai ya dake
”mami,dazu munyi waya da abida,ta ce nan da kwana uku zata zo nijeria”
farinciki sosai maryam ta gani fuskar mami
”masha Allah,gaskiya ta kyauta qwarai kuwa da gaske,kaga ta baka kubya kai da kaqi zuwa”
”to mami me zanje na mata”
”any way dai tunda tace zata zo magaba ta qare,fata na idan tazo din wannan karon konai ya daidaita,canki cankar da kake tayi wa muta ne ta qare”
”haka nake fata,na soma gajiya da qulafucinsu naci da rashin zuciya,inason nima na huta mami na samu peace of mind”

kafadarshi mamin ta buga”ja’iri sai yanzu kasan da hakan…am maryam”
”na’am”
”insha Allahu nan da kwanaki uku zamuyi baquwa abida diyar ambassador muhammad mukhtar kuma idan tazo zata dan zauna da mu na wani dan lokaci,so ya kamata kinga na sanar miki haqqinki ne sa’an nan daura da dakinki zata zauna kinga ke zaki karbi baquncin,ina son kuma a sake tanadin sabbin girki,duk na san ban da matsala dake,ke din ba baya bace”ta qarashe maganar cikin sigar zolaya tana murmushi wa maryam din
murmushin ta maida mata
”insha Allahu mami babu damuwa”

”mami a maida abincin nan kawai kitchen nina qoshi ma”inji abdallah bayan ya gana jagulashi da cokali
harararshi tayi
”baki isa ba ko zaka ci kayi amanshi sai ka ci,maryam tafiyarki kije ki kwanta Allah ya bamu alkhairi,gobe insha Allahu zamu tattauna”sallama ta yi mata tayi shigewarta yayin da mamin ta ja plate din ta soma nado taliyar cikin pork tana cusawa abdallah,shikam ya bude ciki ya dinga diba,dama yana so kasuwa kawai yake kaiwa
”almiri ashe kana ci din kenan shegen girman kai yasa kace baka ci”mami ta fada tana dubanshi
dariya ya qyalqyale da ita ya kanne ido daya
”so nake dama mami ta bani da kanta nasan sai yafi dadi”
”Allah ya shirya min kai abdallah”ta fadi tana murmushi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button