ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

      ▶2⃣

Hundatu ce tayi sallama ta shigo rumfar sanye da unifoam ruwan tsamigaye riga da zani sai farin hijabinta kafadarta rataye da jakar makaranta fara,tana cire takalminta hade da socks tace
”anty maryam ya na ganki yau a gida da wuri?”
dan dafe kanta tayi kadan tace”yau da wuri na kammala aikin ne shi yasa,kuma dama bana jin dadi sosai”
cikin nuna damuwa ta zauna saman kujera
”sannu antin mu,ko na karbo miki magani?”
murmushi tayi har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana
”idan banda abun hindu wanne me chamist za’a samu da uwar ranar nan?”
ta dage gira”haka ne fa anty”
”ki duba locker kusa da gadona akwai paracetamol ki dauko ki sha,tuntuni da kika shigo baki gayamin ba har kika tsaya fada da mutane ko?”

ta karyar da kai ”ayyah maman mu ba haka bane,sallah kinga muka gama yanzun ai”
”dawa antin tayi fada mama?,wannan maras kunyan ne isyaku ko?”
”shine mana”
a fusace ta miqe zata fita maman ta yi kiranta
”ina kuma zaki?”
”mama don Allah ki barni naje naci uwar yaron nan don Allah,yayi matuqar raina yaya maryam,dan iska mara kunya kawai”
”ko da wasa naji kinje gurinsu sai na sabarmiki”
ba haka taso ba amma babu yadda ta iya haka ta wuce daki tana kumbure kumbure ta sauyo unifoam dinta ta dawo dan kitchen dinsu wsnda daki ne gudun tashin hankali suka maida shi kitchen ta zubo musu shinkafa da miya da salad da maman tayi a faranti daya,duka suka sa hannu

hindatu tace”dama zamu samu ruwan sanyi yadda ake zabga ranar nan wlh”
”ai insha Allahu da na dauki albashina,zan siya mana qaramin firji”
cike da doki hindatu tace
”eh wlh yaya”
mama ta dubi maryam din”yanzun maryam ba zaki yiwa kanki fada ba?,bama zancan aure kike ba zancan siyan firji kike ki saka mana,duk yadda mutane ke maganganu tamkar ma ke din baki damu ba maryam?”

duk sai taji abincin ya fice mata a ka,ta sunkuyar da kanta,Allah ne kadai yasan abinda take ji a zuciyarta,itakam tasan ba domin mamanta bata sonta take mata wannan fadan ba,tana yine sabida qauna,ita din ma da za’a tona zuciyarta tabbas babu dadi

????????????????????????

Zaune take cikin rumfar tasu wadda ke da madaidaiciyar yalwa,kujeru ne one sitter two sitter da kuma three sitter masu dan sauqin farashi,falon malale yake da tyles ruwan madara da labulaye suma ruwan madara masu sauqin kudi,sai kayan kallo da suka hada da t.v ta xaune da d.v.d,komai na falon madaidai cine dai dai talaka wanda albashin maryaman ne da qoqarinta ya kai falon ga zama haka

kusan kaf gidan babu muhallin da yakai tsaftar nan,ko yaushe zaka sameshi a goge qal yana qamshin turaren garwashi ko na tsinke,hakan ke qara haddasa qiyayya da kishi mai zafi tsakanin mama amina da sauran abokan zamanta

sanye take da pakistan riga da wando wanda rigar tasa ta kai mata har gwiwa,dan kwalin pakistan dinne daure a kanta,duka hankalinta ta tattarashi kacokam kan wayarta da tayi googling din wasu sabbin girke girke,shirun da dakin da ma gidan baki daya da yayi shi ya qara mata nishadi da fahimtar abunda take karantawa,

sallamar da ta jiyo anayi cikin tsakar gidan ita ta ja hankalinta,ta sauke wayar tana amsawa tare da cewa ”a shigo”
mai sallama ta sake maimaitawa lokacin da take shigowa rumfar tasu,da sauri maryam ta sauke wayar a gefanta fuskarta dauke da murmushin farinciki wandayayi sanadiyyar bayyanar dimple dinta ta miqe
”radiya..saukar yaushe kenan mutanen south africa?”
harara wadda aka kira da radiyan ta cilla mata
”hmmm,babu wani nan,wlh baki da abinda zaki kare kanki da shi,yanzu ma ni ba gunki nazo ba,mama na kawowa jikanta ta ganshi”
”oh ni maryama,laifi baya qaremin,me kuma nayi”ta fada cikin murmushi da dafe kai
harararta dai ta sakeyi”kinfi kowa sanin laifinki maryam,sati na guda da dawowa qasar nan amma ko mai kama da ke ban gani ba,ina dira nigeria kece ta farko da na fara yiwa tex amma ko matsayin reply ban samu ba”

”yanzu dai yo haquri don sonki da annabi ki zauna tukun,don mama bata nan ta tafi kitso”ta fada tana karbe kyakkyawan baby boy din dake sabe a kafadarta,tare suka zauna idon maryam na kan yaron”masha Allah laquwwata illa billah fadil”yana kan kadarta ta shiga kitchen din su ta dauko mata ruwa da lemon sobo cikin fridge din da daqyar ta shawo kan mama da dadin bakin hindatu aka siyoshi suke lemon siyarwa a kuma fita kunyar baqi idan anyi

”bismillah”tace da ita bayan ta tsiyaya mata lemon
”bani dana kawai na wuce”
”haba sister,kada fa ayi mana dariya a ganmu a rana”
”ke kika jawo hakan ai”
”kinsan Allah banga saqonki,ki yarda dani bani da lokaci wallahi yanzu isashshe idan ba weekends ba saboda aiki”
da qyar ta samu ta shawo kan radiya bayan ta mata alqawarin zuwa mata a wannan weekend din wanda daga nan suka fada hirar duniya

radiya ta ajiye glass cup din bayan ta kalli maryam
”maryam har yanzu dai batun aure shiru?”sakin ajiyar zuciya tayi sannan ta tabe baki
”hmmm,barni kawai radiya,samun miji na gari yanzun ya zamo wuya,mazan yanzu duka ‘yan garari ne,yawancinsu ba aure ke kawosu gurinki ba”
”anya maryam,bana manta fa yawan samarin da kike da su tun muna school”
”radiya kenan……manta da wannan,na fada miki yawa yawansu ba don Allah suke sonki ba,sun lallabo ne kawai su kwashi abunda suka kwasa na rasa wannan masifa kamar hadin baki?kamar ni kadai sukewa haka,ke dai ki sani kawai a addu’a radiya”ta qarashe maganar muryarta na dan rawa alamun kuka keson zuwa mata
”shikenan maryam,insha Allahu na miki alqawari ba zan fasa sakaki cikin addu’o’ina ba,komai yayi farko yana da qarshe”

a hankali suka fada wasu hirarrakin nasu a haka maman ta cimma su,tunda ta dauke fadil bata dawo da shi ba sai da zasu tafi,sabulai ta bawa radiyar sinqi biyu da turare,hannu biyu amsa tayi mata godiya sannan maryam ta amsheshi ta biyo radiyan qofar gida don raka ta
”ke da nasir fa muka zo”
cikin mamaki take kallin radiyar”amma baki da mutunci,ki bar bawan Allah a mota duka lokacin nan yana zaman jiranki”
fuska ta yatsina”rabu da shi,fada mukayi da shi sulhu yake nema shi yasa”
”Allah ya shiryeki radiya ”abunda ta samu ta iya fada kenan don sun qaraso gaban motar”

gidan gaba ta shige ta dora mata fadil saman cinyarta suna gaisawa da nasir din
”munfa yi fushi maryam gaskiya”
sassanyan murmushinta tayi”to ayi haquri tunda na wanke kaina next week ina tafe insha Allahu ranan sunday”
”to Allah ya nuna mana”
sallama sukayi ta koma cikin gidan radiyan na jaddada mata ta cika alqawari fa

tana cusa kai gidan suka ci karo da BINTA
dauke da botikin awara zata fita inda aka fi kaurin,maryam dince ta fara ja da baya don tasan bata qi ta bangajeta ta wuce ba,duk da hakan ma dai bata tsira ba daga tsaki da harar da qanwar bayanta ta saba jifanta da su ba koda zasu hada hanya ne sau miliyan

ta rasa me ra tsarewa yaran da iyayensu,gaba daya anbi an cika zukatansu da qinsu,qannenta ne duka amma babu daya dake ganinta da gashi,saidai duk da haka rashin mutunci wani yafi na wani
ga tsantsar rashin tarbiyya da qin karatu da aka dasawa zucoyoyinsu,ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa suka zabawa kansu,da wannan tunanin ta qarasa falonsu ta zube saman kujera tana rowon Allah daukinsa kan halin da take ciki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button