ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

”Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahla,wa anta taj’alil hazna iza shi’it sahla”addu’ar da mami keta maimaitawa kenan fili da zuciyarya cikin sassarfa take biye da maryam suka gifta su nene dake labe jikin window dinsu suna jiran jin abinda zai biyo baya

Yadda ta barshib hakan suka sameshi,a raunace mamin ta isa gaban kujerar ta zube,gaba daya rungumoshi tayo tana kiran sunanshi,ita din ma saidai kallo da ido daga bisani ne hawaye ya gangaro daga ianunshi saboda ganin mamin nashi na kuka haiqan babu kuma baki ko hannun lallashinta,kjran sunan Allah kawai sike daidai lokacin da nene ta shigo dakin a rude kamar gaske

kallon da abdallahn yake mata ya sata tasha jinin jikinta,saidai ta nasar kawai don babu baki ko qarfin yin wani abu a kanta,tana ma sa masa tsammanin wuta zai qara zuwa lahira,
wani kallo ta jefi maryam da shi tare da zabura ta kai mata duka”me kika yi masa muguwa azzaluma”
mami ce ta tare dukan
”haba nene”cike da haqiqancewa tace
”wlh ban yarda da yarinyar nan ba bintu,daga aure jiya jiyan nan ace mutum ya kamu da irin wanna lalurar?,anya ba mayya ya aura ba bintu?”
”me ya kawo duka wannan zancan nene,muyi ta lafiyarsa ma mana”
kuka ta dinga yi haiqan tana fadin duk daren dadewa asirinki sai ya tonu shegiya mayya daga jiya zuwa yau kin lashe kurwar yaro saboda tsabar shahara a maitadaga bisani saiga zahariya da adnan,abun nasu ma sai ya zama over acting,don mamin ce ke masu suyi shiru

????????????????????????

Ranar basu kwana gidan ba cikin asibitin amalam aminu kano suka kwana,cikin kwana biyar babu irin gwajin da basuyi masa ba,saidai komai ya nuna normal yake qwaqwalwarsa spinal code dinsa da zuciyarsa kai har hanta da qoda duka sai da suka duba saidai result sai yazo komai normal

A lokacin zaka tausaya wamami da maryam idan kaga yadda suka koma,duk da qoqarin boye cutan da ake saboda yanayin aikin abdallan,shi kanshi ya rame saboda tashin hankalin da yake gani cikin qwayar idanun maminshi da maryamu

cikar shi sati guda suka koma gida mami ta bada umarni ayi musu visa cikin satin zata fita da shi,kafin nan daya daga cikin manyan security dinsa mubarak wanda yake babba ne cikin masu tsaron lafiyanshi da hisham amininshi ke taimaka su mamin gun kula da abdallah,kamar daga shi zuwa toilet da sauransu,mutum ne mai matuqar kirki mubarak kamar hisham,har albashinmubarak din mami tace zata dada yace baya buqata,babu irin alkahirin da abdallah baya musu don haka bashi da abunda zai sakq masa da shi sai ta wannan hanyar,haka hisham babu komai tsakaninsa da mamin sai fatan alkhairi da sa masa albarka.

Batun fitar da abdallahn da za’ayi yayi masifar daga hankalin nene ta soma zaton kada fa a kaishi wajen ya samu sauqi haj bintu ta dawo musu da hannun agogo baya,don nene ta gama tsorata da irin kallon da abdallan ke binsu da shi duk lokacin da suka shigo duba shi
bata bata lokaci ba ta koma gun malam na hayi ta zazzage masa bakin jaka tare da qarin buqatunta

????????????????????????

Misalin qarfe sha daya ne na safiya suka gama waya da mama ta kirata don jin jikin abdallahn,tana shirin ajjiye wayar taga har sha daya da minti goma,mamaki da fatan Allah ya sa lafiya maryam din ke tayi jin shiruchar yanzu mami bata leqosu ba

mawuya cine qarfe takwas ta gita bata shigo ta dubasu ba,haka nan ba zata tafi ba sai mubarak da hisha amininshi sunzo sun gyara abdallah ita kuma maryam din ta shirya breakfasy ta gyara bangaren nasu ta miqawa mamin break din ta bawa abdallan da kanta sannan taje tayi wanka,to yau kam duka mubarak ne yayi hidimomin shi kadai ita kuma tayi saura,da taga shabiyun rana ta kusa sai ta sanya hijabinta taga gwara taje ta duba mamin,don ta tabata ko bata da lafiya ba zata iya zama ba sai tazo ta gansu

sai da ta sake leqawa bedroom din abdallah ta taddashi har yanzun baccinsa yake don ko break baiyi ba,a haka fes da shi sakamakon kyakkyawar kulawa da yake samu,sai ka rantse lafiyanshi lau,kyau dac kwarjininsa duk suna nan sai ‘yar rama da yayi,tausayi yake bata sosai,ta sake girmama kadaitar zatin Allah,dan adam ba’a bakin komai yake ba,yanzu kake mutum yanzu kake ba mutum ba,duk kuwa kyau asali dukiya da kake da shi idan yaso sai ya maidaka abun Allah sarki
ta share hawayenta sannan ta fito daga sashen,sai data tsaya ta tabbatar ta qulle ko ina don yanzun bata yadda da kowa ta barshi daga shi sai abdallah idan ba mami ko mubarak ba

Ba zato taji ansha gabanta,da sauri taci burki tana dubanshi,adnan ne ya tsaya yana qare mata kallo kamar wani tsohon maye
”babe ina zaki haka?”duk wanda ya fito daga tsatson nene yanzu haka ta tsaneshi bata qaunar ganinsa,hakanan taji bata qaunar koda hada inuwa guda da su,tsaki ta ja kana tabi ta gefansa da niyyar rabeshi ta shige,sai ya sake binta ya tare hanyar yana fadin
”haba baby ki tsaya ki saurareni mana,nifq sonki wallahi nake ki bani dama mu huta abinmu,da kyaunki da komai kin tattare kanki guri daya kin batawa kanki lokaci wajen jiyyar wancan nakasashen,kada ki cuci quruciyarki mana baby,ki bani hadin kai ni kuma na miki alqawarin biya miki kowacce iriyar buqata kike da ita”.

dan ya tsanta ta nuna shi da shi
”ka bani hanya na wuce malam ko baka ji ba”
”common baby ki…..”
batasan lokacin da ta daga hannu ta tsinka masa mari ba cikin zafi da huci tace
”ni ba irin matan da kake tnani bace,hakanqn ni ba butulu bace irinku,nakasashen mijina ya fiye min kai da yan uwanka kai da duka ma danginka,daga rana irin ta yau kada ka kuma kuskuren tarata da banzayen magnganu irin wadan nan,banza shashaaha bani hanya na wuce”
”ni kika mara,wallahi zaki san ba’a ja da ire irenmu,zaki san kin sanya hannunki kin mari adnan”
”na marekan,sai me,na mari banza na mari wofi?”ta fada bayan ta masa wani kallon banza ta kewayeshi ta shige gun mamin

Baaba uwani kawai ta taras itama tana qoqarin fitowa akitchen da alamu wanke wanke ta gama,suka gaisa a mutunce tana tambayarta mai jiki,ta amsa mata da sauqi kana ta tambayeta mamin
”hajiya tana sama,nima tun jiya da yamma rabina da ganinta,tace dqi da yammacin jiya kanra na mata ciwo zata ta kwanta,to tunda ta hau kuma har yanzu bata sauko ba”
”bari na dubata to,Allah yasa lafiya”inji maryam wadda ta fara taka benan
”ameen,kice ina mata sannu”inji baaba uwani dake ficewa daga sashen
”zata ji”

knocking tayi ya kusa goma kafin taji cikin murya kamar ta fada fada ance waye ne?”a sanyaye tace maryam ce”
ta kusa minti talatin kafin ta bude qofar bedroom din
mamin ce fes da ita ikin lace da alama bata dade da gama wanka ba saidai babu make up a fuskarta kamar yadda taje a hade kamar wadda aka aikowa da labarin mutuwa ,kusan zata iya cewa bata taba ganin kwatankwaci yanayin a gun mami ba,kullum cikin fara’a take.
fuskar maryam qunshe da murmushi ta dan rusuna tana gaida mamin,duk da adaqile take amsa mata bata kawo komai cikin ranta ba,tayi tsammanin ciwon kan ne ke damunta

Shiru ne ya ratsa tsakani bayan ta gama gaishetan
”wai lafiya malam kin min tseye a gaba na?”ta fada cikin sautin fushi
a tausashe tace
”ah…..dama ji nayi shiru baki shigo ba,shine nae bari inzo in duba ko lafiya,ga abdallah ma baici abinci ba saboda rashin shigowarkin”
”banga damar shigowar bane,ni baiwar idan ubanku ce,siyata kukayi da zanta muku bauta,ok….na ganoki ma,wato bani da lokaci sai naku ko?,to kada Allah yasa ahima yaci abincin kinibabbe,ruwansa ne daga yau kada ya kuma cin abinci a duniya,ni da zaya mutu ma da bai hutar da muta ne ba,mtswee aikin banza shine kika zo kika taahi mutane suna cikin hutawatsu,to wannna ya zame miki na qarshe da zaki sake takomin saman ma,duk abinda kuke buqata ki tsaya daga qasa har sai na sauko,kinji na gaya miki”
daga haka ta ja qofarta ta bame ta bar ta anan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button