ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

sam basu lura da su ba sai shewa suka ji,inna hadiza nw da binta har da tafawa kamar sa’annin juna
”haka dai za’a qare a boyi boyi”inji inna hadizar,hindatu na shirin maida mata martani maryam ta damqe hannunta ta jata suka fice ba tare da ta bata damar tsayawa sun taya yinsu ba

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:50 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

      ▶????

shiru tayi cikin motar tana maida ajiyar zuciya,zugi take jo tana yi mata
har ga Allah da tana da iko ba zatayi aikinnan ba,sam bai kwanta mata ba ko kadan a rai
”maryam,kiyi haquri kinji,na fuskanci baki son aikin nan,amma ni mai sonki ce maryam,na yadda da tarbiyyarkk,ke yarinyace mai hankali da nitsuwa,idan da nasan zaki cutu a gidan wlh bazan gaba kaiki ba,ki kwantar da hankalinki na tabbatar zaki samu nutsuwa da jin dadi cikin gidan haj hasiyana da dadin mu’amala,insha Allahu ba zaki samu matsala ba,ki cire damuwa a ranki don Allah kinji maryamu”

ta sake sakin ajiyar zuciyar a bayyane ”to msma insha Allah”ita kanta tasan ta fada ne kawai amma Allah ne kadai yasan ranar daina damuwarta,bata taba rabiwa da maman nata ba sai yau

tafiyar mintina kimanin talatin suka iso unguwar,tun daga farkon unguwar zaka gane cewa ba qananan muta ne ke zaune cikinta ba,daga get din farko allo ne mai dan girma dauke da rubutu kamar haka
welcome to millonier quaters

sannu a hankali suke ratsa layukan,layuka ne tsararru tamkar a qasar waje,shuke shuke ne jere reras qofar kowanne gida,hakan sai ya yiwa layin ado ya zamo cike da furanni,layin ya burgeta sosai,duk,da uadda,zuciyarta ke mata babu dadi

qofar wani gida suka ja suka tsaya,dauke yake da madaukakiyar katanga da get mai tsawo da girma,horn tayi har kusan uku kafin wata qaramar qofa ta bude
kallo daya zaka masa ka tabbatar cewa qaqqarfan mutum ne,sanye cikin kaya riga da wando ruwan bula wanda ke alamta unifoarm ne a jikinsa

fuska a hade yake tambayarsu cikin karyayyen turancinsa na brooking
”wa kuke nema?”
haj atika ce ta amsa masa”gurin hajiya muka zo,ta san kuma da zuwan mu”ya sake tambayarta mene sunanta ta gaya mishi
bai sake cewa komai ba ya wangale mamakeken get din motarsu ta fada ciki

gurin parking ne wanda yake cike da motoci na alfarma a qalla guda goma,haj atika ta raba tata gefe kana suka fito,sunyi tafiya ta kusan minti biyar kafin su cimma dogon valcony din dake fuskantarsu wanda lullube yake da nau’in furanni kala kala masu qamshi da kyawun kaloli,qofa ce mai fadi cikin valcony din wanda suna shiga ta kaisu ga tafkeken falo wanda ya lamushe rukunin kujeru har set biyar saboda girmanshi

iya qawatuwa an qawata falon iya ganin mai kallo,saidai kawai na barwa mai karatu ya siffanta shi iya yadda zai iya,shiru falon yake sai qamshin freshner da ya gauraye falon da na a.c

kuyi haquri da wannan don Allah,ku bini bashi gobe uxiri ya riqeni

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:50 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
???? ▶1⃣1⃣

   tsit falon yake tamkar babu kowa cikin gidan,da ido suke kallon falon tare da  yin sallama koda zasu samu wani a akusa ya amsa musu,saidai har yanzu babu motsin kowa

qofar dake hannun hagu suka ji an murda an bude,duk da ‘yar tazarar dake tsakaninsu suna iya jiyo dariyar su,su biyu ne daya a gaba daya abaya
matashiya ce ‘yar kimanin shekara ashirin da biyar sai wata agefenta wadda zata iya bata shekaru uku

basu kula da su maryam ba dake tsaye a tsakiyan katafaren falon ba har sai da suka zo daf da su,ta gaban ce mai kimanin shekaru ashirin da biyar din ce ta soma qare musu kallo,kallo ne na qurilla da saka tsarguwa,sai da ta gama tace
”mu je ko jidda na taka miki”ta fada tana kallonsu sama da qasa
har zasu gota haj atika tace
”ji mana”ba tare data dawo ba ta waiwayo tana jirqn me zasu ce
”don Allah ko zaki mana magana da haj bintu?”

cikin halin ko in kula tace”ku zauna ku jirayi fitowarta,may be yanzu zata fito”daga haka tayi gaba abinta tare da jan hannun wadda suke tafiyar tare,haj atika tace ”zauna maryam,bari na kira hajiyar”
maganar second uku fayi da ita ta kashe wayar,cikin minti biyar katafariyar qofar dake hannun dama ta bude,kyakkyawar mace ce ‘yar kimanin shekara talatin amma a zahiri ta kai shekara hamsin da uku,kyawun jiki iya ado da kwalliya hade da tsafta ne suka wawashe ragowar shekarun suka boyesu

sanye take da swiss lace ruwan toka da adon orange,sai labcoat da ta dora fara tas a sama,takalmin qafarta hill ne shima fari ne qaf kamar ranar ta fara sashi,ta nade wuyanta da mayafi orange,fuskarta qunshe da yalwataccen murmushi
”sannu hajiya,maimakon ku shigo sai kuma ku zauna anan,ku taso don Allah”ta fada tana nuna masu qofar,gaba tayi suka bita abaya

abun mamaki sai gasu a wani gurin,guri ne mai kama da gurin shan iska,saidai dauke yake da tyles fari qal illa tsakiyar gurin da aka yiwa shafe din cycle aka cika shi da ‘yan shuke shuke masu furanni dake fidda qamshi
qofa ce ta glass wanda na waje baya iya ganin na ciki bayan sun shiga ciki ta fahimci hakan,falo ne shima mai dauke da kujeru set biyu,gini ne sama da qasa wato mai bene,wanda matattakalar na acikin falon,tsarinshi abun sha’awa ne matuqa duk iya iya tsarinka sai ya burge ka,komai na cikin falon fari ne da milk,babu alamun qura ko dauda a tattare da shi sai kace yanzu aka bare komai aledarsa aka sanya

”bismillah”hajiya bintu tace musu tana shirin zama
”hajiya ga maryam na kawo miki,kuma bani da haufi a kanta,ke kanki,nasan zaki ji dadin aiki da maryam insha Allahu”haj atika ta fada bayan sun gama gaisawa
murmushi ta sake yi
”ina fatan haka,maryam sannu,ina fata hajiya ta gaya miki komai,girki ne kadai nake so ki dinga yiwa yaro na,kada kiji a ranki cewa wai aiki kika zo,kisa aranki taimako na kika zo yi,ki dauki kanki tamkar diyata,domin dama ina cike da kewar rashin yarinya mace,to ina ji a raina yau Allah ya bani,abu daya kawai nake buqata daga gareki,ki riqe amana don Allah,ki kula ki kuma yi taka tsantsan da abincin yarona,nasan kinsan komai game da abubuwan da ya faru a kanshi,ina son abdallah don Allah ki kula min da shi,na rasa babanshi bana son in rasa shi”ta qarashe maganar muryarta na bayyana raunin da zuciyarta tayi

duk sai taji tausayin su ya kamata,sai take jin ina ma ita ta samu wanna gatan,ina ma ita ke da gata har kamar haka
”insha Allahu haj na miki alqawarin ba zaki samu wani abu mai kama da cin amana ba daga gareni”
hakan data fada dukansu yayi masu dadi har haj bintan na murmusawa
”idan kika min haka kuwa maryam kin gama min komaibani da abinda,zan saka miki da shi,gyara guda daya,indai kina son insinga jinki kamar diyar tawa da gaske to kada ki sake kira na hajiya,ki kirani da mami kamar yadda Abdallah na ke kirana”
sai a lokacin maryam tayi murmushi karo na farko,harga Allah taji dadin karramawar da tayi mata”to,mami”
”yauwa,na gode,hajiya atika na gode qwarai da gaske,bazan iya manta wannan taimakon da kika yimin ba”
”babu komai haj bintu,ai abdallah kamar da yake a gurina,ni zan wuce,maryam…..”
hajiyan ta fada tana miqewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button