ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

A parlour dinta ta samu baaba uwani da lubabatu sun gama breakfast suna zaune suna hirarsu abinsu,gu ta samu ta zauna da yawancin lokuta bata fitowa da wuri sai sun gama shan hirarsu da abdallah tayi wanka sannan ta fito ta karya,cikin girmamawa ta gaida baaba uwani suka gaisa da lubabatu sannan ta sanar musu isowar abdallan
”to alhmdlh,Allah ya iso da su lafiya”inji baaba uwani cikin farinciki,ba tare da bata lokaci ba suka soma yan sabgogin da duk ya kamata suyi din,duk da gidan amarya dama ba wani abu yaje da buqatar a sauya masa ba,amaryar ma irin maryam ami tsafata kula da tattali
lubabatu ke ce mata
”babu wani dan gyara ne haka adda da zakiyi?”batasan sanda ta harareta ba don sarai ta fuskanci me take nufi
”halan wannan karon so kuke abdallah ya kaini kushewa ba asibiti ba”ta fada a zuciyarta,a fili kuwa cewa tayi
”uhhmmm,baku fa da kunya sosai yaran yanzun”dariya lubabtu tayi tana toshe bakinta tare da cewa
”Allah ya bawa adda haquri”

Lubabatun ke mata zancan girki dane dame za’ayi?,sam ba wanda ta yadda ta bawa girkin don tace da kanta zatayi,sabida wannan ne karo na farko da zata yiwa mijinta girki cikin gidan aurensu,abinci ta tsara zata masa kala uku baya ga kala kalar farfesu shima uku,sai drinks don haka tun sha biyun ta fara ragewa don kada lokaci ya qure mata

zuwa la’asar ta kammala komai sai miya da bata qarasa ba guda biyu su din ma suna kan wuta saura kadan su kammala dahuwa,tana falo tana dan hutawa saiga baaba uwani dauke da yar jakarta,cikin mamaki maryam ta dubeta
”a’ah,baaba ne zakiyi da jaka da ranar nan?”
”gida mana meramu,zan koma gidan hajiya,tunda yau abdullahi zai dawo ko”
”haba baaba,ai kwa bari sai gobe tunda baku san zai dawo din na sai dazu da safe fa”bakinta ta kama
”rufamin asiri meramu,haba don rashin hankali sai in zqune muku gotai gotai,hajiya ma ta riga da ta aiko direba,ya iso ma yana waje yana jira na”tana mita ta miqe ta haura sama ta daukowa baban atamfa mai kyau turmi daya,sinqin sabulu da turare sai plate din takalmi guda daya,godiya sosai baaban ta dinga mata har ta sata jin kunya,hijabinta ta zura saboda umarnin abdallah na sanya hijabi ta rakata har bakin get suna yiwa juna godiya

Tana dawowa ciki saiga lubabatu itamq da nata kayan,hararata tayi tace
”wallahi baki isa ba,kada ma kice min tafiya zakiyi,ku barni ni kadai bayan sai magariba zasu shigo”dariya hindatu tayi
”wallahi ya hisham ne yace da naji zaku dawo na bar muku gidanku,idan kuma na zauna duk abinda nq gani nina jawowa kaina,kai take gyadawa
”shi hisham din ya gaya miki haka?,to babu inda zaki kuma zai shigo tamu ni da shi”haka ta tare hindatun ta hanata tafiya

qarfe shida ta fito daga wanka ana ta shiye shiryen kiran sallah magariba,duk bayan mintina sai ta duba wayarta ko zata ga kira ko saqon abdallah amma shiru,a haka ya qarasa gaban madubi ta tsara kwalliya mai cike da tsari bayan ta mulke jikinta da nau’in turaruka kala daban daban,gaban sif dinta taje ta bude cike da tnanin wacce shiga zata yi ma,ta jima tana nazari kafin daga bisani ta fidda wata gown mai bala’in kyau,ashe ce wadda aka mata ado da jajayen dutsina daga gin breast din da kuma furanni,ta gyara gashinta tayi masa kanta daurin V shafe da jan dankwali,fashion ta saka na jajayen sutsina take ta fito gaba daya kamar wadda aka sauya

Babban hijabi ta saka zata tada salla kenan taji knocking ta tambayi waye lubabatu ce tace ta jirata sallah zatayi tana fitowa,tana idarwa ta sake duba lokaci gari har ya dan fara duhu,ta cire hijabin ta sake gyara daurin nata kana ta fito falon,burner ta kunna dake lunguna na gidan duka ta sake sa turaren wuta daidai lokacin da lubabaatu ke fitowa da shirin ta na tafiya,mutuwar tsaye lubabatun tayi
”adda maryam!,kinganki kuwa,shan kyau irin wanann daukar magana haka?”dariya lubabatu ta bata ta dinga darawa,da qyar ta tsata suka fara sallama,ta tambaueta ta me takeso ta bata
”kome kika bani adda maryam yayi,ni ko zaman ma da nayi gidan nan ai ya isheni,ac din da nasha ta kwana goma bakiga har na canza ba,ga kuma babban kamu nayi ya hisham…”
”munafukai,ai dama daga yadda naga kuna wani kallin juna elh ma san da walakin kuma bari yazo sai na tsigaleshi”da sauri lubabatu ta rufe mata baki
”don Allah kada ki masa maganar,bai furta da bakinsa ba,yace kawai dai zamiyi maganar idan ya dawi zaizo gidanmu”hannunta ta cire daga bakinta
”ni kinga kada ki goge min janbakin tun kan wanda aka sa donshi ya gani”ta fada tana dariya kana ta shiga ta dauko mata itama atamfa saidai ita ta hada mata da kayan kwalliya

”inason in bada doguwar riga ki kaiwa binta amma ina tsoron halinsu,ni ko ganinsu a gida ma banayi anya ma kuwa suna nan”
dariya lubabtu ta sheqe da ita
”wallahi sunana,ai yanzu ko nawa za’a basu su miki rashin arziqi ba zasuyi ba,bakisan ya abdallah ne yasa aka debe su aka rufe ba suka kwana aka tsoratasu kan rashin mutuncin da suke miki keda mama?da suka dawo wallahi ko qofar dakin maman ma daina bi sukayi bare su kallshi,kuma da amincewata yasa akayi hakan,dama iskancinsu ya ishemu,yanzu kuwa idan kinji suna rashin mutunci a gidan uwarsu data koya musu suke saukewa”ta qarashe maganar tana cin dariya abinta
mamaki ne ya kamamaryam,a gaida abdallah,shikam halinshi ne idan dai zaiyi abun alkhairi ba wanda yakr gayawa saidai idaniyarka ta gane maka ko a baka labari,qimarsa ta sake daduwa cikin idonta,babu shakka duk wanda zaiga qimar mahaifanka ya tsare maka mutuncinsu ya girmamasu ya gama maka komai koda kuwa yankan naman juna kuke kai da shi,har harabar gidan ta rakata itama bayan ta sa driver ya dauketa zuwa gida

tsuru ta dawo tayi cikin falon tana ta duba lokaci,qarar wayarta taja hankalinta,dagawa tayi da sauri ganin sunan abdallah ne
”hello baby,kimin afuwa bazan samu danar dawowar yau ba,wani muhimmin abu ya tsaidamu,amma din Allah kada ranki ya baci,ki leqo yanzu compound na aiko wani yaro zai kawo miki saqo,idan bai iso ba ki jirashi a nan don bana so ya shigo min gida”kafin tace komai ya katse wayar,galala tayi da waya a hannunta ta rasa nayi ma,jikinta ba qwari ta zari hijabinta data tuna yace ta fito yayo aike

har tsakiyan gidan ta fito bataga kowa ba don haka ta tsaya nan wajen minti goma tana jira taga ko zai iso,ganin tsaiwar tayi yawa yasa ta yanke shawara komawa falo ta zauna bakin window ta jirashi a nan tunda tana iya ganin harabar gidan daga nan,jikinta ba qwari haka zuciyarta babu dadi tana rungume da hannayenta a qirji kanta a qasa har ta iso qofar falon

Cak taji anyi sama da ita baki dayanta,a tsorace ta soma laluben fuskar mutumin saidai tun kafin takai ga tozali dashi turatensa ya gaya mata ABDULLAHINKI NE,falon ya shige da ita wanda suna shigar wasu qwayaye masu launin ja da fari suka kama a take rubutun AM BACK I LOVE YOU ya bayyana,murmushi ya subuce mata bayan da suka hada ido,shima mayar mata da martani yayi kana suka zube kan kujera ya hau aika mata da saqonnin kewarta da yayi,da qyar ta lallabashi yayi wanka yayi sallar isha’i,kadan yaci abincin don baki daya hankalinsa na kanta,tana cikin gyaran gun da suka ci abincin taji baki daya an sungumeta bai sauketa ko ina ba sai bedroom dinshi wanda ayau suka fara amfani da shi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button