ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????
Shida mamin ne tsaye cikin falon hannunshi dauke da kayan bacci na maza,tun dazun yake mata rigima ahifa nazai koma bangarenshi ba
”hooo abdallah,to wai ya kakeso ne da ni,na gaya maka an kwashe maka kayanka dagadakin sabida duka dakin baqi ne a ciki,gobr zasu koma garinsu ko so kake na koresu daga dakin kai ka shiga ka kwanta bayan ga bangarenka can,abinda yasa dama ban barka ka koma daga dawowarka ba gyara ne akeyi kuma an riga da an kammala an maida komai muhallinsa”
cikin shagwaba kamar wani qanqanin,yaro yace
”amma mami for god sake sai kace maye za’a kaini can ni kadai na kwana”
”ohhh,da can da kake kwanar mayen ne kai,ko wani abun ya gutsiri namanka?”
kai ya mirgina
”Allah mami ki rage sona,ina ma laifin kive in kwana dakin maryam tunda ita kadai ce,kawai sai a kaini qarshen gida ni daya tal kamar maraya”
dariya taso kamata amma sai ta dake
”anzo gurin,dama abinda yake ranka kenan kakeson fada,to anqi din,ko kunyar baqi ba zaka ji ba ka tsallakesu ka tafi dakin matarka kwana?,kaga kaina ciwo yake ka wuce sashenka kaje ka kwanta har abinci nasa an kai maka,idan kaqi kuma ka kwana a parlour shikenan”daga haka ta kama step din bene ta haye tana masa dariya cikin ranta
Sai data haye baki daya sanan ha dawo da kallonsa parlour din,yaja qwafa cikin zuciyarsa yana cewa ”duk a gama boye maryam din da yi masa wasa da hankali zasu gamu ne sai ya bata punishment”haka ya juya ya fito ba haka yaso ba cikin ransa
Cikin sa’a ya hangota tana fitowa daga bangaren meron,da azama cikin qwarewa irin tasu ta SS ya labe,sam bata lura da shi ba tana gyara yafen mayafin doguwar rigar jikinta taji an kamota baki daya anrungume tsam,ta tsorata sosai ta bude bakinta da niyyar yin magana
”kina yin magana sai na cinye lips dinki”ta saki ajiyar zuciya jin muryar abdallah ne,sai ya tuna mata lokutan baya da yake tsora tata irin hakan
Luf tayi a jikinsa ta saki ajiyan zuciya ta lumshe idonta,wani yanayi take ji na daban,dumi qamshin jikinsa gami da qamshin mint mouth fresh dinsa tare da maganar da yake mata cikin kunne suka kashe mata jiki,kwanciyarta a jikinsa ya bashi daman sa hannunshi yana shafa kafadarta zuwa yatsun hannunshi
”ina zaki je?”
muryarta low tace”charger zan daukowa mero”
”kishiyarki”ya fada cikin sigar tsokana,sai ta saki murmushi tana sake narkewa a jikinsa
”yanzun ki qyale wata mero muje mu kwanta,yau sashen mami a cike yake ya mana kadan”
ta dan zaro ido
”amma babu kowa a dakina ni ai,ni kadaice”
”i know,amma duk da haka ya mana kadan tunda tare nakeso mu kwana”
”amma mami fa…….”
”shshshshsh!”ya fada yana dora yatsanshi kan lebensa bayan ya juyo da ita da sauri suka koma suna fuskantar juna,idanunsu cikin na juna ya riqe qugunta
”bana son musu,just say yes…”sai ta sauke qwayar idonta,a hankali ta furta
”to”
”good mero na,bari naje na dauko miki kayan barcinki,nasan kina da buqatarsu”ya fada da sauri yana zaunar da ita kan kujerun dake waiting parlour din ya shige bangaren mamin
white night gown ce qal da ita mai santsi da taushi armless,rigar iyakacinta cinya,sai wandonta da ya tsaya qasan gwiwa,yana fitowa daga cikin corridor din da dakunan suke yaci karo da mami na saukowa daga step din benan
”au,baki tafi ba kenan”yayi saurin boye kayan baccin a bayansa yana fadin
”no…..nazo daukan wani abu na ne da aka manta shi ba a hada min ba cikin kayana(maryam)”baki ta tabe tana fadin
”alright,sai da safe”
da sauri ya amsa mata ya fice yana dariya hannunshi a baya gudun kada ta leqa taga maryam din bata nan tabiyo sahu
Tsaf sashen yake a gyare fes komai daidai,ya zube musu kayan baccin nasu gefan gado yana dubanta
”madam muje muyi wanka ko?”
kai ta girgiza
”nikam ban jima da yin wanka ba basai na sake wani ba”
”bazaiyiwu ba,ko an gaya miki bansan yadda kike tsarin wankan ki bane,koda kinyi da magariba idan kika zo yin bacci sai kin sake hakane?”
shuru tayi,ganin haka yasa ya fara cire kayan jikinsa,tayi qasa da kanta don batason ganinshi haka,yana kallonta cikin ransa yana fadin
”zaki sani yarinya”,da kansa ya shiga ya hada musu ruwa mai dumi da turarukan wanka kala kala cikn bathtube kana ya fito,yadda ya barta haka ya taddata bata yi wani shirin yin wanka ba,saiji tayi kawai anyi sama da ita kai tsaye ya shige bandakin da ita,bai direta ba sai da suka shiga ya ajjiyeta kana ya zagaya bayanta,zif dinta ya soma ja zai zuge sai ta hade jikinta guri guda tana fadin
”zanyi wankan,amma sai ka gama,ka barni idan ka gama na shigo nayi nawa”
ya sauke hannunta yana sake zuge zif din yana fadin
”ai daga yau babu wanda zqi qara wanka ba tare da dan uwanshi ba,daya daga cikin qa’idan rayuwar aure na kenan,sabida sunna ce ta ma’aiki,na san kin sani”
Tsori duk sai ya kamata,ta yaya zata iya tsayawa haka gabanshi?
”please abdul”
ta fada cikin rawar murya don tuni har ya kai zif din qarshe
”no maryam”ya maida mata amsa yana sabule rigar anan,ta sake sunqulewa guri guda tamkar qasa ta tsage ta shige ciki haka take ji,ya zura kansa ta kafadarta ya kai bakinsa saitin kunnensa
”ci gaba da yimin musu zai jawo na miki abinda bakyaso ne,wanan abun da kike tsoro,kinga shikenan na kashe boss din mun huta ni dake baki daya”
hawaye ya soma sauka kan kuncinta bai kuka ba don yana tsaye ne a bayanta,ga qoshi ga kwanan yunwa,cikin muryar kuka tace
”naji amma pls ka barni,da underwears dina”duk da mood din da ya shiga sai da ta bashi dariya
”a garinku kika taba gani anyi wanka da underwears?….”
”please…”tayi saurin katseshi,shiru ya danyi kamar bazaice komai ba kana daga bisani ya saki ajiyar zuciya
”alright,amma fa gaskiya kin tauyeni maryam”
kusan dai abdallah rabin wanka yayi,fatar ta kadai ta tsone masa ido,sai sheqi santsi da qyalli take,ai a ranar ya bawa idonshi abinci sosai,gyaran da tasha gun haj laila ya gama rikitashi,kusan awanni hiyu suka kwashe cikin bayin yana bawa idonshi haqqinsa,duk da bai tabata ko kadan ba don ya fuskanci a tsure take sosai
Da ido tabi kayan baccin,abdallah dan garari ne qarshe,bata da daman musa masa tunda itama ya mata alfarma,kuma da sharadin zai mata abinda take gudun indai ta kuma yi masa musu,don haka ta karba ta koma toilet ta saka su,ta kalli kanta a madubi ba shakka ba qaramin kyau suka yi mata ba,saidai kunya ta lullubeta,dukka hannayenta da singalalin qafartava waje yake,haka nan ana iya hango saman qirjinta sabida net ne mai kama da code lace a gun,ba yadda ta iya haka ta fito tana rabe rabe,sai Allah ya taimaketa ya tayar da sallah lokacin da ta fito din,tayi hamdala ta haye gado taja tattausan bargon dake kai ta lulllube jikinta tana satar kallonshi,cikin nutsuwa yake sallarshi da cika qa’idoji sharudda da dokokinta,kallo daya zaka masa ka tabbatar ya samu ilimin addinin islama bada wasa ba,hakan na daya dah cikin abinda yasa take sake ganin qimar mami take sake qaunatar shi kansa abdallan,don ada ta yiwa ‘ya’yan masu kidi kudin goro,saboda yawancinsu idan iyayenka nada arziqi mulki ko sarauta nasu damuwa da zuwa islamiyya,gani suke sunfi qarfinta,amma kuma ai baka fi qarfin shiga wuta ba ko?
don kaje gaban Allah kace rashin sani ne ya saka aikata ba daidai ba sam ba hujja bace a gun Allah,tunda ga makarantu na addini nan ko ina