ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin dakinta suka shiga ita da raaliya hindatu lubabatu da kulu,baaba hadiza da hajiya atika kuwa suna sama gun mami,mami ce tasa duka suka zo don yi mata rakiya,hira suka dinga yi wanda zuwansun ya rage mata fargaba sosai,lubabatu da kulu nata kallen kallen gidan mami don yau ne zuwansu na farko,sun tabbatar cewa Allah ya yiwa adda maryam din baiwa ba qarama ba.

Raaliya ce ta shiryata tsaf cikin codenet din orange da yellow,kana ta dora mata alkyabba da mamin ta hadota cikin kayan,yellow ce mai ratsin fari,fadar irin kyawun da tayi ma bata baki ne,su kansu tsayawa sukayi kallonta,kai tsaye gin mami suka fara zuwa kana suka fice suka barta ita da ita,kallonta mamin take cike da farinciki,burinta kam ya gama cika a yau,hannu ta miqawa maryam din ba musu ta bata,gefeanta ta zaunar da ita kana tace
”maryam,da farko abinda zan fara cewa dake shine kiyi haquri,don babu wani abu da ya wuce haquri da mace zata riqe wanda zai,zame mata jagora kuma madogarar gidan aure,haquri maryam shine komai a rayuwa,kiyi haquri a duk yanayin da zaki tsinci kanki a gidan aurenki,duk wata mace da kika gani zaune gidan aurenta wallahi ba za’a rasa wata matsala da take fuskanta ba komai qanqantarta,ta wata ne tafi ta wata,qila wadda kikewa hangen ta haye ta huta da zata buda miki cikinta wallahi saikin tayata kokawa,komai dadinki da mimi wataran sai kun samu sabani,donko tsakanin harahe da haqori ma ana sabawa,na biyu riqe sirri ki riqe sirrinki ke da maigidanki maryam,koni idan bai zama dole ba bana buqatar jin sirrinku ke da abadallah,ku riqe amanar juna,ku riqe sirrin juna,ku zauna da juna cikin amana”nasiha ta dinga mata irinta tsakanin da da uwa,kuka sosai ta dinga yi har sai da mamin tace
”a’ah,ai kuma zaki batawa abdallahn kwalliyar me akayi kenan kuma uhm…..maza share hawayenki,duk da haka kowacce mace ta saba yau hashi kowa na zaune agidanta”.

Da kanta ta kama hannun maryamun har harabar gidan ta sanyata cikin sabuwar range robber baqa wul wadda kyauta ce mamin ta yi mata,tukuici ne ta bata,kadan daga cikin irin abubuwan da take ji zata iya yiwa maryamu,yadda ta kama hannun mamin itama sai ta karya mata zuciya har sai da ta share qwalla,motocine kusan shida don akwai yayar mami da qanwarta,sai yayar marigayi alhj abdulkareem mai nasara da qanwarsa,tana nan tsaye mamin har motar ta daga suka fice daga gidan kana ta juya ta koma ciki,tun daga lokacin ta soma jin kewar maryamun,bangare daya ga abdallah dake shirin tafiya shima,babu shakka kewarsu zatayi ba kadan ba,don ma ga mero nan,amma kafin su saba su maye mata gurbin maryamunta ai ba nan kusa bane

Sai da suka fara zuwa gidansu suka kaita gun mama da malam mamuda mahaifinta kafin su wuce da ita gidanta.

Wani irin yadine ajikinsa orange colour mai bala’in kyau da taushi,dinkin babbar riga ‘yar ciki da wando,fuskar nan tashi tayi wani irin kyau na musamman,hisham ke riqe da wata iriyar jaka da aka qawata ta da rubutu mai kyau suna tafe yana masa tsiya har suja qarasa gun mami,tana falon nata tana sallah ya tura qofar suka shiga,kujera suka samu suka zauna suka jirayeta har ta idar,sai data shafa addu’a kana ta tashi ta dawo kan daya daga cikin kujerun itama ta zauna,hisham ne ya fara magana
”mami gashi na kawo miki shi,ayi masa nasihar zaman aure”mirmushi mamin tayi tace”ka kyauta kuwa,shi yasa nake sonka hisham badai hankali ba”
harararsa abdallah yayi”jimin dan rqimin wayo,kana nufin zan iya tafiya banzo ga mami na ba?”
dariya ya masa don ya fuskamci yanayin fuskarshi har ya canza ya kuma san ba wani abu ne ya tabashi ba sai barin mamin da zaiyi.

”abdullahi”ta kira sunanshi da salon da bata taba ba,take ya dago idonsa ya kalleta,sai ya kasa civgaba da kallon nata ya duqar da kanshi,son ya hango magana zata masa bata wasa ba
”shi aure da kake gani girma ne da shi,daraja da shi qima gareshi,sunna ce guda ta wanda akayi duniua da lahita dominsa wato annabi muhammad S A W duk wanda ya wulaqantashi baya tare da annabi na tabbatar kuma bazaka so haka ba,a duk sanda ka dauki yarinya,aka rqbata da uwa da ubanta da inda ta taso tavgirma,aka rabata da danginta aka rabata da duk wani wanda ta saba da shi aka baka to ka tabbatar da xewa amana ce aka baka mai girma,kasan sarai hikuncin wanda ya tozaratar da amana ko yaci amana ko?,ka tuna ko yauahe cewa matarka ba siyanta kayi ba,ba baiwarka bace ‘yace ‘yantacci ya mai yanci,kada ka dinga mu’amala da ita irin mu’amalar bawa da ubangidansa,a’ah,ka mu’amalance ta wani lokaci kamar ‘yarka,ka tsawatar mata ka bata shawaea ka tausasa mata kaja girmanka,ka mu’amalanceta wani lokaci kmar mahaifiyarka,ka tausasa mata,ka kyautata mata,ka girmamata,ka mu’amalanceta wani lokaci kamar qanwarak,ka qaunaceta ka kauda duk wani abu da zai cutar da ita ko ya,bata nasabarta,ka dorata kan hanya madaidaiciya,ka mu’amalanceta kamar qawarka,ka gaya mata damuwarka,kayi shawara da ita,kuyi wasa kuyi dariya,matarka duka tana da wannan mtsayin a gareka”.

Ta dora da cewa”na tabbata har yau kana iya tuna mu’amalata tsakanina da mahaifinka wanan kawai ya isheka madubi,ya iaheka littafin da zaka dinga karantawa ko yaushe koda ban ce maka komai ba game da zamantakewa da iyali,abdallah ka guji zalunci,Allah da kansa ya fada cewa ya haramta zalunci abinsa kansa,kuma ya haramtashi a tsakaninmu,ka kyautatawa matarka,ka sauke duk wani nauyi da Allah ya dora maka,yadda kake da haqqi a kanta haka itama take da haqqi a kanka,ban yarda ka take mata haqqinta ba abdallah,iya wannan nasan ya,isheka nasanka nasan tarbiyyar da na maka,don Allah abdallah kada ka watsamin qasa a ido,kayi zama zama na haqiqa da matarka,Allah zai tsadaku ranar gibe kan yadda kuka sauke haqqin jilunanku,wallahi wannan gaskiya ne babu ko tantama aciki”
idanunshi tuni sun hama hada ja,zuciyatsji zafi take masa,karo na farko da zai rana gidan kwana shi da maminsa,a hankaki ya miqe daga mazauninsa ya isa gabanta ya durqusa kangwiwoyinshi,kana ya cire hular kansa
”mami kisa kin albarka,kici gaba da yi mana addu’a,insha Allahu zanci gaba da zama abun alfahari a gurinki”
hannunta ta dira saman kanshi kana tace
BARAKALLHU LAKA,WA BARIK ALAIKA,WAJAMA’A BAINAKUMA FILKHAIR”,ta amshi ukar da kanta ta maida masa ita saman kansa,sai ya kasa jurewa ya dora kansa saman cinyar mamin yana ajiyar zuciya,tausayinsu ya kama jisham,babu shakka ba qaramar qauna nace tsakanin wannan da da uwar ba,sai ya,kasa zama shima ya tashi a hankali ya fice,uwa ba wasa ba.

Mamin bata masa magana ba don ta saba da irin hakan,majority tun yana yaro idan zuciyarsa na quna haka yake ya dira kansa saman cinyarta har sai ya huce,don bashi da qawa a lokacin ko aboki da ya wuce maminsa(yana da kyau iyaye ku zama kune abokai ko qawa na farko wanda suka matuqar shaquwa da ‘ya’yansu kafin kowa,ta hakane zaki samu damar yiwa diyanki kalar tarbiyyar da kikeso mai kyau ba tqre da wasu sin samu damar ruguje miki ba,bawa yara damar shaquwa da aboki fiyr da iyaye da rashin jansu a jiki babbar illace,da abokin nan ko qawarnan zwta dinga shawara,ita zata dinga gayawa damuwarsa bake ba,kinga kenan zai iya dorashi kan irin tasa tarbiyyar,amma idan akwai shaquwa tsakaninku kece mutum ta farko da zai fara dinga gayawa matsalolinsa da damuwarsa kafin kowa,saidai idan kuma yayi aure Allah ya bashi mace ta gari sai ki koya masa neman shawara daga matarsa,saidai idan duka su biyun tunaninsu baikai nan ba ko mas’alar tafi qarfinsu,a kuka don Allah iyaye,tarbiyya abace mai tsada da wuya,amma a qarshenta kuma ke uwa ke zaki fi kowa mora da jin dadinta koda baki duniya kuwa).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button