ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

ya janye idonsa yana sauke ajiyar zuciya,har yazu nauyi da zafin da yake ji a qirjinsa yana nan babu ainda ya ragu duk da faman turereniya da yake masa amma sam ya gaza cimma nasara,cike da kasala ya danna madannin tafiya keken ya nufi dakin da shi cikin wani rin yanayi na jin kadaici da zazzafar qauna

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[8:50pm, 9/30/2017] Huguma????: [3:02pm, 9/30/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

      5⃣1⃣

Allah S W A yana fada cikim alqur’aninsa mai girma”haqiqa ji da gani da zuciya dukkansu abubuwan tambayane (ranar alqiyama)

cikin wata surar kuma yana cewa”ku cika alqawari lallai alqawari abin tambaya ne (ranar qiyama)

Da sauri sauri mami ke tafiya har ta isa ga sashen nenen,nenen ta taras kwance male male tana zabga ihu saboda tashi data kasa yi,zubaida da danan na durqushe kanta suna qoqarin dagota
ta qarasa gabansu tana shirin taba nenen tana tambayarsu
”me ya sameta,lafiya?”zubaida ta bude baki dom bata amsa,da sauri nene ta sake saka wani ihun tana fadin
”wayyo Allah na,kada ku kulata,kada kuyi mata magana”
itadai zubaida da batasan me hakan yake mufi ba tayi zaton ko qwaqwalwar nenen ce ta samu matsala
”wallahi faduwa tayi ne,bamusan me ya sameta ba”ta bawa mami amsa da haka don batasan me zata ce mata ba

idanu adnan ya zq
aro don yasan babu shakka a yau dai asirin jikin mami ya gama karyewa don sun qetara sharadinsa
”Allah ya tsine miki dai albarka zubaida,haihuwarki bata qare ki da komai ba,kin sake jawo mana wata asafar,kin karya mana asiri”nenen ta fada hawaye shabe shabe,kallon rashin fahimta mami da zubaida ke mata,tuni adanna ya juya ya fice mami ta bishi da kallo

ta dawo da kallonta ga zubaida zata mata magana ifanunta ya sauka kan cikinta sai ta kasa magana ta tsaya kawai ta zuba mata idanu,udon zubaidan ya cika da qwalla don kusan duk gidan babu wanda take ganin mutumci mituncinsa kamar mamin,babu wanda yace komai nenen ta sake sakin ihu
”adnan kaje ka duba min yata zahariyya,kada su hallakamin ita”cikin tashin hankali,mami ta kalli zubaida
”kamata mu kaita sama na mata allurar barci ko zata dawo hayyacinta”
”wallahi bintu kada ki sake kice zakimin allurar bacci,lafiyatq qalau,jikina ne kawai yayi nauyin kuma zai warke,na tsaneki wallahi bintu taurin ran danki abdullahi duk shi ya jawo mana wann masifar da muke ciki”

kiran sunan abdullahi ya sanya gabanta faduwa har sai data kirq sunan Allah,haka suka kinkimeta da qyar suka iya haurawa da ita saboda azanar nauyinta,mamin ta yi mata allurar barcin,tana ta surutanta da su basu fahimvi komai ba ciki saboda basu san me ta qulla ba da haka bacci yayi awon gaba da ita

Ta fito daga sashen nene ta nufi sashenta tana dafe da kanta don tun sanda ta kira sunan abdullahi kanta yake mata ciwo,suna take ta nanatawa cikin zuciyarta
ta qarasa bedroom dinta ta shiga tayi wanka ta daura alwala ta bada faralin sallah,har yaznu ciwon kan uaqi saukar mata don haka ta balli magani ta sha ta kwanta,babu jimawa nannauyan bacci ya dauketa

Yana zaune kan kekensa yayi kyau cikin jallabiyya fara sol,fuskarshi qunshe da murmushi yana kallonta,itama shi take kallo,a hankali ya fara tahowa gabanshi tana miqa masa hamnu saidai duk sanda ta kusa zuwa dab da shi keken da yake kai sai yayo baya da shi taga ya mata nisa

Sai ta fara binsa da gudu keken na sake tafiya da shi saidai yana fuskantarta fuskarsa kuma dauke da murmushi,sai da sukayi tafiya mai nisa kana keken ya tsaya cak,sai taji an,dafa kafadarta da sauri ta waiwayo,maryam ta gani tsaye kusa da ita tana murmushi,ta nude bakinta zata kira sunanta bat taga sun bace mata gaba dayansu,dube dube ta dinga yi amma ta nemesu sama ko qasa ta rasa,wani rami ta gani a gabanta ta tafi a hankali ta keqa sai ta hangosu ciki suna zaune,ji tayi luuu ta tafi itama zata fada ciki

firgigit ta farka tana ambton sunan Allah gami da dafe kanta dake sara mata kamar zai tsage gida biyu,tafi minti talatin a haka sannan taji sannu a hankali ciwon kan yana raguwa yana raguwa har ta daina kinsa gaba daya,sai ta jita sawai kamar wadda aka kunce daga sarqa
”abdallah,maryam”ta fada a hankali

Kamar wadda aka tsikara ta dago da kanta ta miqe da sauri ta sanya hijabinta ta fito,hanyar sashen abdallahn ta nufa kanta tsaye tana tafiya wasu abubuwan da suka faru suna fado mata tamkar mutumin da yayi mafarki yake tuna abunda ya faru,kallo daya ta yiwa sashen nasa jikinta ya gaya mata ba lafiya ba,qofar na nan a lallauye yadda su muugu suka yi mata ranar da suka zo nemansa,jikinta babu qwari ta shiga ciki ta dinfa duba ko,ina da ina ta,iya qurar da bangaren yayi kawai ya isheta amsar cewa gidan ya dade babu mai rai a cikinsa,hotunan abdallahn ta dinga bi tana kalla bata ankara ba kuka ya subuce mata,zaman dirshan tayi saman carfet hawaye masu dumi suka shiga turereniyar fita daga idanunta

”ina ka shiga abdallah,ina ka tafi ka barni”abinda ta donga fada kenan a hankali cikin kukanta
mafarkin da tayi dazun ya dinga dawo mata tar kamar a lokacin takeyinsa,babu shakka ta tabbatar abdallah da maryam duk inda suke suna da buqatarta,suna da kwadayin ganinta
maganganun nene suka sako kai suma
kada kuyi mata magana,shikenan kun karya min asiri
asiri?
asiri wanne iri take nufi,wa aka yiwa asiri kuma akan ne ya karye?duka daga shigowarta gidan a tau tunaninta ke ta mata shawagi,mutanen da ta gani sun fita daga gidan kamar ta taba ganinsu cikin gidan,cikin wani dare cikin kuma wata rayuwa data yi a baya,rayuwar data dinga jinta kamar rayuwar cikin mafarki,cikin rayuwar ta dinga tsinto halin da taga abdallah,abunda ya faru da ita ranar da zata soma rayuwar mai kama da mafarki,a hankali tunaninta ya dawo zuwa yau,maganganun nene sunqi daina yi mata amsa kuwwa a kunne,a dazun sam hankalinta bai nasu muhimmanci ba sabanin yazun data dage kai da fata sai ta tuna dukkan wani abu da nenen ta fada,ficewar da adnan yayi da sauri daga gidan
”taurin ran abdallah ne duka ya jawo mana halin da muke ciki,idan da ya mutu salin alin da mun huta”
maganar nenen ta qarshe kenan sanda take surkuda mata allurar bacci
taurin ran abdallah?
ya mutu?abdallah kenan abdallah na?

tambayoyin sun mata tsauri da yawa,saidai data hada dukkan abubuwan dake wulgawa cikin idanunta sai taso sansano qamshin wani abu wanda ya sata ta qarasa shugewa rudani na haqiqa,ita kadai ke fadin duk inda abdallah yake sai ta nemoshi
ba zata iya rayuwa,cikin duniya ba cikin salama ba tare da tasan ina abdallah yake ba,wanne hali yake ciki?,a kullum addu’arta shine Allah yasa ta riga abdallahn mutuwa,zata masa addu’ar samun juriya da qarfin gwiwa kan rashinta,sabanin ita da bata da wanda zai mata wannan addu’ar,ta yaya zata jure rasa abdallah da mahaifinsa ta iya ci gaba da ingantacciyar rayuwa cikin dunuya

A hanzarce ta kima sashenta ta wuce bedroom dinta kai tsaye,kayan jikinta ta sauya ta dauki muqullin motarta,haqiqa dukkanin wani zatonta game da yadda rayuwarsu ta cukurkude lokaci guda ra dorashi ga nene,duk da ta sani wani bawa,bai isa ya dora maka wani abu ba face da izinin ubangiji amma akwai silar komai,nene ita ce sila haka zuciyarta ke gaya mata
ta bude motarta ta shige tana qoqarin tashinta usaini ya qaraso
”hajiya zaki fita gasu ibrahim kuma na zuwa”ta dubeshi kana tace
”idan sum qaraso kowa ya koma bakin aikinsa na maidashi,gobe idan Allah ya kaimu zamu tattauna da ku duka”ta samu damar fada sakamakon ambaton Allah da take yi cikin zuciyarta wanda hakan ya taimaka qwarai da gaske wajen zaunar da nutsuwarta cikin jikinta
Allah yana fada cikin alqur’aninsa mai girma
(KU SAURARA,TABBAS DA AMBATON ALLAH KADAI ZUKATA KE NUTSUWA)
Babu inda yafi dacewa ta dosa irin gidan kawunta wanda yake a yanzu tamkar mahaifi a gareta,mutum ne mai nutsuwa qwarai da fahimta babu bata lokaci ta fice a gidan kanta tsaye ta nufi can

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button