ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????

Saura kwana goma biki aka kawo lefe,lefe ne na gani na fada wanda ita kanta maryamu ta yaba qwarai da gaske,qarara rudewar su huwailan ta fito,sumbatu suka dinga yi don duka cikinsu babu wadda ta aurar da ‘yar da ta samu lefe kwatankwacin haka,komai sai da suka masa dilla filla suka qare masa kallo

abinda ya bata mamaki ganin dukkan ‘yan gida sun shiga shirye shiryen bikin gadan gadan,kada ma inna hadiza taji labari,duk da ba shiga sabgar su maryamun take ba,harda cin bashi da sauya furnitures din daki

maryam na zaune gefan mamanta tana lissafa mata sunayen mutanen da zata tura hindatu takaiwa cingam tana rubuta mata a takarda hindatun ta shigo,hannunta ledar dinkunanta ne da ta door mat da maryam ta bada ta siyo,ta zauna kan kujera tana fadin
”sannu harkin dawo?”
”eh wlh amma fa na sha wuya”ta fada tana shiga kitchen ta dauko ruwa cikin gorar faro da suke durawa susa a fridhe dinsu,sai da tq shanye sannan tace
”mama”
”na’am”
”nifa abun nan na bani mamaki”
”mefa?”ta tambayeta tan duba rubutun,da maryam keyi
”su hauwa mana da su jamila,gaba daya sai hidimar biki ake yi,kada ma jamila taji labari ita da mamanta,mutanen da aduniya babu wadanda suka tsana kamar mu?”
sai a lokacin maman ta kalleta duka harda maryam din
”to,banda abinki hindatu sai ku godewa Allah,me yiwuwa Allah ne ya ganar da su gaskiya,tunda babu wanda za’ace ABADAN zai dawwama a halin da yake,dole watarana akwai sauyi,qila Allah ya ganar da su ne”
”nima dai mama haka nayi tunani,kuma wallahi bakiji dadin da naji ba,Allah yasa silar gyaruwar tsakanin mu kenan”
”ameen”cewar mama,ita dai hindatu tabe baki tayi tace ”to Allah yasa,amma ba girin girin ba tayi mai”

sallamar jamila ce ta katse hirar tasu,dukkaninsu suka bita da kallo,don basu iya tuna yaushe ta shigo dakin na qarshe,koda sun tuna ma ba alkhairi ne ya kawo ta ba
”sannu mama”
”yauwa sannu”
”gurin maryamu nazo”
”to gani”injita
”cewa nayi yaishe zqki lalle,ina son na biki ne muje tare,kinsan qannan amarya dole su fito kamar amaryar”

sosqi maryamun taji dadi har ta saki tattausan murmushin ta
”ai ba damuwa,jibi ne sai mu tafi tare ai”
”to shikenan”ta juya ta fice
hindatu ta kalleta
”haba ya maryam,nidai gaskiya bazan hada tafiya tare da su ba”
”sai ki fasa zuwan ai”inji mama
”don kuwa ni zan biya mata ma kudin lallen,haba hindatu dan uwanka dan uwanka ne fa,kuma ka dinga kyautatawa dan uwanka musulmi zato,ki zama mai tsarkakkiyar zuciya kinji qanwata”dole hindatun taja bakinta ta tsuke

Tare suka je lallen maryam hindatu da jamila,ita biya kudin dukkaninsu

????????????????????????????

cike gidan yake da mutane kasancewar yaune ranar daurin aure,ga gauyar yan uwa daga bangaren mama da inna hadiza,kusan yawancin danginta na cike a gidan danqam,har ita kanta maman tayi mamakin hakan,amma sai ta share,batun sanin cewa babu yadda Allah baya iya sauya lamarinsa

maryam na maqotansu ita da qawayenta ciki harda raliya,tayi shar cikin atamfa super riga da zani plain,ba qaramin kyau tayi ba,fuskarta cike da walwala da farinciki

guda suka dinga ji tana tashi sosai tamkar a cikin gidan akeyi kasancewar maqota ne gida jikin gidan,raliya ta saki tata gudar tana fadin
”shikenan alhmdlh an daura,tazama tazama,yau diyana ta shigo sahu,Allah yasa wata tara iwar haka mu hadu suna”dariya duka aka saki wasu na cewa amin wadda shigowar hindatu cikin gunkin kuka ya katse musu ita
maryam ce ta soma miqewa tanajin qirjinta na bugawa tun kafin taji me ya samu hindatun zuciyarta ke mata saqe saqen munanan abubuwa

zubewa tayi gaban maryam tana fadin
”ya maryam don Allah me kika yiwa ya jabir?,me kika yi masa da zai miki wannan sakayyar?,me kika yi masa da har ya guje miki ya maida aurenshi kan JAMILA?”
dum taji kunnuwanta sunyi,qwaqwalwarta lokaci guda ta gaza yin aikinta,sai ta daina gane komai,meke shirin faruwa d ita?tambayar da taji qwaqwalwarta na mata kenan,kafin bijirowar amsar sai taji tamkar an zare dukkan wata garkuwa da ta sata ta iya tsaiwa da qafafunta,yaraf taji ta zube,daganan komai ya dauke mata dif kamar an dauke wutar nepa adaki mai tsananin duhu……..

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????✍????
[9/17, 12:50 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

       ▶6⃣

”ya maryam,me kika masa da har ya guje miki ya maida aurensa kan jamila?”
maganar da keta amsa kuwwa cikin kunnenta kenan bayan ta farka,sai hawaye ya fara turereniyar fitowa daga runtsatsun idanunta da ta kasa budesu suna bi ta gefan fuskarta su sauka har cikin kunnenta,wani irin yanayi take ji daban cikin zuciya da gangar jikinta
me ta aikatawa jabir da zafi haka wanda har ta cancanci wannan hukuncin?
a iya saninta ba zata iya tuna abu guda ba mara dadi da ya taba hadasu a tarihin rayuwar soyayyarsu ba

hindatu ce ta fara ankara da farkawar tata ta sanadiyyar hawayen fuskar tata dake bi ta gefen kuncinta,da sauri ta taso
”sannu ya maryam,me yake miki ciwo yanzu”
kai kawai ta gyada mata alamar babu komai
mirya can qasa tace
”dagoni hindatu”
a hankali ta taonaka mata ta tashin ta jingina da filo sannan tace bari na kira ”mama”

maman ce ta takurata kan ta tashi hindatu ta rakata asibiti,bata biqatar fita koda falon nasu ne don bata san da wanne iso zata kalli jama’a,hakanan suma batsan da wanne ido zasu dubeta ba,ta tabbatar maganar ta gama zaga unguwar ma gaba daya ba gidan ba,amma ba zata iya misa mata ba don ita don ma so take tadan gusa daga gidan saboda haka ta zura hijabinta hindatun tace bari ta nemo dan adaidaita sahu sai tayi mata magana

bayan fitar hindatun shiru dakin yayi,baka jiyo komai sai hargowa da hayaniyar jama’arsu huwaila da inna hadiza cike da farinciki,mintuna biyar sai ga hindatun ta dawo ita ta riqe maryamun suka fito yayin da ‘yan uwan maman nata dake zaune jugum a rumfar tasu suke mata sannu da jaje,don tuni wasu ma soma hada kayansu don komawa inda suka fito

Sun samu ganin likita cikin qanqanin lokaci don private clinic suka je,likitan yace zai riqe ta zuwa magariba ta huta sosai tasha magungunanta,bata musa din ba suka bata gado hindatu na tare da ita

basu bar asibitin ba sai magariba,suna hanya ne hindatu tace”anty raliya ta kira ki har sau biyu kina bacci,tace zaga sake kira,ya nasir ne yayi kiranta tunda kuma ta fita bata dawo ba”
kai ta iya gyada mata kawai don bata jin zata iya bude bakinta
suna shigowa layin gabanta ya dinga dukan uku uku,ji take tamkar ta,canza wani gidan ba nasu ba,ji take kamar ta yanka a guje ta bace a nemeta a rasa,motocine a jere har zuwa qofar gidan nasu,sauka sukayi suka biya shi sannan suka dutfafi gidan wanda har qofar gida jama’a ne

duhun da garin yayi yasa babu wanda ya shaidasu har suka shige gidan wanda tun daga soron suke jiyo tashin muryoyi cike da hargowa,babu wadda tace da ‘yar uwarta komai har suka shigo ainihin tsakar gidan,ga mamakinsu qofar dakinsu ne cike yake da jama’a wanda ya tabbatar musu da koma mene ya shafesu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button