ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin baccinta ta jita aruwan zafi yana ratsata,da azama ta bude kumburarrun idanunta ta saki qara data bashi tausayi,duk yadda yaso sata ciki ruwan dumin taqi shima kuma ya kasa saboda baison kukan da take,ahi ya gama shiryata tsaf kana ya bata guri don ta tubure masa sai wani dakin ya canza ya bar mata wannan
Qarfe bakwai ya sake leqota sai ua sameta kwance kan abun sallah bacci ya dauketa,a hankali ya lallaba ya dauketa ya maidata kan gadon ya fara qoqarin rabata da hijabin jikinta saboda zafin zazzabin dake tashi a jikinta,garin haka ta bude idonta sai ta tabe fuska zata saki wani kukan,da sauri ya kwantar da ita yana daga hannayenshi sama
”ni fa babu abinda zan miki,hijabin da kika bari a jikinki qara miki zafin zazzabin yake”
kanta ta cusa cikin filo tana fadin
”nidai ka fita wallahi”
tsam ya miqe ya fice daga dakin yana waiwayenta,ta sa gefan hijabinta tana share hawayen da yaqi tsaiwa,itakam da tasan haka ake shan wuya da ta gudu wlh,ashe duk wayo abdallahn yake mata don yaga ya girmeta
Har qarfe goma na safe yana fama da ita,taqi yarda ko dakin ya shigo bare ta sha tea din da ya dafa mata,don ba girki ya iya ba,da zarar ya shigo dakin zata fashe masa da kuka,duk yabi ya susuce,ga ciwo da alama tana jinsa sossi,ya kira raaliya bai sameta ba tilas ya kira baaba uwani,a falo ta taddashi kwance kan doguwar kujera rigingine,da sauri ya miqe yana tambayar baaba uwanin
”gaskiya ranka ya dade kuje asibiti,ta gayamin tana jin ciwo,sosai hakanan ba zata iya shiga ruwan zafin ba”shiru yayi donshi ba wani asibiti da ya sani idan ba mallakin maminshi ba,don tun yana yaro acan ake bashi duk wata kulawa saidai idan abbanshi ne yace a fiddashi waje,yana kunya kuma yajewa mami da maryam a hakan,dabara ta fado masa don haka da sauri ya yiwa baaba uwani godiya yasa driver din gidansu ya maidata
Sai da ya hada girar sama da ta qasa sannan ya shiga dakin,tana kwance don bata isa ta zauna ba,ganin fuskarsa a haka yasa bata yi masa boren ba,don ta manta rabin da ta ga fuskarsa a hakan,gaban ma’ajiyar kayanta ya isa ya ciro mata atamfa da hijabi,ganin yana niyyae sa mata su ns yasa ta saki shagwababben kukan nata sai ya kauda kai yana jin ciwon kukan har cikin ranshi ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa
”ya isa,idan zaki iya ki sauya da kanki yanzu na baku minti goma”ya fada yana ficewa a dakin
Cikar mintina goma ya dawo dakin har ta sauya din kuwa saidai zanin da bai dauru ba,ya dagata ya gayara mata daurin zanin kana ya dauketa cak ya fice da ita,Allah yasa babu kowa a gidan don har security dinshi ya basu hutun sati guda,a motar ya sakata ya dan kwantar mata da kujerar sanann ya dawo ya rufe ko ina
Sunan asibitin kawai data gani yasa ta tuna cewa asibitinsu ne,idonta cike da qwalla ta dubeshi yana gyara parking na motarsa a inda taga manyan likitoci ke parking kawai a gun
”amma ya za’ayi ka kawoni gun mami abdallah baka jin kunyarta ne?”sai da ya daidaitata ya kashe kana ya jingina jikinsa da makarin kujerar ya dubeta
”ba gun mami zan kaiki ba nima ina jin kunya ai dear,akwai doctor farida ita zara ganki kin gane?”limshe idonta kawai tayi ta kwantar da shi ba tare da ta amsa masa ba,sai taji hannunsa kan fuskarsa yana share mata hawayen
”bansan ganin hawayen nan mana maryam,ki zama jaruma kinji matata,ni da nakeson shekara iwar haka na kawoki kina naquda”ai batasan sanda ta bude idonta ta watsa masa harara ba,ana fama a yanzu ma ba’a warke ba yana mata zancan naquda,shi don ba jikinsa bane wato,dariya ua qyalqyale da ita kamar yasan me take rayawa cikin zuciyarta,bai sake cewa komai ba ya ciro wayarsa ya kira reception na asibitin yace a turo masa nurse din da take on duty
Cikin minti uku kacal ta iso sanye da fararen uniforam,matashiya ce yar kimanin shekaru talatin mai yawan fara’a,ta gaida maryam ta amsa mata cikin fara’ar yaqe tana satar kallin abdallah,ranshi a hade kamar bashi ya gama qyaqyata mata dariya ba yanxun,tambayarta yake doctor farida tazo?
”eh naga office dinta a bude duk da banga wucewarta ba amma nurse halima naga ta fara shigar da files”
”mami na fa”
”office dinta gaskiya a rufe yake”ya gyada kai kana yace
”ok,inason ki bawa nurse halima din wannan ta kaiwa doctor faridan yanzu zan shigo na gantq ni da madam”a ladabce ta amsa kana ta juya ta shige,ratar minti biyar ya bada ya fito daga mazauninsa ya rufe motar kana ya zagaya bangarenta,daukarta yayi da gaske tana masa mitar ya ajjiyeta kada ya jawo musu yan kallo
”idan daukar da na miki bata jawo mana yan kallo ba sauke kin da zanyi ya jawo mana tunda kona ajjiyekin ba iya tafiya yadda ya kamata zakiyi ba”ta yarda haka dinne don haka tayi luf ajikinsa idonta aruntse duk kunya ta gama kamata
Bai damu da jama’ar dake reception din ba kansa tsaye ya wuce office na doctor farida da ita,bayan ya sauketa a bakin qofar office din ya kama hannunta,ya tura qofar kana yayi sallama,ya juya yana maida rufin qofar ta dago kanta daga laluben takardun da takeyi,mami ce zaune kan kujerar zaman likitan,zame hannunta maryam tayi tana fatan ina ma zata iya gudu babu shakka da fellawa zatayi
fes ta gane kunya ke damunsu tunda taga highlight na problem dinsu a short note din da ya bada a kawowa doctor farida, don haka sai tayi mirsisi kamar bata sansu ba ta musu nuni da gurin zama
”bismillah”abdallah yayo gaba yayin da maryam cikin lallaba takunta ta biyo bayansa,mami ta dan bita da kallo cikin tausayawa amma afuskarta ba zaka gani ba idan baka lura ba sosai,sai da tayi yan rubuce rubucenta kana ta dago da kanta ta gyara zaman glass dinta
”uhmmm,meke damun patiente din?”sai aka rasa mai magana tsawon mintina,dariya ta dinga cin mami kamar ta fito ta dara ganin yadda sukayi tsilli tsilli maryam harta fara sharan hawaye
Abdallah ya miqe yana fadin”ummm…ina zuwa,bari naje na dawo doctor ta miki bayani”sai ta kuma hade rai
”c’mon dawo mara haquri kawai ina zaka,dora min ita saman can”ta nuna mishi wani dan gado da take duba marasa lafiya kana ta dake kamar ba ita tayi maganar ba taci gaba da rubuce rubucenta gami da dauke kanta cikin zuciyarta tana tausayin maryam tare da dariyar abdallah,tunda suke bata taba ganin bala ‘yar iyar kunyarta cikin idanunshi ba irin wannan karon,sai da ya dorata kana ya taho gefanta ya tsaya
”mami,na dorata”
”doctor ce ba mami ba”ta fada cikin shan kunu,sai ya dan shafi gefan fuskarsa kana yace
”sorry……doctor”
allurai ta hada pain killer harda wadda zata sata bacci na yan lokuta kafin ta gama dubata ,don ta san da kunya musamman maryam dake da bala’in kunya,bai yiwuwa ta dubata a sake kuwa alhalin idonta biyu
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
[5:58pm, 10/14/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶6⃣5⃣
Daga abdullahi dan umar R.A.H.M yace:Manzan Allah S A W yace:((haqiqa mafi soyuwar sunaye acikin sunayenku a wajen Allah mai girma da daukaka sune ABDULLAHI DA ABDUR RAHMAN))