ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

kai ta girgiza”haba jabir,yau ko maqota muke mu da su jamila ai duniya ta zagemu balle iba daya”
”ya kamata kiyi amfani da ilimin da Allah ya huwace miki,ki dinga saka addininki gaba da al’adarki,babu wani abu da ya jaramta min auren hindatu koda kuwa ke na aura matuqar mun riga da mun rabu”
cikin girgiza kai tace
”haba jabir,amma dai ai ana barin halas don kunya”

take yanayin fuskarsa ta sauya
”gwara maryamu ki fito kanki tsaye kice min ba kyason tarayyata da hindatu,gwara ki cemin jabir ba zamu baka hindatu na tafi qarfinka
wace iriyar kunya kike magan akanta ne maryam?
su waye kima wadan da za’aji kunyar?
ko kin manta jin kunyar mara kunya asara ce?
har kin manta da abunda suka miki ne,shin a lokacin da suka aikata din ba’a halicci kunya ba ne ko kiwa akwaita sune basu da ita?”ya qarashe maganar cikin bacin rai,ta bude bakinta zata yi magana ya dakatar da ita da hannunshi kana yace
”dakata maryam,bana buqatar kice komai,tun yanzun na cireki daga batun nan,ban neman kimin komai,zan yiwa kaina yaqin samun hindatu,naki kawai ido addu’a da fatan alkhairi”bai bata damar cewa komai ba ya tashi ya nar gin yabi hanyar da hindati tayi

kimanin minti talatin ta gaza tashi a gun,wani bangaren na zuciyarka na gaya mata bata kgautawa jabir ba,mai son naka ai ya gama maka komai,yayin da wani,bangaren kuma ke ganin dai dai tayi,don rigima ce zata riri ba qarama ba cikin gidan,daya barin uace mata,to sai me?,da ba naki bane jabir din suka aikata abinda suka aikata suka maidashi nasu?to ai dama idan mai guri yazo mai tabarma nade kayarshi yake

shiru shiru hindatun ma bata dawo ba,ta ciro wayarta tayi kiranta,abun mamaki sai taji jabir ne ya daga,kafin tace wani abu ya rigata
”kada ki cikata da fada gamu nan zuwa”hangame baki tayi tana kallon wayar,bata qarasa daskarewa ba sai da ta jangosu sun jero suna tafe suna qyalqyala dariya hannun jabir din riqe da fararen ledoji masu dauke da tambarin sahad store
duban hindatun tayi saivtaga yarinyar ta waske mata tamkar babu wani abu da tayi,kabir me ya katse kallon da take mata ta hanyar ajjiye mata leda daya kusa da ita
”kada ki cinye min gimbiyata ki barta hala,s
duka sauran tuhumarki ki hadiyeta na karbi tutar hindatu”
bata data cewa kallinsu kawai take,haqiqa ta san cewa indai hindatu tayo,nasarar auren jabir bata da sauran matsalar rayuwa,miji na gari kam ta gama samunshi,suka qaraci mata shaqiyancinsu suka miqe don tafiya,nan ma ya kasa ya tsare kan shi zai kaisu,hindatu ta takura tolas suka bishin ya ajjiyau har qofar gida

suna shiga soron gidan maryam tayi saurin janyo hindatu da har tayi gaba
”hindatu ashe baki da tunani?”
ta zumburo baki
”me kuma nayi adda?”
”kin manta waye jabir tsohon mijin yayarki jamila?”
sai ta kwashe da dariya har maryam na toshe mata baki kada ta dauko hankalin mutanen gidan
”nice ta biyu wajen sanin waye jabir bayan ke ta farko,to wai ma anty don autukina yaje aikin hajji sai in kasa zuwa in sauke farali nima saboda kunya?,jabir yayi min adda don na tabbatar yana da nagarta tunda har kika amince da shi a baya”
sai ta kuma yin qasa da murya
”baya ga haka adda wannan wata qatotuwar dama ce garemu ta rama duka cin kashin da aka mana,wallahi sai na dauki fansar duk baqincikin da suka cusa mana”

ta fuskanci da gaske hindatun take
”Allah ya taimaka”ta fada kana ta shigeta cikin zuciyarta tana musu addu’ar tabbatar lamarin cikin nasara da farinciki

????????????????????

Batasan ya akayi ba itadai taji an kawo kudin hindatun har da kudin sa rana jimillar naira dubu dubu dari uku dubu dari kudin aure dubu dari biyu kuma kudin sa rana,hakan ya sanya baba yace ta shaidawa abdur rahim ya turo a saka rana,su din ma kudin sa ranar suka bada naira dubu dari biyar,kudin sun bawa maryam din mamaki,murmushi abdur rahim din yayo yace
”ko nawa na bada kudin aurenki yayi kadan maryam,kinfi qarfin haka,me din mai tsada ce”murmishi kawai tayi tana sake ganin qima da darajar son da yake mata

duk abin nan da ake jama’ar gidan basu da masaniya,kusan duk ranar da za’azo din basu gidan suna yawon asara yawon bidar asiri,asara goma da ashirin babu kudinsu ba imani

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:54 PM] 80k: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

     ▶3⃣5⃣

???????? wannan page naku ne

???????? haske writers asso
???????? huguma conversation and novels rooms_
???????? da kuma
???????? Zauren biebie isah
Allah ya bar qauna????????❤????????

Ankarbo daga imam bukhari r.a,manzan Allah s.a.w yace
(qarami ya yiwa babba sallama,matafiyi ya yiwa wanda ya taras,jama’a ‘yan kadan su za suyi yawa masu yawa)

a wani hadisin da imamu muslim ya rawaito daga annabin rahama s a w yace(wanda a zuciyarshi akwai girman kai daidai da qwayar zarra bazai shiga aljanna ba)

Allah kayi mana tsari kada ka haramta mana aljannarka,ka hanamu dukkan wata baiwa ko ni’ima taka da zata yi sanadin zamowa masu girman kai

Fadar irin farincikin da mama da iyalinta ke ciki ma bata baki ne,sunyi amanna cewa wannan ce shekarar farincikinsu,addu’o’in da suka dade suna qwanqwasawa qofa yau kam an bude musu dukkan qofofin,duk wani tsohuwar ajiya ta mama data jibanci kadara ta daga ta saida,ta yiwa bikin shiri matuqa da gaske,ga dangi masu zuciyar yi mata da Allah ya hadata da su

takanas suka ziyarci gaya ta saida manyan gonakinta na gado guda biyu,ba qaramin kudi ta samu da su ba kasancewar yadda a yanzu kowa ya koma noma gonakin daraja suke,tuni ta fidda kudin kayan gado kayan kitchen da sauran tarkace na hindatu,maryam kam dama da yan kudadenta da take sa ka ran zasu isheta sayan kayan gado,ga mamakinsu saiga kudade baban su ya damqa masu a boye yace sukaje su zabi kayan gadon da suke so,shi din ma gonakinsa biyu ya siyar dake gayan,dama bashi yake amfana da su ba yan uwansa ne,cikin rufin aairi, Allah sai gasu sun tashi da kayan gado na kere sa’a masu kyau tsada da aminci

bata sake shiga farinciki matsananci ba sai da mami ta damqa mata passport dauke da visa ta qasashe biyu saudiyya da china
”maryam,inason inje siyayyar lefen abdallah ne,sannan ke kanki ina son in miki siyayya irin wadda uwa take wa diyarta,naso ‘ya mace amma Allah bai bani ba,to a yanzun kuma sai Allah ya bani ke,naso ace lokacin bikinki da abdallah bai hade ba da ina mai tabbatar miki anan gidan zaki zauna har akammala taro a miqa ki gidanki,saidai duk da haka bikin magaji ai bazai hana na magajiya ba,zamu fara zuwa china muyi siyayya sanan mu dawo saudiyya muyi umara,kuyi addu’a kowannanku ya roqawa kanshi alkhairi kan sabuwar rayuwar da zaya shiga,ni da ke ne da abdallah”

rasa bakin da zata gode mata tayi saidai ta tsinci kanta cikin zubda qwallar farinciki,tabbas uwa ce,mami uwa ce wadda tasan ciwo da darajar ‘ya’ya,babu shakka ko ita ta tsugunna ta haifeta iyakacina binda zata mata kenan,haduwars ta tabbatar daga Allah yake,bata manta yadda taqi taji batason aikin gidan mamin ashe alkhairi ne Allah yake nufinta da shi,gaskiya ne maganar Allah haka take da yake cewa cikin alqur’a ninshi mai girma
(zaku iya qin abu kuma alkhairi ne agareku,sannan zaku iya son abu kuma sharri ne a gareku,Allah shine ya sani ku baku sani ba)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button