ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin yana niyyar sallamewa ya sata maida idonta ta gimtse don kada ya kamata tana satar kallonshi,murmushi yayi don tuni jikinsa ya bashi kallonsa takeyi,baice komai ba har ya kammala da dukka addu’o’insa kana ya miqe ya isa gadon yana jan bargon gami da cewa
”malama mai,baccin qarya a tashi a bani,abinci naci”da sauri ta damqe bargon bayan ta bude idonta,sai da ya tuntsire da dariya ganin yadda ta haqiqance wai ita bacci take amma daga jin anja bargo har ta zabure ta miqe,ya sakar mata bargon ya koma gefan madubi ya zauna bayan ya harde hannayensa ya zuba mata ido yaga ta yadda zata tashi,ai kam kasa tashin tayi qarshe sai ta yayimi bargon ta yafashi ta cukuikuye kana ta soma yunqurin tashi
”nikam a haka nakeson ki tashi”ya fadi yana boue dariyanshi,marairaice tayi
”amma fa babu mayafi kuma yakayan yan gajeru ne”
girarsa ya daga
”yes,haka nakeson in ganki,ko kinfison naje na kalli wasu?”ya fada yana dage gira.

Sai ta hade rai ta cuno baki kishin ya motsa,miqewa tayi ta sauka daga kan gadon sai ta tsinci kanta da sauya taku,binta yayi da kallo kamar ya hadiyeta haka yake ji har ta fice a dakin ya kasa dauke idonsa daga hanyar,ba kyau na fuska kawai Allah ya mata baiwa da shi ba har diri na jiki duka ta samu,shikam Allah ya zaba ya bashi bashi da abinda zaice da ya wuce alhamdulillah

Cooler ce mai dauke da friede rice da coleslow,sai farfesun hanta daban,kusan tare suka ci abincin saidai shi ya dinga bata tana karba cike da kunya
”kunyarki tayi yawa maryam,amma…..na kusa tsige miki ita”haka ya fada yana wane kashe mata idanu

cikin jikinsa ya janyota bayan ya kashe wutar dakin yana sansanar qamshin jikinta,wani qamshi yake ji na tashi a jikinta da bai taba jin irinsa ba,sai da ya gama sansana iya son ranshi kana ya hautsinota suka dawo fuskantar juna
”hira nakeso muyi irin ta ma’aurata my dear na”ya fadi bayan ya hade tafukan hannunsu cikin juna,sai ta sunne kanta a qirjinsa tana murmushi,batasan haka zama da masoyi yake da,dadi ba,sai,yanzu ta sake tabbatarwa tabbas a baya batasan farincikin zuci ba sai yanzu
”maryam”ya kira sunanta tamkar mai rada,bai jira amsarta ba ya dora
”gobe ne zamu shiga wata rayuwa,rayuwa ce da bamu taba sanin ya take ba sai a labari,rayuwa ce da bamu taba dandana irinta ba sai a mafarki,zama zamuyi na dindin din,ina son don Allah maryam ki riqe amana ta,ina sonki da yawa ina qaunarki fiye da yadda kike hasashe ko zato,zuciyata bata taba dandanar soyayya wata diya mace ba baya ga mami na sai akanki,kinsan gausawa sunce zo mu zauna zo mu saba,ni yarima ke sarauniya,inason mu gina masarauta mai cike da ni’ima nutsuwa da kwanciyar hankali,ina so matata ta kasance tamkar qawata,qanwata,yayata mahaifiyata mahaifina da kuma ‘yata ta yadda ta kowanne bangare daga cikin mutanen nan da na lissafa zata iya taka rawa a gurbinsu”ya zarce da gaya mata ra’ayinsa da qa’idarsa me yakeso da abinda bayaso,ya kammala yana maida numfashi yayin da maryam tayi shiru har yanzu kanta na kwance a qirjinsa

Babu shakka abdallah mutum me mai sauqin ra’ayi da hali qwarai da gaske,tasha jin ana fadan halayen masu sunan,sai yau ta sake tabbatarwa hakan suke,yau din da Allah ya hadata zaman aure da mai irin sunan,wata qila sun samu tabarrakin sunan da ya zamto babu sunan da Allah yafi so irin abdullahi sai abdur rahman,dama ya bata ta fadi nata dukkan ra’ayin yaci mata alwashin kiyayewa shima,saboda zaman tare kowa,nada haqqin akan dan uwansa,bawai shi kadai ke da haqi ko keson kyautatawa ba,Allah ya fada cikin qur’aninsa mai girma cikin suratul baqara”walahunna mislul lazi alaihinna bilma’aruf,suna da(su mata)kwatakwamcin abinda ke kansu na kyautatawa(akan mazansu,ma’ana yadda zata kyautata maka kaima akwai kawatankwacin hakan a kanka)
itakam kasa fada tayi sai da ya matsanta mata kan haqqinta itama ta fadi din
”qaunarka kawai abdul idan ka bani ya isheni rayuwa,ka soni har mutuwarmu,ka riqe amana ta,kada ko tozarta qaunar da nake maka”
”har ABADA har ABADAN maryam banjin akwai abinda zai sa na tozarta tukuicin qaunar da kika yimin,idan dai wanan ne matsalarki ki goge shi daga babin matsala daga ciki kundin rayuwarki”ya fada yana shafa gashin kanta da ya sauka har kafadarta

wani irin bacci sukayi mai cike da qauna da tsantsar bege cike da shauqin juna

????????????????????????????

Da safe sai guduwa tayi don ta fuskanci abdallah na son sake tsareta wai tayi wanka ta shirya anan,ita kuwa batason abinda zaisa mami ta gane bata kwana a dakinta ba,duk da tasan babu ruwan mamin ba nunawa zatayi ba ama abun da kunya tusa gaban suruki

shigarta waitin parlour din taci kark da kibrin yana fitowa daga sashen nasu,ta sake kallon agogo qarfe shida saura na safe,da,sauri ya qaraso gareta
”yauwa dama ke nake nema na rasa yadda zanyi na ganki”da mamaki kan fuskarta ta kalleshi
”lafiya?”
sai ya hau sosa kai
”ah…mero…mero ke nemanki,tana daki”
mamaki ya cikata saidai bata ce komai ba ta nufi bangaren nasu
gabanta ne ya dunga faduwa ganin meron nafa rusa uban kuka,duk da ita kanta ta tsorata amma sai ta danne ta qarasa inda take,sai kuwa ta sake qara sautin kukan nata,take ta gane abinda ya faru da ita,bata iya cewa komai ba ta taimaka mata tare da koya mata wasu dabarun data fusknaci meron bata sani ba,ta tausaya mata tsoro ya sake cikata,jikinta duk yayi sanyi saidai bata nunawa meron ba din kada ta karya mata gwiwa,haushin labaran ya kamata,me yasa sam su,basu da haquri,atleast ai ya bari yan uwanta su koma

Kukan mero yaqi qarewa,zama tayi ta dinga mata bayani sannu a hankali ta fahimceta,ta samu ta daina kukan bayan digon bayani data mata,duk da ita ma ba sanin wani abun tayi ba ga kunya na yadda zata mata bayanin,bata kai ga tafiya ba kiran abdallah ya shigo wayar ta,da sallama tare da sanyin jiki
”shine kika gudu ko?,idan kin gama da maryar labaran din kicewa mami na fita amma bazan jima ba zan dawo,shima gashi nan muna tare ki gayawa amaryar tasa”kunya ta cikata
kada dai ace ya sani abdallan,kamar kuwa ya san me take tunanin yace
”ba wani,abu yace da ni ba,nina fuskanta da kaina,naga kuma yana buqatar training,so kada kunya ta ta qaran miki akan ta da”ya qaraahe maganar yana dariya ciki ciki

A sanyaye ta sauke wayar a kunnanta,ji take ma kamar ita yakewa dariyar,ta dubi mero dake kwance hajaran majaran ta miqe
”maigidan naki sun fita da abdallah,zan je mu gaisa da su mami,amma dole ki dinga qarfafa jikinki kada ki nunawa su inna wani abu kin fahimta”kai ta gyada mata ta yi mata godiya ta fice

Tuni har sun tashi,kasancewar mutumin qauye ya saba da tashin wuri,baya malalacin baccin nan na bayan sallar asuba,Allah ya taimaketa mami bata fito ba,don haka anutse suka dinga gaisawa daga bisani ta shige dakin da inna wuro take.

*mrs muhammad [truncated by WhatsApp]
[3:19pm, 10/12/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? *ABADAN*????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button