ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

alhamdulillah finally a found someone who loves me just for me,ba don wani abu da nake da shi ba,but ban manta ba i promise sai na ninka sona cikin zuciyarki fiye da da,nasan nayi nasara duk yadda kika kai ga boye hakan alredy na ganahi cikin idanuwanki koda zaki qaryata ni,abu na gaba shine ki fadamin shima na tabbatar miki cewa sai nayi nasara nayi alqawari,TO THE MOST BEAUTIFUL GIRL IN D WORLD,AM SORRY BABY,

Lumshe idanunta tayi tana jin wani abu da bata taba jin irinsa ba na ratsata,gaba daya abdallah ya gama kasheta,muguwar kasala ce ta lullubeta,sai ta ninke takardar ta lalubo jakarta da take ajjiye muhimman abubuwanta zata jefa ciki idanunta suka sauka kan takardar,takarda ce data dauketa washegarin daren da abdallah ya fara cuta,sam ta mance da ita,da sauri ta daukota ta bude ninkin da tayi mata,rubutune mai kyau kamar wancan saidai bai kai yawan wancan ba

idan da kina da masaniyar tun yaushe na fara sanki ba zaki nemi abdallah ya rabu da ke ba,na soki a lokacin da bakisan akwai mai sonki ba cikin duniya,maryam tun kina ‘yar secondry school na fara sonki,cikin kulawaata da sa idona kika kammala universty dinki,can you remember sau nawa kike zuwa registration ace miki an dau nauyinki saboda hazaqarki cikin dalibai?,zaki iya tuna samari nawa kika yi suka tafi basu sake dawowa ba?,har kina tsammani ko matsala ce daga gareki,kin kusa auren jabir a lokacin bani qasar nan ban sani ba na tafi jinya na gubar da naci london,cikin qurarren lokaci na samu labarin hakan ina can,sauran qiris na rasa raina san da na samu labarin zakiyi aure amma da yake Allah na sona ya tsinke lamarin,dalili kenan da na nemi sabon mai dafa min a binci saboda na sani bangarenki ne………

Iyakar rubutun dake ciki kenan saidai tasirin da ta yuwa zuciya da gangar jikinta mai yawa ne har ta kasa zama ta miqe tsaye,da gaske abdallah yake?shekaru nawa nufinsa yana tare da sonta,abdallah ya dade tare da ita ba tare data sani ba
A hankaki wasu abubuwan da suka dinga faruwa da ita a baya suka dinga fado mata,sautari akan tsaya da mota ta alfarma da niyyar rage mata hanya,a lokacin haushi da takaici na kamata ne don tana tsammanin ‘yan kama wuri zauna ne kawai wadandq suke barewa duniya gyada taci keson hilatarta,saidai bata taba katarin ganin fuskar abdallah cikinsu ba,duk cikin nashi salon game din ne kamar yadda ya mata kan ABDUR RAHIM?.

sai kawai taji murmushi ya subuce mata
abdallah?
abdallah?,wanne irin mutum ne kai abdallah,basira da wayinka sun isa,you have play good game with me”ta samu kanta tana fada cikin zuciyarta,sai ta koma bakin gado ta zauna tana tuna abubuwa masu yawa a wancan lokacin,tasha ganin abubuwa masu yawa da suka sa ta dinga jin tsoro har take ganin ko jinnu gareta

Wayarta dake silent taga tana haske,ta miqa hannu ta daukota daga gefan pillow,baquwar number ce,sai data daga kai ta kalli agogo qarfe sha biyu da minti goma sha biyar na dare ,ta maida kanta kan wayar tuni har kiran ya tsinke,tana shirin maida wayar wani kiran ya sake shigowa,da tayi kamar ba zata daga ba daga qarshe ta daga din ta kara a kunnenta kana tayi shiru don tantance waye
”assalamu alaikum”muryar abdallah ta daki dodon kunnenta,kasa zama tayi sai ta sulale ta kwanta ruf da ciki saman gadon saboda wani makami da ya aikowa zuciyarta,sake maimaita sallamarsa yayi wanda wanann karon sai da ta lumshe idanunta,lebanta ne suka amsa ba tare da ko wane harafi ya fita ba
”baby nasan kina jina,zuwa yanzu na tabbatar kin karanta saqona”itama so take ta dan rama ko yaya ne kafin ya dawo kano,muryarta low sosai wanda ko kai dake dakin babu lallai kaji me take fadi
”ban duba ba,don bani da time na duba takardu”murmushi ya saka mai sauti da wata ‘yar shashsheqa wanda har sai da ta jiyo shi,tsigar jikinta ta zuba
”baby,baby,baby,kullum kina yiwa kanki qarya me yasa?,i know tuni saqona ya isa,ko kice eh ko kice a’ah,na kira ne dama naji muryarki ko zan iya bacci,sai nakejin dama mu koma qauyen ni’ima muyi zamanmu,atleast acan zamu dinga kwana daki daya,idan da rabona ma sai in kwana cikin ni’imtacce jikinki,baby na kasa mance moment namu na dazun ina jin kamar ya dawo,i want feel you beside me,i want to feel your lips……on my neck and…..baby i want…. Iwant”ya fadi kamar mai tsoron magana
”i want to run my head along your chest,kiss your lips….”ai bata iya jumurin sauraronsa ba ta katse kiran nasa ta jefa wayar gefanta bayan ta tsura mata ido

Tana kallin kiran nasa amma bata jin zata iya dagawa yaci gaba da horata babu gaira babu dalili,shi dole sai ya tada zaune tsaye,sai da ya hada mata missed call kusan goma sanann ya haqura,qarfe saya da kwata ta sauka a gadon ta shiga bandaki ta daura alwala tayi nafila raka’a biyu ta kwanta,tunani ne fal kwanyarta ta kama wanann ta saki wancan,cikin haka tunanin mero ya fado mata,sai taji ranta ya baci,tana son sanin haqiqanin me tsakaninsa da ita kafin komai ya daidaita,a uziyya tayi ta kori tunanin daga ranta don haka dabi’arta take bata kwana da kowa cikin ranta

????????????????????????

Ta makara sosai gun tashi kuma mami bata tayar da ita ba,bakinta ta wanke da fuskarta ta fito falon bata tadda mami ba sai baaba uwani tana ta gyara kitchen,nan ta tsaya sunq gaisawa har mamin ta sauko,tayi adonta cikin dogowar riga mai zubin buba saidai ready made ce wannan,bayan sun gaisa mamin ta gaya mata ta shirya hajiya laila na zuwa anjima zata fara mata gyaran jiki,ita gaba daya kunya ma kamata take duk da ta sani mami bata dauketa suruka ba amma akwai kunya tsakani,ta amsa mata da to sannan ta koma daki.

Ta daura towel tana shirin shiga wanka saqo ya shigo wayar sai ta dawo ta duba,number din dazu ce wadda ta tabbatar ta abdallah ce
”baby jiya kin kusa kasheni wlh,sauran qiris na gayawa mami yadda kike gara mata yaro,ina gaya miki damuwa ta kika gudu kika barni,me yasa baby?,i need your help baby”
bata shirya ba amma sai da murmushi ya subuce mata,ya tuna mata ma,take ta kira mamanta,hira sukayi sosai wadda ta qara mata kewar gidansu

Cikin kwanakin gyara sosai maryam kesha wanda ko bazawara aka yiwa hakan sai ta tsere ma sa’a,itadai maryam nata ido,wannan qauna da mami kewa abdallah ba kadan bace

????????????????????????????

Zaune suke su biyu cikin fallen dakin nata wanda yafi kama da kango,idan ba kyakkyawan sani kayi mata ba zaka tsammaci mahaukaciya ce sabun kamu,tuni ta saje da su tabi sahunsu kamar yadda habiba ta shaida mata,ta tsotse ta rame kamar wadda kullum ake diba ana kada miya,ga uban ciki a gaba ya fito yayi tsororo kamar dosana shi akayi babu kyawun gani.

”yanzu habiba babu wata hanya kenan ta kubuta”ta tambayeta cikin damuwa
”bana zaton zahariyya akwai”
dariya sukaji ana babaka musu a razane suka daga kansnsu,malam na hayi ne tsaye bakin qofar dakin yana shigowa
”kuna batawa kanku lokaci ne amma babu wadda ta isa ta kubuta daga gareni,mutane ne ku masu son zuciya,kun bijerewa Allah kuna neman biyan buqatarku kan wani mummunan qudiri naku,yadda kuke da baqar zuciya nina haka nake,kunga kenan zamu je ta tadda da mujemu,a sannu sannu mata ire irenku zasu ci gaba da shiga masibu kala kala,walau a nan duniya ko a lahira,irin mu muna nan da yawa Allah ya ajjiyemu saboda ire irenku,haka gaba dayq mu da ku kuma sai munje lahira za’a hukunta mu baki daya,ni dama na riga na sani bani da rabo a lahira,kunga ai gwara naci nawa tun anan”ya juya ya fice yana sheqa dariyarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button