ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Ita ta riqo hannunshi suka sauko qasa,ya zama kamar ba abdallah ba,qwarin rai da qarfin zuciyar nan duka babu,har dariya ta dinga masa kan cewa ya girma fa,ya kamata ya koma abdallahn sa,nan da ten months yana iya zama daddy,abinda ya sashi dariya ya kuma bashi kunya kenan,bakin freezeer suka isa ta bude ta ciro wata qatuwar leda ta sake jansa har suka fito harabar gidan inda motocin security dinsa guda uku data abokansa guda uku ke jiransa,cikin motar da za’a kaishi ta bude masa da kanta ta sanyashi kana ta miqa masa ledar”Allah ya tsare hanya,a sauka lafiya”ta fada kana ta rufe musu qofar ta koma ciki,a varanda ta tsaya har sai da taga ficewar motocin duka.
Mus’ab abokinsu ke tuqa motar,usman na gefansa baya kuma hisham ne da abdallahn,cikin salonvtsokana hisham din yace
”idan bakason rabiwa da mamin kawai mu maidaka gida sai a yiwa maryam waya ta haqura kawai”harar ya galla masa bayn ya sauke ajiyar zuciya
”mami da maryam duka rayuwata ne hisham,ka sani,ba sai na maka dogon bayani ba”tsokanarsa suka ci gaba da yi tare da yi masa shaqiyanci kala kala irin na abokan ango har suka iso unguwar.
mrs muhamma ce????
????????????✍????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶6⃣4⃣
An karbo daga Abdullahi dan salaamin Allah ya yarda da shi yace:naji manzan Allah S A W yana cewa:((ya ku mutane,ku yada sallama,ku ciyar da abinci,ku sada zumunci,kuyi salla cikin dare lokacin da mutane suke bacci zaku shiga aljanna cikin aminci))
imamut turmuzi yace hadisi ne ingantacce
gaisuwa ta musamman gareku tare da dimbin godiya da jinjina
mom hanee
fatimah zahra haske asso
zainab idris makawa(takari)
maman farida(samun wuri)
maman rufaida (manal)
hafsat mai sharif(rayuwar aure na)
Billy galadanchi(hanjin jimina)
khairat
mrs ibrahim
maman aysha(gadar zare)
ummu zainab
rabi’ah haroun
maryam gital(ba halul kitabi bace)
KAI !KAI!!, INA KUKE MASOYAN ABDAN,TO KU MATSO NA GAYA MUKU????????
????????????????????????????????????????????????????????
wannan page dinfa naku ne,duk inda kuke na sadaukar muku da shi kyauta,wanda na sani da wanda ban sansu ba,na kusa da na nesa????????????
NAGA SAQONKI AISHA GARKUWA ????????????,NI DAKE AI DUKA DAYA NE MUSULMI DAN UWAN MUSULMI NE????????,KICI GABA DA KARBAR SU AI DAMA NANA AISHA AI UWAR KOWA CE,UWAR MUMINAI R.A,NA GODE DA KIKA MIN KARAR KARBAR FANS DINA DA MUTUNTAWA KIKA BASU FURA DA NONO,ALLAH YAYI MANA JAGORA????????????????????????
????????????????????
Gida ne gini na alfarma,gini irin na gata,gini ne mai cike da tsari kyau da fasaha a cikinsa,kana shiga gifan kawai zaka tabbatarwa kanka cewa gida ne da ni’ima da kwanciyar hankali tayi kaka gida acikinsa,sanyi da iskarsa ma daban take albarkacin tsirrai daya wadatu da su,duk inda zai kasance ansa tiles cikin harabar gidan baki daya an maye gurbinsa ne da grass carfet mai ban sha’awa,duk cikin abokan nasa babu wanda ya iya tsuke bakinsa ba tare da ya yaba ba,a haka suka ajjiye motocinsu suka dunguma zuwa,cikin gidan
parlour na farko anan suka ci burki,ya dubesu baki daya babu ko kunya yace da su
”daga parlour na farko fa banjin zan iya barin wani ya shiga parlour na biyu bare na uku,saboda haka anan zamuyi sallama da ku”
mus’ab yace
”dan iska,zakayi abinda yafi haka ma,kamar a kanka aka saukar da wahayin kishi,mun gama maka amfani ai tunda mun rakoka”
dage gira hade da kafadusahi yayi
”eh da gaskiyata fa,haka kawai na kwasheku har bedroom din matata,ina da kishi gaskiya”
”muma bamu ce zamu shiga ba malam,tunda munyi na Allah ai shikenan”inji usman yana ajjiye ledar hannunshi,yana dariya qasa qaa ya dafa kafadarsa”yauwa mutumina,dadi na da kai sauqin kai”
Tsokana dai irin ta abokan ango haka sula yo masa yana ramawa,barkwanci sosai suka dinga yo kama suka juya suka fito ya rakasu,har sunyo gaba hisham ya dawo
”yauwa,inason ganinka fa”
”zaka batan lokaci kenan,na bar gimbiya fa batasan na shgo ba ma fa”murmushi hisham din yyi mai hade da dariya
”me kake ci na baka na zuba,kunnenka na tsaya na ja don naga yadda kamka ke rawar nan,wlh kayi a hankali kada ka cutar musu da diya,na sanka sarao idan kana som abu baka daukar lamarinsa da wasa”
kunnen abdallah ya turo masa yana fadim
”to daddy,ga kunnen,fadi da kyau,ko daki zan baka ne ma kusa da namu kayi sa idon da kyau”tare suka sheqe da dariya kana suka tafa
”Allah ai kaine da iua shege,kai wa yasan me zakayi ranar da aziza ta zama taka”har wani sosa kai hisham yayi kana yace
”wlh fa,na barku lafiya to”ya fada ya juya yabi sahun yan uwansa dake zaune cikin mota suna kiransa aballah ya bishi da kallo,yana son hisham mutum ne mai amana wanda samun kamarsa sai an tona,ba duka mutum bane a wannan zamanin zakamasa alkhairi ya saka maka da alkhairi,mafi yawancinsu da sharri suke saka maka sai yan kadan
Sai da ya tabbatar sun fice sannan ya isa ya rufe gate din gidan don bai kawo mai gadi ba tukun,bai koma ciki ba sai da ya tabbatar ya rufe ko ina
A hankali yake takawa yana nufar cikin gidan,iskar damina na kadashi,wani irin ni’ima ce yau lullube da sararin subhana,iska ake mai dadi da shiga jiki,gefe guda wani tawagar farinciki ne ke shawagi cikin zuciyarsa,jinsa yake cikin wata duniya ta musamman,yau gashi ga maryamunsa,cikar muradinsa cikar burinsa,sashensa ya bude ya ciro kayan bacci farare tas da towel dan qarami kana ya rufe ya dawo sashenta ta cikin parlour din gidan na biyu,a hankali ya,keta har falo na uku wanda daga shi sai wani dogon corridor wanda kana shiga zaka tadda dakunan bacci uku,sai matattakalar bene wadda saman shima ke dauke da dakunan bacci parlour toilets da kitchen,a hankali ya,haura saman kansa tsaye ya tura qofar daya daga cikin dakunan da ya gani a bude wanda hakan ya tabbatar masa a ciki maryam din take
”assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatu”ya shiga da sallama wanda hakan ba qaramin rage mata fargaba yayi ba,gefan kujerar dakin take zaune,kanta na duqe lullube da alkhyabbar jikinta,tsayawa yayi cak kana ya kingina da bangon dakin yana qare mata kallo duk da bai ganin fuskarta,ya kashe a qalla mintina biyar a haka zuciyarta na bugawa a hankali kanta na a qasa,ta tabbatar har yanzu yana cikin dakin saboda qamshin turaransa da ya cakude da nata ya lullube dakin,haka nan ya sake haifarwa da dakin wani irin ni’imtaccen yanayi,sannu a hankali ya dinga takowa gareta bayan ya ajjiye kayan hannunshi duka saman dan qaramin table na glass dake a gaban gadon,ya isa gabanta ya zube duka kan gwiwoyinshi,hannayenta ya kama ya sanya cikin nasa yana qarewa qunshinta kallo,tamkar yasa harshensa ya lashe haka yaji,sai da ya more kallonsa sannan ya dora kansa saman cinyanta yana leqen fuskarta,bai ga fuskar sosai ba sakamakon hular alkyabbar ta sanya ta yin duhu,a hankali ya sanya hannunshi ya janye hular take fuskarta ta bayyana saidai idon nata a rufe dai yake
Cikin wata sassanyar murya da bata zaton yana da ita ba taji yace”zan rayu dake zan mutu da ke ABADAN dani dake zauna”murmushi ya subuce mata don bata taba jin waqa a bakinsa ba sai a wanan karon,sai taji tafi dadi a bakinsa ma fiye da mawaqin,a hankali ta dago brown oily eyes dinta ta zuba masa,dama abinda yakeson gani kenan,shima murmushin ya sakar mata wanda saura kadan ya narka mata zuciya,ajiyar zuciya ya saki ya lumshe sexy eyes dinshi kadan sannan ya sake budesu”ya Allah ka gafartawa mami na,kayi mata albarka data sauqaqamin hanyar samunki,ta shiga lamarina” kana ya daga girarsa
”yes….zan rayu da ke har ABADA maryam,haka kuma nake fatan koda mutuwa tazo min ta daukemu tare….”