ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

gadan gadan ya hauro gadon yasa hannunshi ya janyo maryam dake jikinshi wanda hakan ya sanyata farkawa afirgice,ba qaramin kaduwa tayi da ganinshi cikin dakinsu ba cikin takiyar dare,bata ankara ba ya sabule hijabnta ya wurgar take gashinta mai tsaho da santsi ya warwatsu,runtse idonshi abdalah yayi yana jin tamkar an ciro zuciyarsa ana tststsagata,kamar an karata kusa da tukuba turiri kawai take maa,ya bude idonshi yaga yadda ake dambe tsakanin adnan da maryam,gashi kwance bashi da ikon tsinana komai,qoqari yake na daga hannunshi saidai hakan ya faskar,ihi yakeso ya kurama na baqinciki da takaici amma ko bakin ya kasa motsawa,sai ya koma kiran sunayn Allah ciin zuciyarshi tare da yunqurin motsa hannun nashi

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

    ▶4⃣2⃣

assalamu alaikum warahmatullah,zuwa ga masoyan ABADAN,kamar yadda aka saba ???? duk lokacin da littafi ke tafiya readers kanyi qorafi kan wani abu da ya shafi jaruman cikin littafin,wannan karon ma hakan ta faru,abinda nakeso ku sani shine bangaren rayuwar maryama true life story ne banbanci shine ita wadda abun ya faru a kanta kishiyar uwa ce ta mata hakan ba kishiyar suruka ba,hakanan na samu saqo daga gurin daya daga cikin makaranta ita kuma bangaren abdallah ne ta sani a gaske ya faru da wani da ta sani,kada ku manta babu yadda Allah baya iya jarrabtar bayinsa,gwargwadon imaninka da Allah gwargwadon girman jarrabawarka,na yarda da addu’a fiye da zaton mai zato☝????don ta yimin rana ta bani kariyar da har a nade duniya babu wani abu daya isa yamin kwatankwacin abinda ta yimin,na gani a zahiri na gani a mafarki,a rayuwa babu dole a lokacin da ka roqa Allah ya baka a take,yana iya jinkirta maka gwargwadon yadda yaso,kuyi haquri kuci gaba da bin littafin a duk yadda yazo muku don mu samu cimma manufofi da alfanu da gaci da nake son kaiku,idan kuma abun na damunka ????,a shawarce ka tara littafin har sai an wuce inda baka son ji sai ka ci gaba da karatunka hankali kwance,na gode matuqa da gaske don nasan duka qauna ce,nima ina qaunarku a duk inda kuke,MRS MUHAMMAD DINKU CE????

Ji yake tamkar ya kashe adnan,bai kuma jin ciwon lalurar data sameshi ba irin yau,saboda ya riga da yayi amanna dukkan wani abu da zaya samu bawa da sanin ubangijinsa,hakanan bazai jarrabceka ba tare da wata manufa da take alkhairi ce a tattare da kai
bai gaza ba ci gaba yayi da ambaton sunan Allah cike da neman agaji don yana jin cikin zuciya da gangar jikinsa matuqar wani abu ya faru da maryam mutuwa zaiyi

a gigice ta sake dawowa jikin abdallan ta maqale shi tana neman agaji ta cukuikuye jikinta ta dunqule guri guda,tsabar gigita ta mance da halin da abdallan yake ciki,cikin dariyar mugunta ya biyota,ya tsaua a gabansu dukkansu ya qare musu kallo kana yace
”kin daga hannu kin mare ni ga zatonki kin ci bulus?,bakisan dama na jima ina sha’awarki ba hanyar kawar da ita kawai nake nema?,sai gashi yau Allah ya ara min dama ta yaya zan yi sake ta kufcemin”
ya kalli abdallah da idanunshi suka kada suka koma jazur,dukkan wata jijiya ta kanshi ta gama fitowa rada rada
”hmmm,sarkin zuciya,ka qaraci quncin zuciyarka amma babu abinda zaka iya yau sai na cika buri na”ya sake yin kanta gadan gadan,ya miqa hannu da niyyar damqota
cikin qaraji da kuka mai quna tace
”kaji tsoron Allah,yana kallonka,yana kallin duka abinda kake aikatawa”

ga tarin mamakinta sai taga ya qyalqyale da dariya
”ki bari idan na kammala sai ki gaya min duk abinda kike son gayamin,amma a yanzu babu abinda nake ganewa kinji ko”
ya sake yunqura zai fincikota yayib da take sake lacewa jikin abdallah kamar zata koma cikinsa
cikin hikima ta ubangiji hannun sa bai qarasa kanta ba yaji saukar wani abu mai azaba a qeyarshi,ga mamakinsa ya juya don yaga wanda ya masa wannan aika aika,abdallah ne yana daga kwance yaji tamkar an kakkatse duk wani abu daya hana hannayenshi biyun motsi,cikin hikimar Allah ya bashi sa’ar janyo plate din tangaran da maryam ta zuba abinci dazu Allah ya sa mata mantuwa bata dauke shi ba,don bata barin kwano ko daya ba’a muhallinsa ba ko ba’a wanke ba

sai kuma ya juyo yayo kan abdallah,saidai ina tuni jini ya fara dibarsa ya sona tangal tangal,ganin gaka ya sa maryan saurin maida hijabinta,qofa taje ta bude ta dakin kana ta dawo ta dinga tura adnan da ragowar qarfinta tana hankadashi yana dawowa amma da yake jini yaci qarfin sa sai ta samu nasarar tunkudashi har qasan benan yana qoqarin biyota ta dawo benan a guje ta datse qofar falon kana ta shige bedroom din ma ta saka muqulli tana maida numfashi

babu abinda qirjinta yake sai dagawa sama da qasa kamar numfashinta zai dauke,har yazu tsoron bai saketa ba,ji take kamar adnan din zai dawo,hannu ta ga abdallah na dago mata da alamun ta taho,mafaka take nema ibda zata sanya kanta taji sanyi,inda zata sanya fuskarta tayi kuka,babu musa ta isa gadon cikin sassarfa ta hada jikinsa da nata,cusa kanta tayi cikin qirjinsa wani kuka ya qwace mata

shafa kanta kawai abdallah yake yana hadiyar zuciya,godiya yake ma Allah maras adadi da ya bashi damar tserar da mutuncin iyalinshi,maryam ta riga da ta zama jinin jikinshi,sukan qirjinshi kukanta yake,saidai babu bakin hanawan babu kuma cikakkiyar lafiyar rarrashi,a hankali ta dinga jin nutsuwarta na dawowa,ta dinga sauke ajiyar zuciya kadan kadan
hannun abdallah ta tuna taga yana motsi dazun,a hankali ta zagaya hannunta ta saman cikinsa ta laluba dayan hannun abdallahn,tafin hannunta ta zura cikin nasa ga mamakinta sai taji ya sanya yatsunsa cikin nata ya hade hannayan nasu gam,wata sassanyar ajiyar zuciya ta saki
”alhamdulillahil lazi bini’imatihi tatimmus saalihaat”ta fada cikin zuciyarta tare da rufe idanunta,wani farinciki taji yana ratsata,atleast tasan cewa wani ci gaba ya fara samuwa game da lafiyar abdallahn
dukkaninsu a daren babu wanda ya iya runtsawa,zuciyoyinsu tamkar anyi gobara kada ma abdallah yaji labari,ita kam takan samu sassauci kadan duk yayin data motsa yatsunta dake cikin nasa wanda yaqi sakinsu taji nashi hannun ya motsa

????????????????????????

zaune yake gabanta qasan carfet din dakin kansa nannade da farin bandeji,zahariyya na agefansa saman kujera nene na kusa da ita ta zubawa danan ido
”adnan,wanne irin mahaukacin yaro ne wai akau,sau nawa ina gaya maka ka fita hanyar yarinyar akwai lokaci ka bafi idan yazo sai kayi duk abinda kake buqata?,yanzun inda ta samu dama kasheka fa zatqyi?,baka lura da irkn yadda take mana wani irin kallo ne,dukkan zarginta ina mai tabbatar maka ita da abdallan a kanmy yake don babu bakin magana ne”

cikin fushi ya dago ya dubi nene
”to wai nene ke wanne mataki kika dauka yanzu,na rantse da Allah ba za’a zubar min da jini a banza ba”wani shu’umin murmushi ta saki
”ni yanzu duk wani mataki nawa nafison abdullahi ya wuce tukun shine babbar matsalarmu,yaron ne shegen taurin ran tsiya kamar kyankyaso…..amma yanzun bamu da nutsuwar da zamu tattauna wanna batu ku tashi kuje jibi zamu zauna,na kira malam na hayi yace baya nan sai jibi zan kira shi naji mataki na gaba,zan sanar da bintu abinda yarinyar tayi don bani da burin da ya wuce ta sata ta bar gidan saidai abun mamaki duk irin aikina bata kudina da nake taqi sallamarta hakanan ko ma samu sauqin tafiyar da aikin….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button