ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

ta bi dakin da kallo ya sake kyau ya canza,cike yake da tsafta da qamshi,wani kewar dakin ta kamata,sai ta cilla mayafinta da jakarta saman kujera,kai tsaye ra shige dakin maman ta fada gadonta data yi kewarsa matuqa

Tana son gadon umman nata tana jin dadin kwanciya a kai,gadon da tasha dabdalar quruciyarta a kai har yanzu katifarshi ce a kai,duk da canza kayan daki da taga umman nata tayi amma bata canza abarta ba,ta sake juyawa tana tuna rayuwarta cikin gidan quruciyarta zaqi da madaci kala kala,a haka bacci yazo ya sureta.

Can cikin barcinta taji kamar ana kiran sunanta,a hankali ta dinga bude idonta har ta budesu tarwai kan fuskar mamanta,farinciki ya kamata,yaushe rabon data ganta,tana tsaye cikin unifaorm ash colour doguwar riga da hijabi,sun mata kyau kuwa unifaorm din sosai
”ki tashi kiyi sallah kina ta bacci har anyi azahar”sai ta miqe tana mutstsuka ido
”ashe har kun dawo mama”
”eh kina ta bacci har girki akayi aka gama baki sani ba,halan bacci kika koyo”murmushi tayi ta miqe zata fice a dakin tace
”sannunku da dawowa”
”yauwa”maman ta amsa tana rataye jakar makarantar ta data daukota daga falo gami da cire hijabinta ta linke ta saka a sif

Duk inda tayi maman kallonta take,godiya take wa Allah cikin zuciyarta,farinciki fal ranta,lallai addu’a bata faduwa qasa banza,duk wanda ya kalli maryam din koda makaho ya shafata yasan ba a wahala take ba,babu shakka Allah ya share mata hawayenta na shekara da shekaru wanda ya jima yana zuba,hirarsu suke gwanin sha’awa da maman bayan baaba huwaila ta aiko mata da abincin rana don girkinta ne,bata zauna ba sai data shiga dakin baba huwailan suka gaisa,kayan dakin mama datq cire ne jere a dakin nata,ba laifi sunyi kyau kam,cike da sanyin kiki da nadama ta dubi maryam
”na godewa Allah da ya ganar da ni gaskiya tun lokaci bai qure min ba ni da yarana,maryam na cutar da ke a baya na kuma so na sake cutar da ke amma da yake ALHERI ne cikin zuciyarki sai Allah ya kareki ya kuma sanya kika mana zarrah a rayuwa,maryam don girman Allah ki yafe min ni da yara na gaba daya”
sam magiyar da take mata bata yi matq dadi ba,ko da can baya ta sani cewa shedan ke rudarsu da duhun kai,bata taba riqar baaba huwailan ba
”baaba,tamkar mahaifiya kike a gurina,nikam dama ban riqe ki ba,na yafe miki Allah ya yafemu baki daya”

Data zo cin abinci duka qannenta ne kewaye da ita suna hirarsu abinda bai taba faruwa ba tsakaninta da su ba tarihin rayuwarta,nan take jin duka baaban su ya maidasu makaranta,sosqi taji dadi don babu gatan da zaka yiwa yaro da ya wuce ka bashi ilimi(har kullum haka iyayenmu ke gaya mana,burinsu kenan (rabbirham huma kama rabbayani sagirah)

maryam ta dubi mama”ni ka ban ma ga baaban ba”
kubrah tayi caraf tace”baaba yana kasuwa,sai shida zai dawo”ta juya ta kalli mama
”kasuwa kuma mama”
”eh,kin manta da shagonsa da abdallah ya bude masa cikin kwari?”
”abdallah,a cikin kwari?,yaushe abdallahn yayi haka ba ta taba sani ba,koda mami bata taba mata magana makamanciyar wannan ba”cikin zuciyarta tayi maganar amma a fili sai tace
”au na manta fa”
”ai kullum malam sai ya yiwa yaron nan addu’a,yanzu kam qlhmdlh malam ya dauje duk wani,nauyi na gidansa da a da baya iya daukeshi,abdallah kam ba baya ba wajen alkhairi,abu daya zaki mana maryam ki wanke mu kiyi zaman aure mai cike da biyayyar miji,duk yadda kika zauna da mijinki kina nuna masa irin kalar tarbiyyar da kika samu kenan,kibi mijinki maryam ki riqe abdallah hannu biyu,bawai don arziqin da yake da shi ba,a’ah ko daya,kinfi kowa sanin cewa ba wannan ne gabanmu ba,nagartattun halayen abdallah kadai sun isa su sama masa kowacce kalar mace ta gari,ina fata kin fahimceni”kanta ta gyada
”na fahimta mama”
”Allah ya albarkaceku ke da shi baki daya”
”ameen ameen mama”ta fada cike dda jin dadin addu’o’inta

kafin ta rafi sai data tambayi yan qannenta me suke so ta saya musu kowa ya fadi abinda yakeso wanda bai wuce sabon unifoarm,jakar makaranta da lunch boxs,excercise book,lubabatu ce mai registration na placemen da sauran tarkacen kayan karatu,bata bar gidan ba sai data hadasu da lubabatun da kulu sukaje aka siyo,murna da tsalle kam sun sha shi,ko idon inna hadiza bata gani ba bare jamila ko binta,tana tsammanin ma basa gidan don idan banda isyaku data gani dazun da take shigowa gidan babu wanda ta gani cikinsu

mrs muhammad ce

????????????✍????✍????✍????
[8:18pm, 10/9/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

    ▶6⃣0⃣

Daga abi musa al asha’ari R.A yace:Manzan Allah S A W yace da ni”ya Abdullahi dan qais,shin bana nuna maka wata taska daga cikin taskokin aljanna ba?LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH”a ruwayar nisa’i ya qara da ”LA MALJA’A MINALLAHI ILLA ILAIHI”

Daga abu hurairah R.A yace: Manzan Allah S A W yace ”duk wanda ya fadi SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI sau dari za’a kankare masa zunubansa koda sun kai yawan kumfar kogi”

ruwayar bukhari da muslim

Bata bar gidan ba har baaban ya dawo,a tsaitsaye suka gaisa saboda an soma kiran sallar magariba ya daura alwala ya fice yace yana dawowa,itama alwalar tayi ta shiga dakinsu tayi sallah,tana idarwa kiran hindatu ya shigo,a dokance take cewa
”Allah yasa adda baki tafi ba,gamu nan ni da jabir”
”da daddaren nan”
”wlh,daga asibiti muke kuma akace kina gida”
”ina nan ban tafi ba baaba nake jira,sai kun iso”ta fada sanan kowacce ta kashe wayarta

Tana dakin baaban ita da shi bayan baaba huwaila ta ajjiye masa kwanukan abinci ta fice,hira suke yi abinau gwanin dadi,abin ya faranta ranta sosai,ashe akwai lokackn da zata ga rana irin wannan?,lallai komai yayk farko zaiyi qarshe,basu damu da yadda inna hadiza keta kai kawo bakin qofar dakin ba,baaban ya dubeta bayan ya ajjiye carbin hannunshi
”maryam,ina fata zaki yafemin,na dade ina daukan haqqinki,na yi watsi da duk wani haqqi naki da Allah ya doramin,tun kina mitsitsiyarki na watsar da duk wani haqqi naki da Allah ya dora min,gashi daga qarshe ta inuwarki muke samun rufin asiri,ki yafemin maryamu,haqiqa na dau darasi a rayuwata,na qiku don kuna ‘ya’ya mata,ina neman dq namimi,ido rufe,sai gashi yarin yana daf da lalacewa,Allah ya sa baiyi girma mai yawa ba,duk da haka har yau na kasa saitashi kan hanya madaidaiciya saboda na riga da na batashi na nuna masa gata,duk da haka na godewa Allah da ya ganar da ni gaskiya tun da wuri,a yanzu ne nake ganin budi cikin harkokina da nake yalwatawa iyalina nake daukan duk wani nauyinsu bakin gwagwado,kimin afuwa maryam”

Itakam bata jin dadin yadda mahaifinta wanda yayi sanadiyyar zuwanta duniya ke faman roqonta haka
”nikam baaba wallahi abunda kamin bazan taba iya biyanka ba,banga wani da zaka yimin ba na riqeka,komai qaddara ne kuma nasan haka lah ya qaddara dama zanyi rayuwata”
”duk da haka,na sani maryamu ki yafe min”
”na yafe maka baaba har abada duniya da lahira”
”na gide madyamu na gode,Allah ya albarkci rayuwarki,ki sake yimin godiya gurin yaron nan abdullahi,babu shakka babu abinda zamu iya cewa da shi,tsakaninmu da shi fatan alkahairi ne”
har yanzu mamamin abdallah bai saketa ba,yaushe ya shiga jikin yan gidansu ne wai haka?,yaushe suka saba soaai har yake musu alkhairai bai taba nuna mata ba ko sau daya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button