ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Sake maida kansa yayi yi ya kwanta a cinyarta
”soyayya gaskiya ce baby,haqiqa,babu abinda ya kai so dadi,so shine abu mafi girma dake iya sarrafa zuciya kota wanene,haqiqa so ba ruwanshi da kyau nasaba ko cancanta mulki ko wata dukiya,yakan kama mutum ne kansa tsaye ba tare da qwaqwasa qofa ko neman izini ba,maryam kici gaba da zama tawa ni kadai har abadan don Allah”idanunta a runtse suke ya riga da ya gama kashe mata jiki baki daya a hankali ta dora hannunta saman sumarsa
”ni taka ce abdallah,takace ni,ina ji a jikina saboda kai aka halicceni,kaga kuwa har abada maryam ta abdallah ce,to ta yaya jiki zai iya rayuwa babu daya barin nasa?,ta yaya zuciya zata iya rayuwa da tsagi guda ba tare da daya tsagin ba?,ka zama ni na zama kai mutu ka raba”,qanqameta yayi kamar za’a qwace masa ita yana mata godiya tare da sheqar daddadan qamshinta dake barazanar juya akalar tunaninsa

A hankali ya dinga rage mata kayan jikinta tana zaune don ba musua tsakaninsu,a yadda taga mayen sonta cikin idanun abdallah zatayi matuqar qonashi a wanann lokaci idan tayi masa musu,da undeies kadai ya barta kana ya shige bandaki yayi nashi wankan ya fito bayan ya hada mata ruwan,kafin ta fito har ya zura kayan baccinsa ya saka ‘yar hularnan tashi ka fiya naci fara ya nutsu saman abun salla,gefe taga nata kayan bacci,sai da ta qare musu kallo tanayi tana satar kallon abdallah dake salla,babu yadda zatayi haka ta juya ta sanyosu,gaba daya bata da maraba da babu dadinta daya akwai babban hijabi dogo a gun shita zura ta koma gefan gadon ta zauna,yayi sallama kana ya mata izini ta taso suyi sallah,raka’a biyu suka gabatar,addu’a mai tsaho suka yi ta neman alkhairai da samun zaman lafiya da haduwar kai a tsakaninsu sannan ya waiwayo ya kama kanta ya karanto addu’ar da annabin rahama ya koyar da mu
Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi,wa a uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi”,da salatin annabi ya rufe musu suka shafe tare

idanunsa cikin nata wanda a yanzu fargabarta ke dada yawa,girarsa ya daga yana murmushi
”wai duka tsoron nan na meye ne?”cikin nuna dakiya ta noqe kafada
”wanne tsoro?”
”gashinan ina ganinshi cikin idanunki?,kada kice a’a maryam,ina iya karanta abinda ke zuciyarki kai tsaye ta cikin idanunki,ko kin mance zuciyarmu guda ce?”
murmushi tayi cikin son nuna dakiya da jarumta amma sai ta sake ce masa
”ni tsoron me zanji”
tafa hannunshi yayi sau uku yace
”good girl,naji dadin samunki jaruma,kinsan kuwa irinki,nake so saboda irinkin ne kawai zasu iya jurata,ko da yake….nafa gasgata zancanki,kefa kince yadda kike kallon mace yar uwarki haka kike kallon abdallah kinga kenan ya kamata yau mu gane hakan ne ko ba hakan ba,uhmmm….are u ready?”
ta tuna sanda ta gaya mishi hakan cikin jirgi,take sai idanu suka raina fata,qwalla ta tarar mata,tana tsoron kada ya mata mugunta fa,cikin shagwababbiyar murya irinta me sonyin kuka tace
”kaima ba ka tsokane ni bane a lokacin?”dariya ya mata
”wasa nake miki matsoraciya,kwantar da hankalinki,babu abinda abdallah zai miki kinji,bacci zamuyi dukkan mu a gajiye muke,koke baki gaji ba ayi miki?”wata iriyar kunya ta dirar mata sai ta cure guru guda ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana dariya qasa qasa,waishi abdallah wanne irin dan kai tsaye ne?”na gaji,na fika ma gajiya”kai yake gyadawa yana sake gano yarinta quruciya da rashin wayonta
”to kin gani,so ki saki jikinki kinji,ni yayanki ne ko?”da sauri ta gyada kai kuma taji nutsuwa ta saukar mata,umartarta yayi ta samo musu plate da cups a kitchen

da hijabin jikinta ta miqe har ta soma tafiya ya kirata ta dawo,hannu ya miqa mata kana yace
”ciro min hijabina dama aro na baki ai”
sai ta dan zare ido
”amma fa jikina…”
ya katseta ta hanyar dora yatsanshi kan lips dinshi yace
”shshshsh,i know….haka nakeson ganinki,kin mance ba musu?,idan kika qi kuma to yau….”bata ma barshi ya qarasa ba ta zareshi ta miqa masa ya amsa idonsa akanta a haka ta fice zuwa kitchen din ya mata rakiyar idanu

wayon da ya mata yasa ta dan saki jikinta kadan taci naman da dan drinks,sai da ya tabbatar ta kwanta yaja mata bargo har zuwa kafadunta kana ya sunkuya ya sumbaci goshinta
”kiyi bacci baby,kina tare da ni”a hankali ta gyada kanta kana ta lumshe idanunta,shi ya tattara kayan da sukayi amfani da shi duka ya fidda zuwa kitchen

A qalla mintina talatin yayi kafin dawowarsa dakin,ya shigo ya rufe qofar da bismillah sannan ya isa ga makunnin qwan dakin ya maida hasken zuwa kala mai duhuwa ta bacci,tun dazun idonta biyu tadai rufe idin ne kawai amma fargaba ce fal ranta,tana jinsa ya gama tofa addu’ar bacci ya shafe jikinsa da ita,ya karanta mata itama ya soma shafa mata
zarcewan da ya soma yi shi ya sanyata bude idanunta ta riqe hannayensa duka,cikin rawar murya tace
”kayi alqawari fa….”
”baby bazan iya cikawa ba kimin afuwa”ya bata amsa
”amma….”hade bakinsa yayi da nata wanda hakan ya hana mata damar qarasa abinda take ahirin fada din

Ya kusa minti goma bakinsa kan kunnenta yana gaya mata wasu kalamai da suja kashe mata jiki gaba daya shi kuma ya samu daman aika mata da saqonni kala daban daban masu dauke duk wani tsoro da fargaba,cikin shu’umancinsa ya mantar da ita duk wani tsoro da wata fargaba,sai da ya mata jagoraxa duniya ta daban wadda ko cikin mafarki bata taba shiga makamanciyarta ba sannan ya fito mata da muradinsa muraran,sai a lokacin ta gane lallai wayo abdallah kawai ya mata,kuma a lokacin ta raina duk wani wayo nata,koma mata yayi tamkar mahaukacin zaki da yunwa ta koroshi ya fito farautar abinci,ba qaramin tsorata tayi ba,ya koma mata gaba daya kurma bebe kuma makaho,bai sauraran komai sai abinda yasa a gaba,cikin zafin nama yake fidda zazzafar soyayyarta data jima danqare cikin zuciya da gangar jikinsa

Bai ankara da barnar da ya tafka ba sai bayan shudewar awanni kusan shida,kuka take sosai idanun nata sun gama zama gauta saboda ja,sosai suka kumbura kamar an hura su,duk yadda yaso ta tsaya tsaiwar ta gagareta,dole ya maidata ya kwantar,tausayinta ya ratsashi,ta ya akayi ya yiwa maryamunsa irin wannan barnar?,shi kansa bai sani ba baisan lokacin da ya aikata ba,kawai sai ya koma saman gadon ya fara qoqarin janta jikinsa,a tsorace take da shi sosai saboda haka runtse idonta tayi sosai ta qanqame jikinta guri guda duk da ciwon da jikinta yake mata,bata so ya ko taba ta,gani take tsabar mugunta ce yana sane ya mata hakan bayan ya mata alqawarin babu abinda zai mata,wanne irin roqo da magiya ne bata masa ba amma yayi banza da ita,shi kurma ne ko makaho ne?
sarai ua fuskanci batason ya taba ta ne shi kuma kukan nata ne bayaso,cikin matuqar sanyin jiki da na murya tamkar ba abdallahn mami ba yace
”ba wani abu zan kuma miki ba maryam,kiyi haquri ki kwanta jikina,baki ganin yadda jikinki ke rawa kina buqatar taimako na”

cikin muryar kuka tace
”ko mutuwa ma nayi ba kai ka jawo min ba,ina zaman zama ne ashe baka da imani,so kake na mutu”duk da hankalinsa,a tashe yake sai da taso bashi dariya,ta yaya wannan abun zai kasheta,idan da yana kisa ai da mata da yawa sun mutu kenan,ganin ta kafe kai da fata bazai taimaka mata ba ya sanyashi shareta,ya sanyata cikin jikinsa ta dolenta,babau qarfin qwatar kai hakan ya sanyata taci gabq dq kukanta tana cewa baya sonta dama,bashi da bakin magana illa
”am sorry,am verry sorry,kiyi bacci idan yaso gobe saikimin duk hukuncin da ya dace da ni abdallah zai karba saboda laifi yayi miki,shi kansa yasan ya cancanci hukunci”
tun yana jin surutanta har yaji dif,ya keqa fuskarta data hada ja yaga bacci ne yayi awan gaba da ita,ajiyar zuciya ya kuma sake ya sake maidata jikinsa,sam bacci qauracewa idonsa yayi,tausayi qauna da soyyarta ke addabarsa,a hankali yaji jikinta ya fara daukar zafi da alamun zazzabi ne yake kamata,addu’a ya dinga yi,cikin zuciyarsa Allah ya kawar da zazzabin nan kada abun ya yiwa diya nan yawa,kafin asuba kuwa jikinta yayi rigif da zafi,har wani huci yake fitarwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button