ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya miqe ya isa gaban madubinta ya daidaita hular bisa kanshi kana ya sake dawowa inda take
”wanne saqo kike da shi gun imna wuro,qauyen ni’ima zamu je,yau idan Allah ya nufa zan zama angon mero”
batasan lokacin da ta daga kanta ba,ta yi masa wani birkitaccen kallo ido cikin ido,wani irin zazzafan kishi baqinciki da takaici ya lullubeta
”naga kina duba na maryam idan da magana kiyi”ya fada yana sake matsowa kusa da ita tare da riqo hannayenta ya sanyasu tsakiyar tattausan tafin hannunsa,a zafafe ta fusge hannun nata kana cikin tsananin fushi da bacin rai da kuma masifa tace………..

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[4:28pm, 10/10/2017] Huguma????: [3:31pm, 10/10/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

      ▶6⃣1⃣

An karbo daga Anas dan maalik R A yace: Manzan Allah S A W yace”dukkan dan adam mai kuskure ne,mafi alkhairin masu kuskure sune wadanda suke tuba(idan sun aikata kuskuren kuma bazasu sake komawa ba)”

Tace cikin wata iriyar murya mai dauke da tashin hankali
”jeka…..jeka nace,kaje tunda ka fadi abinda kake son gaya min lallai saqonka ya isa”tayi maganar cikin zafi da juyewar kalar qwayoyin idanunta
ya sake matsota yana fadin
”to kima me nayi don Allah maryam,ina cewa ke kika bada damarcda,zan qaro auren ko?,tunda na baki dama na ganin canji kafin dawowata saidai har naje na dawo din banga wani canki ba,it means abdallah jeka auri ero ko?”

Idanunta cikin nashi tana dubanshi kuka takeson tayi saidai ta kasa
”dama kana sonta din abdallah na dade da sanin hakan,toma meye donta ka aureta,hakan na nufin yankewar numfashin maryam da qarewar rayuwarta aduniya?”ya fuskanci ta fara ficewa daga saitinta,don haka sai ya miqe yana sake saba babbar rigarsa yana shirin ficewa tare da cewa ”Allah ya kyautq,Allah ya baki haquri,sai mun dawo”
tsintarta kawai yaui a gabansa tana tura qofar hadi da jingina jikinta da qofar,hawayen da bataso su fita su suka soma turereniya kan kuncinta.

Ta jingina kanta da bango kana ta saki kuka,muryarta a shaqe cikin raahin sanin me yake fitowa daga bakinta tace
”idan kana so ka tafi kaje,amma banu inda zaka fita abdallah sai ka tsaga qirjina ka cire zuciyata ka tafi da ita,wananna wanne irin so ne?,wanne irin horo ne wanan?,na gaji…..na gaji abdallah da irin wanann horon,me yasa kake ma zuciuata irin wanann hukuncin?,me yasa ka kasa gane qirjin maryam cike yake da so da kuma qaunarka?,kasan matsayinka a cikinta kuwa?”

Kasa tsayuwa yayi har sai da ya qarasa inda take tsayen yasa hannayenahi duka biuun ya dafe shima qofar ya yiwa maryam din rumfa,numfashinsa na fita da sauri,wani irin nau’in farinciki da baiyi tsammanin akwai irinsa cikin duniya ba ya mamaye ilahirin jiki jini tsoka da zuciyarsa yace
”abdallah ya dade da sanin ya dasa qauna cikin zuciyar maryamunshi,irin qaunar da ko mutuwa kayi bata barin zuciya ta huta,abu daya abdallah yake da muradon ji daga bakin mace qwaya daya tal aduniya shine NIMA INA SONKA ABDALLAH KWATANKWACIN YADDA KAKE SONA K……

NIMA INA SONKA ABDALLAH FIYE DA YADDA KAKE SONA,FIYE DA YADDA KAKE TSAMMANI KO HASAAHE CIKIN ZUCIYARKA,ta fada cikin tare numfashinsa ba tare da ta barshi ua kammala fadar abinda zaima fada din ba,kasa daurewa yayi sai da ya ji duminta ajikinsa,sai da yaji hucin numfashinsu na gauraya guri guda,gaba daya ta narke a qirjin nasa tana sake cusa kanta cikin qirjin nasa,tsaiwa ce ta gagaresu ya jata gefan gadon suka zauna,bai janata kuka na don shi kansa badon kada ya nada yammazqn ba dira kanshi zaiyi a kafadarya ya sha kukanshi saboda tsabar farin cikin da yaji yana kewaye duniyar subhana da shi

A hankali kukan ya soma jan baya sai ta janye jikinta ta dubeshi da brown oily eyes dinta da a yau suka sauya kama
”abdallah……mero fa?”ta tambayeshi tana jan majina,dariya taso qwace masa dik da haka sai da murmushi ya wadaci fuskarsa,ta tsareshi da ido sosai da alama kishi ne ya bude fagenshi cikin zuciyarta,sai da ya lakuce mata hanci kana yace
”gaki nan,ai kece MERO NAkuma kece MAIRAMU hakanan kece DIYANA duka”
kunya ta kamata,wai haka abdallah ya qware wajen buga game ne?,bata tsammaci a fili tayi maganar na sai da taji yace
”yes abdallah good player ne,sanna kuma winner ne,yau nayi winning,the game is OVER today”shigewa jikinsa tayi yama boye kanta aqirjonsa murmushi kwance kan fuskarta,hannunahi duka ya sanya ya marabceta zuwa jikinsa yana fadi cikin dariya dariya
”ashe haka kike da kishi maryam?,amma fa kin danji kunya kadan,kishi da ‘yar qauye?,ya akahi kika aminta abdallah zai iya duban wata mace dina ma burgewa ma balle a kai ga batun so,macen ma irin mero,kin manta da su abida salma saddiqa zubaida da sauransu,basu isheni kallo ba sai mero?”

Kuma fa haka me,but ya akayi ta kasa tunanin hakan kishi duk yabi ya rufe mata ido ,ba shakka taji kunya,sake duqunqunewa tayi a jikinsa
”amma fa ta bangare guda kin burgeni haka nan kin gama biyana”ya fada yana lalubar kunnenta son so yake maganar ta koma ta sirri tsakaninsu
”yadda kika nuna kishi na na tabbatar cewa ni din ba qaramin dan gata bane”

Tayi har da ido duk da bai ganinta,can qasa muryarta tace
”amma daurin auren wa zaku a ni’ima,kuma waye zai zauna a bangaren nene na da”
”daurin auren mero,amma fa meron qauye,kuma a ni’ima din sannan bangaren nene na da anan zata zauna nata ne”
sai ta miqe daga jikinsa,hawayen ta na som dawowa
”abdallah ya zaka yimin haka,dai da zuciyata ta gama kamuwa da qaunarka zaka qara aure,bazan iya ba….bazan iya sharing wata da kai ba Allah,ina kishinka fiye da yadda kake zato”ta fada tana girgiza kanta tare da yunqurin sauka daga gadon,wayyo farinciki ya kamashi kamar yayi adungure,tuni ya riqota yana girgiza kai shima ya birkitota ta fada jikinsa ya rungumeta tsam

”Allah na gode maka da ka bani mai kishi na,nasan ba komai ya jawo hakan ba face tsatsar qauna,calm down madam,maro zata auri labaran ne nata nacan qauye na daukota ta zauna nan ne tare da mami ta dinga tayata da aikace aikace da kula da gida,tunda mamin tace tana sonmu tana son zama da mu amma ta rantse gidan mu zamu tafi,ba zata zauna tare da mu ba gudun shiga haqqinmu,labaran kuma na bashi aiki cikin kamfanoni na na nan kano,kuma banyi qarya ba YAU ANGON MERO NAKE AMMA MERO DIYA NA don na tabbatar yau ba zaki tsallake tarkona ba saikin fallasa min da bakinki qaunar da kike son binneta cikin ranki bayan akwai mamallakinta,shi yasa nayi miki adon angwayen don nima ango ne,haka daga yau ba zaki sake kwana gidan mami ba sai cikin gidanmu,gidan da na fara ginashi tun daga sanda na fara tizali dake a rayuwata,don ke dama na ginashi na dana jeshi dalili kenan da yasa a china na muku shigar sauri na zabi gadon amarcinmu don ni kadai nasan wanda zaifi dacewa da gidan,a lokacin mami na ganin na miki shishshigi batasan tanadi na yiwa kaina ba”

”wato abdallah mugun dan duniya ne?,ya iya buga qwallo son ranshi cikin hikima kuma ya saka ta cikin raga ba tare da golan ya sani ba”maryam ke gulmarsa cikin ranta bayan tayi luf a qirjinsa,tashi yayi ua fidda babbar rigar jikinsa ya dorata saman madubi bayan ya je ya sakawa dakin key,ya cire yar cikin ma daga shi saura farar vest dinshi qal da dogon wandon shaddar,gadon ya dawo ya haye yana fadin
”yau kam nima zan more soyayya mai ‘yanci”sai ya kuma bata kunya ta cusa kanta tsakani cinyoyinta,sam ta kasa hada udo da shi,kowanne sakon kunya yake sata turata ciki,anan ya lalace yana gaya mata yadda take da tasiri cikin zuciyarsairin girman matsayinta,da irin yadda yake ji game da ita,yadda sonta ya dade da illata zuciyarsa,duk inda ta duqa sai ya hanata,yace ta barshi yau ya bararraje ya fidda duk wani feelings da yake ji game da ita,daga qarshe tallafe kumatunta tayi tana kallonshi,tayi imanin ya zauce cikin so kamar yadda ita ta zauce,saidai tsakanin shi da ita batasan wanda yafi wani ba,sau biyar hisham yana kiransa yana katsewa,qarshe ma ya daga yana fadin
”kaga malam idan zaka kama hanyarka ka wakilceni shikenan,nikam a inda nake yanzu ko mami,nasan zata min uziri”da yaga yaqi daina kiran nasa sai ya kashe wayar baki daya ya jawo bedside ya wullasu ciki yana jan tsaki ya sake dawowa sukayi zaman dirshan saman gadon suna kallon junansu cike da shauqim bege da qauna

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button