ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Itama mamin ba ta nemi ko daya daga cikinsu ba kamar tasan tsiyar da abdallah ya qulla,cikin dakin sukayi sallar azahar har ma da la’asar,babu wanda yayi tunanin wani abu waishi abinci a cikinsu,wani irin shauqi ke dawainiya da su wanda gaba dayansu basu taba zaton akwai irinshi ba,a haka ma maryam na doddojewa saboda tsoro da gudun kada a tafka abun kunya cikin gidan suruka,ya qaraci fitinarsa sau biyu yana wanka tana kallonsa,
Sai da suka idar da la’asar maryam tace
”ya kamata ka tafi haka,kaga kada mami taga rashin,hankalinmu”kamar ma ba da shi take ba sai ua dira kansa saman cinyarta yayi kwamciyarsa yana fadin
”babu rashin hankali,tsakanin miji da mata sai Allah ita kanta mamin ya sani,nasam ta mana uziri,uziri kam dole ne ayi mana musamman ni Allah sarki da na jima ina faman rainon soyayyarki tun kima qwaila”ya qarshe maganar cikin salon zolaya
ta fara tura bakinta tana qoqarin tureshi
”ni daga ni,nikam ba qwaila bace ko a da dinma”yadda ta turo bakin ba qaramin sha’awa ya bashi ba,bai iya haqura ba sai da tsotseshi tas,abdallah na haukata ta iya yau da salon soyayyarshi tana zaton na gaba sawa zaiyi ta manta kowa da komai
cikin haka sukaji ana knocking,aka rasa mai magana tsakaninsu,murya qasa qasa tana zare ido tace
”mami ce fa”
kafada ya daga ya ware hannunshi kana ya miqe ya nufi qofar,ido ta sake zarowa ta biyoshi da sauri tana roqonsa qasa qasa saitin kunnanshi kada ya bude sai yasa rigarsa
”sai na cire wanann ma na zauna da boxer ki da kanta ma idan mami ce anjima zata kaimu gidanmu”kunu tasha tana miqo masa rigarsa kana ta fece bandaki ta saka maqulli ta buya,bai kuwa saka rigar ba ya budewa mamin,ita kanta sai da taji kunya ta kamata,ta kautar da kanta sanan tace
”ba kai nake nema ba diyata nake nema,kasan bata gama warkewa ba akwai sauran magungunanta da zata sh”
shima sai ya hau sosa kai don ya gama fuskantar inda mamin ta dosa
”mami ki kawo sai na bata”
hararasa tayi gafara min ni na wuce,haka zaka dirka mata maganin bata ci komai ba tun safe?,baka iya kula da mutum ba sai sakarci ka iya”ba shiri ya matsa ma ta shigo,ta kalli gadon da suka yamutsashi don akai suka yini salla ke sauko da su ta dauke kanta tana kiran sunan maryam din,gyaran murya ta yiwa mamin kamar maiyin wani abu a bandakin
sai ta samu gefan kujera ta zuan bayan ta ajjiye maganin kan madubi,shima gefan madubin ya jingina yana fadin
”kinsan kuwa mami cikin wadanda na kama tare da alhj hamza da yaranshi harda adnan?,mami ashe yana daga cikin manyan yaranshi,duka poising da naci sau biyu har da hadin gwiwar alhj hamza din”salati mamin ta saka tana tafa hannayenta
”kai Allah ka tsare mana imaninmu ya Allah,wadan nan mutane wadan nan mutane sun cika butulu,amma dama hausawa sunce idan zaka gina rakin mugunta ka ginasho gajere wataqila kai zaka fada,yanzu gashi su suka fada din,nene kam ba ita ba labarinta har yau ita da zubaida,yanzu don Allah meye ranar wanann?”
kanshi a duqe yake jijjiga kai,har yau yana jin takaicin yadda mutanen suka ci amanar mahaifinaa da mahaifiyarsa,har yau yana tuna yadda babanshi da mamanshi suka hada gwiwa aka auro nene gidan cikin halin qunci da wahala ita da yayanta amma yau da ita akayi yunqurin rusa su badon Allah baya bacci ba ya basu kariya da kariyarsa,kasa cewa komai yayi don idan ya tuna su bacin ransa ne ke tashi qwarai da gaske,badon mami tace ya qyalesu ba dukkanau sai ya nemo su yayi shari’a da su har igiya tayi saura,amma gashi a yau ya samu adnan wanda ko tantama baya yi hukuncin kisa ne zai rataya awuyansa sabida irin barna da kisa da suka dinga yi
shuru shiru maryam bata sake motsawa ba,babu yadda mami batayi ta fito ba amma ta kasa,shi kuwa abdallah na gefe yana musu dariya,da mamin ta gaji tilas tace
”aishikenan gasu nan idan kin fito din kyasha,ki tabbatar da kinsha kuma sabidayau hajiya lailan tace kisha shi”ta juya ga abdallah dake masu dariya
”ka shiga tsakaninmu ko,zaka dara da kyau musamman idan na saka ranar tarewarku nan da watanni goma”
”lokacin ta haihu kenan ta gama wankan jego” ????,ya fada qasa qasa yana duban sama
”me kace?”mamin ta tambaya,da sauri yana dariya yace
”babu komai mami,Allah bani na shiga tsakaninku ba,kunyarki dai kawai take ji”
”gafara min,ka maidani wata kakarka ko,tamu ce ni da kai”ta fadactana rabeshi ta fice qasan zuciyarta cike da farinciki,ta tabbatar cewa irin qaunar da take sha’awa danta ya samu ga matarsa ya gama samunta sai godiya ga Allah,abdallah kam ta sani bamai wasa bane gun kula da nunawa iyali soyayya tuntuni ta sani halinshi ne a qidarsa ce
Wanka kawai ta zarce da yi bayan ta ji fitar mamin,kayan jikinta ta maida don ta tabbatar abdalla yana dakin,towel ta rufawa kanta sabida jikqewa da sumar tata tayi,yana tsaye bakin madubin hannunshi daya ya dafe amdubin da shi dayan kuma yana ruqe da yar kwalabar maganin yana karanta rubutun lrabcin dake jiki,ta qarasa gaban madubin da sauri da niyyar tattare magungunan don batason ya gane na meye,ajjiye kwalbar yayi ya zare towel dake kanta yaci gaba da goge mata ruwan gashin nata na burgeshi tare da bata sha’awa
”baby kici abinci gaskiya kisha maganin nan”
”na ciwon kaine kuma ya riga da ya sauka”ta fada akunyace
dariya ya saka kana yace
”eh kam gaskiya ne,na gani ai”
ta tsargu don haka tace
”qarya nayi kenan?”ta fad tana hade rai din kada ya bullo da wani abun,ai kam bai fasa ba sai da ya ja habarta yana dariya yace
”gaskiya na sake tabbatar da irin son da mami na kemin,ya Alah ka sake jamin da ranta ka qara mata lafiya da tsawon rai mai amfani,kice gyarani kawai take yi ni ban ma sani ba,i luv my momma”sai kuma tayi shiru bata data cewa don ta tabbatar ya gani
sai ya leqa fuskarta bayan ya jawota ua rungumeta ta baya kana ya dora habarsa kan kafadarta yana cewa
”kina zaton Abdallah bai iya larabci ba ko yammata,zan baki mamaki kamar yadda na saba,kwanan nan zan daina magana dake da hausa”
dariya ta subuce mata
”ni din ma akace ban iya bane?”
”i know baby na,ke din gwanace ta kowanne bangarr tunda kika iya sace zuciyar abdallah tun ruwanki bai isa alwala ba shi kuma da ya tashi ramawa sai ya haukataki baki daya ko?”diddira qafarta ta shiga yi cike da shagwaba taba kukan qarya,anan ya lalace yana ta faman kallonta,don ba qaramin kyau tayi masa ba ji yaje kamar ya hadiyeta ya huta
Bai fita adakin ba kuwa sai da aka kira sallar magriba,yana fita ta rufe da key don tasan idan batayi da gaske ba ma yana iya cewa adakin zai kwana mata tundavyaga mami mai dauke kai ce wunin sur ta fita a harkarsu tana cikin mutanen dake ta aikin bangaren mero
????????????????????????
Tun kafin ta tashi abacci yake ta faman doko mata kira tazo yana son ganinta,har qaryar bashi da lpy ya mata,tana jin kiran nasa ta shareshi don haka jiya ya dinga buga mata qofa har ya bata kunya don baaba uwani ta jisu tana ji tana gaya masa qila tayi bacci ne
Takanas ya tashi ya taho dakin nata ya soma buga mata,cusa kanta tayi qarqashin fillow tana kuma qudunduna cikin bargon,qasa qasa yake kiran sunata
”wayyo abdallah wallahi kunya kawai kake bani,tun jiya kasa na kasa hada ido da mami na”haka ta dinga fada cikin zuciyarta,likimo taci gaba da yi har ta daina jin bugun nasa