ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

abdallah shine shugaban jami’an tsaro na farin kaya wato S Sna nijeria gaba daya,wanda aikinsa kansa na buqatar ya zamo cikin kulawa da tsaro na musamman

bata da lokacin zama agida kasancewarta cikakkiyar likita kan fannin matsalolin da suka shafi mata,wannan ne yasa ta bayar da cigiyar amintacce ko amintacciya wanda ya qware kota qware afannin girki,to qawarta aminiya ta ce hakan ne yasa ta bani cigiya ni kuma naga ke kika fi cancanta da wanna aikin maryam,ina fatan kin fahimceni abunda kuma ya shige miki duhu kina iya tambaya ta”

shiru tayi domin tana jin abun da kamar wuya,sam bata ji ya kwanta mata ba aikin,tamkar aikatau zata tayi,kenan tunda aikin dafa abinci zata gidan wasu?,anya kuwa zata iya amsar tayin maman,amma tana jin nauyinta ,ba zatq kallon tsabar qwayar idonta tace mata a’a kai tsaye ba,kusan minti biyi sannan ta ajjiye numfashi
”ina ganin mama zanje na sanar da maga batana tukun,idan yaso duk abinda suka yanke akai zan sanar miki”
”yayi kyau,hakan dai dai ne maryam,wannan shike dada nunamin hankalinki da kaifin tunaninki,amma ina fatan bazaki watsa min qasa a ido ba”
”insha Allahu”
ta fada ka a qasa”
a haka sula rqbu bayan ta baiwa hindatu dubu daya tace ta siyi kayan kwalliya

cikin mota hindatu ta isheta da karadin wallahi yaya maryam ki amshi aikin nan
murmushi kawai tayi
”yarin ya ce ke hindatu har yau baki da hangen nesa”
”to,ya maryam meye aibu a ciki?”
bata amsa mata ba sakamakon jin ringing din wayarta da tayi ta soma kiciniyar cirota dqga aljihun jakar,raliya ce mai kiran
”hello ummin fadil”
”na’am mommyn fadil kina ina ne?”
”kin ganni a hanya na dawo ne a wata unguwa”
”yauwa don Allah ina son ganin ki ne ya za’ayi?”
”babu damuwa bari kawai na qaraso”
”yauwa ta gurina”
dariya ta bata tace ”sai na qaraso”ta maida wayar jaka sannan ta yiwa mai adaidaita bayanin inda zai juya da su”

????????????????????????

”daga ina kuke da yammacin nan ne?”raliya ta tambayi maryam sanda take dire musu drinks
”hmmm,wallahi kinga haj atika ce tayi kira na,wai ta samamin aiki gidan marigayi abdul kareem mai nasara”
sai taga fuskar raliyan ta sauya ta dan tsuketa
”ba zaki koma wani aiki ba,aure zakiyi maryam”ta gada kai tsaye tana kallon maryam din
ba tare,da kawo komai cikin zuciyarta ba tayi murmushi
”banda abinki qawata ba sai Allah ya kawo mijin ba?”ta fada cikin rashin kulawa
”Allah ya kawomiki miji maryam”sai da taji qirjinta ya wani irin buga
”miji?,wa ya gaya miki,qarya ne ni babu mijin da na samu”
matsowa tayi sosai ta kama hannayen ta
”maryam kin amince da ni kin kuma yarda da amincin dake tsakaninmu?”
”me ya kawo wannan tambayar kuma raliya?”ta tambayeta cikin yanayi na shiga duhu
”maryam so nake ki auri nasir mijina”

a hagunce take kallon raliyan,jo tayi lamar ta doka mata guduma atsakiyar ka,gani take kamar ba’a hayyacinta take ba”raliya,me kika sha yau,ko baki da lafiya?”
murmushi tayi
”nasan zaki fadi haka maryam,amma ras nake,kuma nasan me nake,cewa nayi mijina nake so ki aura nasir”
”shi ya aiko ki lo ke kika aiko kanki?”ta tambaueta tana mata kallon ba a hayyacinta take ba
”ni na aiko kaina tare da amincewarsa”
zame hannayenta tayi ta miqe
”idan kin warke kya kirani muyi maganar da kika rani domin ita,don dai wannan ban daukeshi da muhimmanci ba”
kamo hannunta tayi
”zauna maryam,wallahi a hayyacina nake,kuma lafiyata lau”

wani kallo ta watsa mata”sake ni raliya,ni ‘yar halak ce kuma nasan halacci na kuma yi imani da akwaishi,idan haka kike to ni ba haka nake ba,idan kuma nasir din ne ya saka ki to ki gaya masa ni maryam ‘yar halak ce”ta zame hannuwanta ta fice yayin da raliya ta bita tana qwala mata kira amma ko waiwayota bata yi ba,hindatu dake farfajiyar gidan tana waya itama wucewar maryam din ta gani sai binta tayi a baya

kuka zata yi ne ko ihu?me kuma yake shirin faruwa da ita?me yasa guguwar rayuwa ke walagigi da ita?,yau wai amiyarta ke gaya mata ta auri mijinta,ta ina ta yaya ma zata iya auren mijin raliya ko su biyu ne suka rage a duniya,ko da suka ke gida mama kasa gane kanta tayi,don tunda ta shigo gidan dakinta ta wuce kai tsaye,cikin damuwa maman ke tambauar hindatu me ya faru da maryam din
”ni dai mama da mukaje gidan hajiya lafiya lau muka fito,kuma iki ta samar mata gida alhj abdulkareem mai nasara,amma dai mun biya gidan anty raliya,to nidaiina waje bansan me suka tattauna ba naga dai ta fito da sauri ma biyo bayanta”
”alhj abdulkareem mai nasara?”mama ta maimata sunan don ba boyayyen mutum bane,mai arziqi ne na gani a fada wanda akayi qiyason duka nigeria babu wanda ya kama qafarshi

”to Allah ya kayuta,indai raliyance ai ba’a ashiga tsakaninsu,idan kuma aikin ne ma zamuji,qyaleta hindatu,nasqn zata min maganar da kanta”don shaquwar dake tsakaninsu yasa maryam bata boyema maman tata duka damuwarta

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????✍????
[9/17, 12:50 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

      ▶9⃣

kwana guda da yini daya bata ce da maman tata komai ba,itama zuba mata idon tayi bata tambayeta ba

kwana na biyun ne qarfe uku taji sallamar raliya,tana kwanve can cikin dakinsu saman katifarta,don yanzu zaman daki da kwanciya kuma ta aira wanda hakan baya rasa nasaba da yawan tunanin da take fama da shi,sai da gabanta ya fadi lokacin da tqji suna gaisawa da mama ta fadi mata tana cikin dakin

jawo dankwalinta tayi tana dauraqa tare da qoqarin yashi duka a lokaci daya,raliya ta iso bakin katifar ta zauna bayan ta shimfide fadil dake sharar bacci a gefanta
”na gode diyana,na gode”
”ai ni ke da godiya”ta fadi tana sake matse fuska
”wai ni zan ta kiranki maruam amma kiqi dagawa?”
”kadan ma kika gani matuqar kina kan qudirinki,nan da dan qanqanin lokaci zansa almakashi na datse igiyar mu’amala ta dake,tunda ba son Allah da annabi kuke min ba,so kuke ku cutar da ni”
dafe bakinta raliya tayi tana kallon maryam din kamar yau ta fara ganinta,ta sani babu shakka ba qaramin baci ran maryam din yayi ba tunda har ta iya furta mata haka,tafi kowa sanin halinta na rashin son fada da tashin hankali

”sonki muke kuwa maryam,saidai ke dake ahirin juya manufarmu ta alkhairi ki maisheta ta sharri,meyw aobu cikin aurenki da nasir maryam?”kafeta tayi da ido cikin bacin rai tace
”baki bar maganar,nan ba kenan ko raliya?”
”ta yaya kikeso nabar alkhairin da na hango miki ha wofanta kenan a banza?”
”lallai babu shakka kin gaji da hulda da ni…..ina zuwa”sai ta yunqura ta miqe kana ta fice

mintina kadan sai gata sun shigo tare da mama
”wai me ya hadaku ne da raliyan?”maman ta tambaya tana daga tsaye ba tare da ta zauna ba
”mama kinji abunda raliya ke fada kuwa,ba shakka ina tsammanin ta haukace ne,wai mama na auri nasir mijinta fa take cewa”
ba shiri mama ta nemi giri ta zauna,ta dubi raliya sosai
”da gaskene abunda maryama ke fadi?”
cike da tabbatarwa ta girgiza kai
”eh mama haka ne,ni a ganina ni da maryam mun zama daya,na yadda da ita na kuma aminta da kyawawan halaye da dabi’unta,na tabbata ba zata cuce ni ba,to mama laofi ne don na gayyatota tazo mu zauna qarqashin inuwa guda?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button