ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????

Washegari tun bakwai mami ta fita tace zata ta nada excuse wa patients dinta don gobe da jibi bazata samu fita ba saboda dawowar dan lelenta wanda ya koma england cheekup bayan dawowarsa ta farko ya sake komawa tun bayan poising din da yasha,mutum ne mai qulafucin aikinsa saboda haka ya jefi tsuntsu biyu da dutse guda,bincike suke kan wani dan nijria tun kafin ya kwanta jinyarsa ta poising din da yaci wanda ake zargi da safarar muggan qwayoyi,a dan binciken da ya fara ne ya gano ya gudu england saboda haka yana gama ganin likita ya kutsa binciken mai laifin,cikin taimakon Allah
gogewa jajircewa da qulaficin iya aiki ya gano shi,abunda ya tsaidashi ya sashi qara kwana uku shine kamo ragowan abokan sana’ar tasa guda uku wanda dukkaninsu ya samu nasarar daqumosu ya aunosu nijeria gaba daya dan su girbi abunda suka shuka

jirgin da zai sauka qarfe shida na maraice ne zai sauka da su don haka tun misalin sha biyu na rana maryam ta shiga kitchen,tun jiya ta gama redy din duka abunda zata biqata ciki kuwa harda qullin waina da sinasir,miyar agushi ta soma hadawa wadda ta wadat ta da busashen kifi hade tantaqwashi sannan ta hada lemuka kala uku

bayan sallar la’asar ta hau suya wainar da sinasir,ta kammala tana shirin wanke kwanukan da ta bata ta jiyo shigowar mami,kan ta fito ta taddata cikin kitchen din,da fara’ar dai tace
”gaskiya an tayarmin da yunwata,qamshin kawai yasa naqagu inji dandanon ya yake,tunfa daga waje maryam nake jiyo qamshin nan,kai yau kice Abdallah da santi kenan”
murmushi tayi
”ko na zubo miki mami?”
sai da takalli agohon dake daure atsintsiyar hannunta sannan
”a’ah,jirginsu Abdallah ya kusa sauka,sauri zanyi na shirya kafin a daukoshi,idan naci abincina kuma ai masha qorafin don me banyi jiranshi ba”

sallamar zubaida ta ratsa dodon kunnensu,mami ce ta amsa mata tana fadin qaraso kitchen din

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:51 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

      ▶1⃣4⃣

Sallamar zubaida ce ta katse hirar tasu,mami ce ta amsa mata tace ta qaraso suna kitchen
taci ado ta cake cikin code lace dan ubansu wanda kana ganinshi kasan ba qananun kudi aka kashe wajen siyanshi ba
orange ne don haka ya haska baqar fatarta,tayi kyau sosai
”mami zamu je airphort taro ya Abdallah” ta fada tana dan sunkui da kai
”Allah ya tsare sai kun dawo”
”ameen”

har ta juya mami tace
”am…zubaida,cikin ayarin su zai iso,ina ganin zaifi idn kika jira isowar a gida ko”kada kai tayi
”mota ta daban da tasu ai mami”
itama kan ta kada ”shikenan sai kun dawo”

sai da ta fice mami ta dawo da kallonta kan maryam
”zan haurq sama maryamu,idan kin kammala kema kije ki huta,sannunki,lallai kin aikatu”
”to mami,sai kin fito”ta fada cikin
murmushi
sai da ta sake biyawa ta dining din ta tabbatar komai yayi neat kana ta wuce dakinta

wanka tayi ta sauya kayanta zuwa atamfa dinkin riga da skert,gashinta kawai ta kama ta daureshi da qaramin ribbom saboda bata fiya sa babban ribbom ba kasancewar gashinta akwai tsaho da cika,gefan gadonta ta koma ta zauna bayan ta dauko man da zata sjaf ta soma sjafawar a kasalance tamkar mai tausayin kada ta jima fatar tata ciwo,haka kawai take jin wata kasala na saukar mata,ji take kamar ta lwanta abinta tayi bacci

bata kammala shafa man ba ta jiyo jiniya da hayaniyar motoci cikin harabar gidan,a hankali ta miqe ta isa bakin window din dakin ta dan yaye labulen,bata hango komai yadda ya kamata sai dan abunda ba’a rasa baba kasancewar window din ba dirwct harabar gidan yake kallo ba ya dan fi karlata wani sashen,na doguwar valcony dinsu,bugu da qaro jama’ar da auka shigo gidan cikin motocinsu wadanda dukansu yan rakiya ne

tawagar mutanen suka biyo ta cikin valcony din tanan ta hango zubaida wadda fuskarta ke a dinke tsaf da alamu cikin bacin rai take

yana tsakiyarsu,saidai dukansu ya fisu tsaho,tafiya yake cikin hanzari wanda alamu ke nuna cewa cikin kuzari da qoshin lafiya yake,fari ne sol wanda yasa ya zarta duka jama’ar dake tare da shi hasken fata,ko ba’a gaya mata ba ta fuskanci shine abdallan mamiyawan jama’ar dake baibaye da shi ya sanya bata iya ganin fuskarshi saboda juya kanshi da yayi daya bangaren yana magana da wani saurayi da sauran jama’ar dake gefan nashi,abu uku zuwa hudu zata iya fadi a kanshi suit ne a jikinsa baqa wul mai sheqi wadda ko da bakasan kudin sutura ba kallo daya zaka mata ka tabbatar bata qananen kudade bace,sumar kanshi cike take kuma akwance luf ba tsayayya tamu irin ta hausawa ba,tafi kama data jaruman fina finan india ko larabawa,sai abunda ke saqale bayan kunnenshi guda daya wanda take gani gurin masu aikin tsaro,saidai wannan mai azabar kyau ne haka nan shima baqi ne

har suka kammala wucewa tana tsaye a gun,ita kanta batasan me ya tsaida ta din ba,sai daga bisani ta saki ajiyar zuciya hade da sakin labulen ta koma ciki ta lalubo hijabinta ta zura ta tayar da sallah don wasu guraren har sun idar

mami na tsaye qofar sashenta harde da hannayenta,duk yawan ‘yan rakiyar abdallah bai hanata gano yaron nata ba,yayin da murmushin farin ciki yaqi bacewa fuskarta,daga hannun hagun falon kuma haj nene ce tsaye ita da zahariyya,idonsu tsaye car kan abdallah da zubaida wadda a yanzu ta bar bin bayanshi ta nufo inda suke tsaye
zahariyya ce ta tabe baki”don Allah nene dubeta,aikin banza shegiyar yarinya kawai mahaukaciya,wai har wani murna take da dawowar abdallah,don Allah ki barni da ita nene wallahi sai na gyara zamanta”

dafa kafadar zahariyyan tayi tana wani murmushi da na kasa fassara shi”um…um,kinga matsalarki kenan zahariyya gaggawa,idan bakiti wasa ba zaki bata mana plan,ki bar zubaida tayi yadda take so loka ci ne fa,kuma ke kanki kinsan nasan me nake yi ko?”
”to amma nene wallahi idan ba muyi taka tsantsan ba zata zame mana matsala”
”ita din ubanta,ni na haifeta ko ita ta haifeni,ki rabu da ita dai a yanzu,akwai lokaci kamar yadda na gaya miki”
”ko tazo kada ki mata maganar”nenen ta fada da sauri ganin zubaidar ta kusa cimmasu,dama mutanen dake falin ne suka hanata isowa da wuri

har isha’i maryam na jiyo sauran hayaniyar jama’a,don haka tana idar da sallar isha’in tayi rigingine abunta bisa gado,kusan goma saura tunanin mamanta ya fado mata,layin hindatu ta shiga nema saboda muryan maman da takeson ji,saidai tayi rashin sa’a is switched off,tsaki taja cikin rashin jin dadi a ranta tana raya cewa da ta dauki albashinta na farko cikin abunda zata yi harda siyawa maman ta waya sabuwa da kuma power bank mai aiki da hasken rana

tana tsaka da tunane tunanen nata taji an turo qofar dakin,mami ce wannan karon cikin kwalliyar atamfa super mai kalan blue maidan turuwa,abunka da fara sai tayi tas
”a’ah maryamu kwanciya akayi?”
”eh wallahi mami”ta amsa mata tana mai miqrwa daga kwanciyar da tayi tana maida daurin dankwalinta da ya zame
”a’ah,yi kwamciyarki abinki,ai kinsha aiki bsna tasheki ba”
tana saka slipper dinta dake bakin gado wanda mami ta bata take amfani da shi tsakanin edroom din zuwa parlour zuwa kitchen
”ba komai mami me kije buqata”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button