ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????

cikin baccinsa ya dinga jin qamshin girki,da sauri ya farka ya mutstsuka ido,ya duba gefansa bata nan,kenan ita ke aikin girki a kitchen qarfe tara na safe?,da azama ya diro daga gadon ya doshi kitchen din

tsayawa kawai yayi yana kallonta tamkar ba ita ta gama sheqa amai jiya ba?,tayi kwalliayarta tayi kyau kamar ka saceta ka gudu,ta matse cikin wata riga mai roba wadda iya qibarka iya yadda zata kamaka iya kacinta qauri an mata tsaga daga gabanta daga qaurin qasa zuwa gwiwa,ta gyara gashinta yayi kyau sosai,ji tayi kawai an rungumeta ta baya sai ta saki yar qaramar dariya
”kasan kuwa irin tsoron daka bani?”
”nima ai kin bani tsoro baby,ke da baki da lafiya ina ke ina kitchen fisabilillahi”waigowa tayi suna fuskantar fuskarta qunshe da murmushi juna yana zagaye da qugunta,ta shafi sajensa kana tace
”ras nake jina shariky,ina mai tabbatar maka idan za’a saka tsere sai na wuceka”dariya ya saka ya sumbaci kumatunta
”babu musu don naga alama,wai baby meye sirrin ne?”ya fada yana kashe mata ido,itama maida masa martani tayi
”name fa?”
sai da ya jujjuyata ya sake kallonta sannan yace”gani nayi sai wani kyau kike qarawa,fatankin nan har tafi tawa laushi,kumatunki kamar kin boye qwai,brown oily eyes dinki kamar an kuma diga musu zaiba da oil,ke tsaho ne kawai har yau na fiki ba…..”kasa qarasa maganar yayi saboda manna bakinta da tayi cikin nashi,sai da ta dan birkitashi sanann ta cire tana duban bakin nasa
”wannan bakin nawa kada ya cinyeni”sake janta,jikinsa yayi yana dariya
”Allah am seriouse,meye sirrin”
”matso na gaya maka”sai tayi dage don duk tsahonta abdallan ya fita ta kai bakinta kunnensa ta shiga jero masa
lumshe ido ya dinga yi yana saurarenta tare da sake shigewa jikinta,banji komai ba face kalmarta ta qarshe
”kaga kuwa kaine sirrin”dukkansu murmushi suka saki mai,hade da dariya dariya,ya kamo fuskarta ya hada goshinsa da nata shima yana mayar mata da martanin kalmomin,sun kusa kwashe a qalla minti goma a haka har ruwan shayin da ta dora ya fara qonewa sannan ta ankara ta zame jikinta da sauri tana cewa
”you see,shi yasa idan ina abu mai muhimmanci banso kazo ka riskeni,don sawa kake ina mantawa da kowa da komai ciki harda kaina”shi ya qarasa hada kayan karin tana tayashi da wasu abubuwan kana suka,yi wanka suka shirya don yaune ranar da abdallahn ke raba tallafi gidan gajiyayyu da asibitoci wanann karon kuma tare zasu shi da mami,maryam ma ta kafe itama sai taje don baza’a samu ladan babu ita ba


tafe suke cikin motar gwanin sha ‘awa don baka banbance waye danta,tsakanin abdallah da maryam,shike jan motar maryam na gefansa,yayin da motar security dinsa biyu ke gabansu biyu ke bayansu,yawanci indai tare da maryam ne cikin fitarsa bai yarda driver yayi tuqi wai don kada a gane masa ita,mami na baya tana duba wasu takardu jefi jefi suna hira da abdallah

”yauwa mami”
”uhmmm”taje dashi kanta na kan takardunta ,tasan tunda ya fadi haka tambaya gareshi
”dama wani lokaci mata na daina cin abinci sai wani abun daban?”bata bawa tambayar tasa muhimmanci ba,don a zatonta shirmene kawai irin na abdallah din haka tace da shi
”kamar yaya kenan?”
”mami maryam,na rasa meke damunta,safe rana dare garin kwaki mai tsamin nan,abinci saidai ta dafa min kawai ni nayita narka,jiya da na matsa mata sai taci amai tayi mami,ni tausayinta ma nake ji”
wannan karom saida ta dago ta dubeta,kunya kamar tayi me ta kama hannun abdallahn a sace ta matse cikin nata
”wayyo hannu na diyana”ya fada yana yamutsa fuska kamar qaramin yaro,da sauri ta sako hannun nasa taja hijabinta ta lullube fuskarta
”kada ka sake matsa mata kan cin abinda bataso,ka barta”cikin damuwa yace
”amma mami gari fa?,bazai mata komai ba?”
”eh yana yi ne zata daina nan kusa”ta fada zuciyarta tamkar qanqara,addu’a take cikin ranta Allah yasa hasashenta ne zai tabbata

Ya sake rausayar da kai
”amma mami ni gani nake kamar yana tsotse jinin mutum ko ruwa jikinsa”
”ba daya,nace maka zata daina ne fa”
”to Allah yasa”ya fada cike da hope,donshi har ga Allah abun na damunsa,gani yake wata cutar ce ta samu maryam dinsa,shi yasa ya sanar da mamin nufinsa idan ya gaya mata akwai wani maganin ta bata,kasa cewa komai maryam tayi,lallai ta yarda Abdallah gabuntar dan fari da tabarar auta na tabashi sosai,a hankali mamin tace
”ki kula kawai da kanki maryam,duk lokacin da kika ji wani sauyi a tattare da ke kumin magana,kada kuce zakuji kunyata,ni mamarku ce baku da kamata”kanta aqasa ta amsa da to,shi kuwa gogan cewa yayi
”ni dama maganin kawai kika rubuta mata mami Allah na tsani naga tana shan garin kwakin nan”murmushi ta dan saki
”bakasan komai nada qa’ida ba,ba’a rubutawa mutum magani kai tsaye,indai kawai kuka ga alamun canjin wani abu ko matsala to ku sanar da ni”
”to mami”ya amsa mata yana ci gaba datuqinshi

a gurin ajjiye ababen hawa suka yi oarking duka motocin nasu,mami ta riga fita saboda isowar shugaban asibitin din ya tarbeta,abdallah na qoqarin fita maryam tayi saurin riqoshi da qarfi har sai da ya dawo ya zauna don bai zata ba,ido ya kashe mata guda daya yana fadin
”ya akayi baby da magana ne?”kicin kicin tayi
”yanzu shariky don kawai ina cin garin kwaki sai ka gayama mami don Allah?”ido ya dan zaro
”to menene don mace kina shan gari dear na?,na tsammaci ciwo ne shi yasa na gaya mata ko zata rubuta miki magani”
”kada ka sake don wallahi ka bani kunya”kiss ya bata a goshi kana yace
”is ok,afuwan my sister”dariya ma ya bata tana zaune ya zagayo ya bude mata side dinta ta fito bayan ya sake gyara mata zaman hijabinta,duk yama tasa gun tsayawa don gaba daya atsarge yake,gani yake wai kallonta ake,security din ma da suka saba binsa a baya yace suyi gaba su zasu biyo bayan nasu,don kada wai su dinga kallonsu ta baya

kimanin su goma sha biyar suka kutsa kai cikin asibitin,daki daki suka dinga bi suna raba taimako,kudade ne masu tsoka suka dinga bayarwa tare da biyan kudin magunguna ga duk wanda ya kasa biya,wayyo Allah,kada kaso kaga abun tausayi kala kala,talakan qasata yana cikin wani hali,talauci yunwa fatara jahilci duka ya tattaru ya narke a kansa,wasu har kukan dadi suka dinga yi,maryam kuwa tuni zuciyarta ta karye,tunvtana share hawayenta a boye har ta saka kuka saboda azabar tausayinsu,abdallah ne ya fara jin sheshsheqarta,gefe ya janyeta hankalinsa a tashe
”sai da nace kiyi zamanki a gida dear kkka ce sai kinzo bayan ba lafiya ce da ke ba,sai na maida ke gida idan ba zaki iya jurewa ba”da sauri ta goge hawayen tana danne kukan din batason ya maida ta din,ganinsu na qara mata imani tare da godewa Allah kan matsayin da take kai,ya zabeta ya dorata ba don tafisu ba,ta yiwuwu a cikinsu ma akwai wadanda suka fita kusanci da Allah amma ya jarrabesu don ya sake tabbatar da imaninsu da shi,duk da haka fakar idinsa ta dinga yi tana goge hawayen ta handkherchief sabida abun tausayin ya isa

A haka suka gangara dakin ‘yan haihuwa,tsoro ya kama maryam sosai ganin masu larura kala kala,akai kai ta dinga gigr hawayen nata wanann karon,ta tsorata sosai da haihuwar,daga bakin wani daki suka ga jama’a tsaitsaye agun anata hayaniya,mami ta tambayi jama’ar dake tare da ita,daya cikinsu ya mata bayani
”yarinya ce aka kawota daga gidan mahaukata zata haihu,ta jima agunsu ana bata magunguna ashe ba mahaukaciyar ba ce,to da suka kawota sai kuma suka yi tafiyarsu suka barta,kuma bazata iya haihuwa da kanta,ba don bata da isashiyar lafiya da zata iya jurar naquda,shine ake ta neman wanda zai sanya hannu kan fike din da za’a mata aikin an rasa mai yin signing tunda ba’asan kowa nata ba,shine aka fito da ita daga gadonta aka sanya wata akai kafin asan yadda za’ayi da ita”haushi takaici da tausayin yarinyar ya kama mami duk da batasan ko wacece ba,fada ta dinga yi sosai
”saboda tsabar rashin imani,ko cikinku ai a samu mai saka hannu dai,sanadiyyar haka fa tana iya rasa ranta,kuma idan ta mutu shikenan ta mutu a banza sabida bata da gata bata da galihu ko”da wannan fadan da takeyi suka qarasa gun da take kwance tana matagugu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button