ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

”hmmm um”hindatu ta fadactana turo baki,maryam ta juya ta dubeta
”ya akayi bakin ki da magana kenan”
”wlh akwai,haka kawai zaki narka albashinki ki siyi abincin gida wanda har wadancan mutanen za’aci,jamila ma da suke qaryar arziqi bata taba siyan gallon din mai ta ajjiye tace kowa yayi amfani da shi ba sai ke da kike nema da guminki,a jikinta kawai zaki ga samunta ita babarta da ‘yan dakinsu”

kumin afuwa kuyo maleji da wannan,a bini bashi

mrs muhammad ce ????

????????????✍????✍????✍????✍????
[9/17, 12:52 PM] 80k: ABADAN22
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
murmushi maryam tayi
”akwai bambanci tsakanin jamila da maryama,mama ce mu ta haifemu uwa ta gari,mai nuna mana hanyoyin alkhairai da samun dacewa duniya da lahira,yayin da su kuma inna hadiza ce ta haifesu,kowanne mutum da kika gani yana kyauta ne da abunda yake hannunshi yake kuma da shi na alkahairinsa ko sharri,ma’ana duk abunda mutum yayi miki na sharri to abunda ke hannunsa kenan sharrin,ke kuma kada kice za kiyi amfani da abunda yake hannunki na sharri ki maida masa da martani,nuna masa ke alkhairi ne da ke,kada ki damu da sai wani yayi abu zakiyi,idan kina da dama kiyi din,kuma ki qudurce cewa kinyi ne saboda Allah,to sai kiga koda wanda kika yiwa din bai gani ba baki da haufi don kinyi ne domin Allah kuma ahike bada lada da sakamako”
cikin hikima maruam ta ragewa hindatu haushin da take ji na abunda tayi shirin yi a gidan nasu,har ta rakata super market din dake bayan layinsu ta siyi cartoon na macaroni taliya da couse couse,galoon na manja da man quli,dan madaidaicin buhun shinkafa,ta siyawa mamanta kayan tea complete,har da su cornflakes saboda hindatun
ledar da mami ta bata ta atamfofine guda biyar ciki da sabulai masu tsada sinqi biyu mamanta bawa guda biyu hindatu daya ta ware biyu zata bawa huwaila da hadiza,yara suka samu suka dauko musu kayan hindati na biye da su yayin da maryam tayi gaba
sallamarta atsakar gidan tayi arba da baban nata,cikin fara’a ta nufeshi tana shirin tsugunawa tace
”baba,barka da warhaka”yayin da shi kuma ya tareta cikin hade fuska ba kuma tare da amsa gaisuwar ta ba yana fadin fadi
”lafiya ,ya akayi me kika zo yi?”
”ya salam,taya za’a raba mjtum da gidan mahaifinshi koda kuwa aure yayi ballantana ita da bata yi aurenba?”take zantawa ita da zuciyarta
”zuwa nayi na gaidaku baba,kusan wata guda ban ganku ba”
”amma dai maryamu ina cewa…..”maganar tasa ta katse lokacin da yara suka soma ahigo da kayan suna ajjiyewa
”yaya,kai,wannan kuma daga ina?”
”siyayyar adda maryam ce”hindatu ta bashi amsa lokacin da take sallamar yaran da naira goma goma ladan dako
”uwarta ta siyowa kenan?”baban ya fada yana duban kayan
”a’ah baba,na dukka gida ne,ga wannan baba a sa mana albarka”ta ce tana ciro naira dubu biyar ta miqa masa
washe baki ya shiga yi
”ah,lallai haihuwa mai rana,maryamu dukka haka,basuyi yawa ba?”
mirmushi ta danyi zuciyarta fal mamaki
”basuyi ba baba”
”ah lallai wannan gidan aiki ya karbeki,to Allah yayi albarka ya bada miji na gari”ya fada yana irga kudin fuska qunshe da fara’a
ko banza taji dadin addu’ar da yayi mata,tunda dai uba uba ne ba’a canzawa tuwo suna,sai take jin ranta yana mata dadi
ina wuta inna hadiza ta saka maryam,qememe taqi karbar atamfar da ta bata din ai ita tafi qarfin atamfa wallahi,su yanzu atamfa saidai su bayar,ita kuwa huwaila hannu ta saka ta amshe kayarta tana tunanin gobe idan Allah ya kaimu taje kasuwar bakin rimi ta saida barta ko dubu biyar suka bata ta rage son tuni bokan uwani suka soma tatsarta,ita kuwa hindatu ta kalmashe tace gaba ta kaita,
”aikin banza aikin wofi,wa ma yasan daga inda kudin suka fito,an tura yarinya yawon karuwanci tana samo kudi tana kawo muku kuna karbewa an fake da gidan aiki aka kaita,a dai juri zuwa rafi da tulu diban ruwa wata rana zai fashe,ke kuma na dawo gareki munafuka makwadaiciya,an baki abu kinsa hannu kin karbe,to ni nafi qarfin atamfa wlh ehe”
”Allah ko?,Allah sarki,mu gani a qasa mana wai inji kare ance ana suna a gidansu,idan akwai uwar makwadaita ta duniya to kece kakarta,kwadayin ne ya sakk cusa ‘yarki inda bata da gurin zama,kuma da sannu unguli zata koma gidanta na tsamiya”ta yaue labulen dakibta ta shige tabar inna hadiza na ci gaba da babatu da sharrence sharrance kala kala
lokacin da maryam ke sallama da mama tana shirin ficewa daga tsakar gidansu zuwa soron jamila ta danno kai zuwa,ta cake ado cikin wata yar ubansun shadda dinkin riga da skert na rashib arziqi,qam rigar ta kamata har boobs dinta na yowa sama,babu zancan mayafi sam atattare da ita sai daurin zamanin nan da ake kira ture kaga tsiya,waya take tana taku cikin isa da qasaita tamkar wata diyar qaruna
”yanzun nan na fito daga gidan mu hadu kawai a ni’ima guest palace din,amma fa gaskiya wannan karon bazan kuna ba gida zan koma,ok sai na iso”daidai lokacib da ta kammala wayar,bangazar kafadar maryam din tayi sannan ta juyo a wulaqance ta qare mata kallo,wata mahaukaciyar dariya ta saki tana ci gaba da kallonta
”sannu adda maryam,ana nan ana fama ko,ko da yake dai….”ta fada tana kuma kallonta daga sama har qasa
”ba laifi naga kin dan canza,ko an fara bin kwalta ne?”
waniabu ne ya tokarewa maryam dim maqoshi,rainin hankalin ya fara isarta dukan ya mata yawa,tayi mata uwarta ta mata,batasan lokacin da ta daga hannu ta zabga mata mari ba,ba ita kadai ba hatta da hindatu tayi mamaki,tsawon shekarun da suka dauka bata taba gwada yiwa wata cikin maraina wayon ta haka ba
”kan can uba,kut,me nayi miki,ko ko tsabar baqin ciki da qyashi ne…”
”kika ci gaba da magana ina mai tabbatar miki zaki kwashi haqoranki a qasa,banza jahila dabba wadda batasan inda yake mata ciwo ba”
tsit tayi da bakinta don taga irin bacin ran da bata taba gani cikin idanun maryama ba,gaskiyar hausawa dake cewa wargi ma guri shika samu
daga haka bata dada ba ta mewayeta tayi wucewarta,dadi kam tamkar maryama ta taka rawa saboda farinciki,mama ma wannan karon bata ce uffan ba,don tsan yau da gobe tafi qarfin wasa,fitarta waje babu inda idanunta suka kai sai kan jabir dake zaune mazaunin direba,idanunshi qur bisa qofar gidan tamkar dama an sanar da shi maryam din na fitowa,mamaki da tausayi suka cika maryam,jabir ne wannan,jabir ne ya koma haka,ina gayu davtsaftar jabir suka tafi?,me yake faruwa da jabir me ya sameshi?,mamakinta bai sake daduwa ba sai da taga ya dauke kansa daga gareta tamkar ma bai taba saninta ba
cikin matuqar sanyin jiki take takawa har ta isa bakin titi ta tari napep tayi gida
lokacin da ta isa gidan tuni anyi sallar magariba duhu ya riga ya shigo,ba haka taso ba taso ne ta koma da wuri ta dora musu dinner din,saidai lokacin ya riga ya qwace mata,kitchen din ta nufa kai ysaye bata ko doshi dakinta ba,mami,ce gaban gas din tana ta hidimar hada abincin,yayin da kuna dan shagwabar nata ke tayata da dauko wannan dauko wancan
”idan banda rigimar abdallah don Allah ina kai ina girki?,nace ka…”sallamar maryam ta katseta
”sannu mami da gida,har kin dawo?”ta fada tana ahirin amsar aikin daga hannunta
”yauwa maryamu ya kika barosu?”
lafiya mami suna gaidaki?”
”kinga maruamu barmin nayi yau dai daya ki huta kema,nima na wasa qwaqwalwata ko?”mami ta fada tana hanata aikin da take qoqarib karba
”ayyah,mami da wuri ma naso na dawo lokaci ne ya qwace min”
tsaki abdallah ya ja hadi da barin miqo albasar da yakewa mami ya koma ya zauna
”ki bata mami aikinta ne,idan baki bata ba ma acikin albashinta na wani watan”
yau ranta abace yake tana jinta daidai da duk wanda ya taba tane,hakan ne yasa ta maida masa raddi
”babu damuwa,mami ina jinta ne tamkar mama na ne saboda haka babu ciniki tsakaninmu,ko ba kudi qimar shekarunta sun biya in mata aiki”
baki ya tabe kamar mace
”gaskiya ne naga kina amsar albashinki,ai da,sai kice kin yafe”
murmushi tayi cikin gatse,sanann cikin qasa da murya ta yadda mami da ta tafi sink wanke albasa ba zata ji ba
”kada ka manta haifata akayi yadda akayi yadda aka haifeka,aiki nake kamar yadda kake wa qasarka aiki da albashi ake biyanka,am not a servant,ciniki kuma ko tsakanin da,da uwa halas ne”
tofa baki yasan me zai fada tuni fuskar ‘yan maza ta sake hadewa
a zafafe yayi niyyar maida raddi saidai isowar mami gun ya katse masa hanzarinsa,tilas ya hadiye abunda ya qunso
”zan zuba miki albasar maryamu kafin nan ki shiga daki kin ajjiye kayan hannunki kin sauya kaya ko?”
”to,mami na gode”maryam ta fadi gami da juyawa ta bar kitchen din,abdallah ya bita da kallon zaki san koni waye,yayin da ta daga kafadu alamun dake nuna masa am ready
mrs muhammad ce
[9/17, 12:52 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
???? ▶2⃣3⃣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button