ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

azafafe maryam tace
”kinjifa mama irin abunda take cewa,ro billahil azim indai raliya bata sauka daga kan bakanta ba na miki rantsuwa mama har da Allah daga yau babu ni babu ita har abada”
tsot dakin yayi son su kansu aun sani matuqar maryam ta rantse akan abu to sai ta aiwatar,kuma alamu duka sun nuna irin yadda batun ke taba mata zuciya ba qarami bane,maman ce ta soma magana
”koda maryamu ta amince da maganar ma ni bazan amince ba,haba raliya aisai duniya ta zagemu,jama’a su saka mu a tadinsu,idan banda abunki ma raliya kwata kwata shekarunku nawa da yin auren,banda quruciya haka kawai kuna zamanku gwanin sha’awa ki dinga kira ma kanki kishiya uhm raliya?,na roqeki nima ki bar maganar haka nan kinji?”
qwalla ta cika mata ido ta tausayin maryam don qaunar da take mata ta fisabilillah
”shikenan mama,koda baki roqeni ba zan bar zancen ko don kada na rasa aminiya irin maryam,saidai….maryam na gode,na gode da kika nuna min iyaka ta”
duk da taji rashin dadin batawa raliyan da tayi amma sai taji kamar an tafiyar mata da wani qullutu da ya tokare mata wuya,sai taji damuwarta ta rage farashi zuwa kaso tamanin

durqusawa tayi bayan ta miqe tana qoqarin daukar fadil tace da mama
”mama ni zan wuce”
”kinga malama ajjiye fadil din ni zan daukeshi,tunda ba ke kadai bace ai uwarshi ba”cewar maruam tana yafagyalenta don yi mata rakiya,don ta fuskanci tafiya,zata yi,ta san halin raliya ciki da bai tasan fushinta koda ta tsaidata ma ba hirar atziqi zasu yi ba
”ni kadai ce mana uwarsa tunda kinqi ubansa”ta maida mat martani tana qoqarin ficewa,murmushi kawai maryam din tayi ta saba fadil din ta biyo bayanta

”halan driver ne ya kawoki?”
”ban sani ba,idonki ya baki amsa”tave da maryam din lokacin da auka fito tana gaba ita na binta abaya,mirmuahin dai ta kuma yi har beuty points dinta suka loba
”Allah ya baki haquri,yau kam ai akan gwiwa kike sai lallabe”
”a’ah,akan haba nake”
amsar da ta bata ta sanya maryam tuntsirewa da dariya har itama raliyan ta dan murmusa don fushinta da maryam ba ya wani tasiri
suna isa gaban motar ta ganshi zaune,shi ya kawota kenan,raliya ta bude ta shiga yayin da maryam ta galla masa harar lokacin da suka hada ido,dariya ya tuntsure da ita yana kallon raliya da tayi kicin kicin
”kada kice komai,don babu ruwan nasiru,kinga kanwar nan”
”babu wani nan,waye baisan halinku maza ba,to wllahi bari kaji,idan ka sake ka yiwa aminiya ta kishiya ban yafe ba koda wace ce kuwa,ke kuma kici gaba da nema masa aire kinji ko solobiyo”ta fada harda dan kama kunnen raliyan
dariya abun nata ya basu
”ni don Allah sake min kunne,tunda kin gujemu dai ba shikenan ba”
”indai irin wannan gudun ne raliya am sorry to say….zanta gudunku har abada”ta dan ja da baya ta rue musu qofar tana murmushi sanna ta dan sara mata shigen yadda sojoji suke
”Allah ya huci zuciyar ranki shi dade,oya kai kuma kaja mini aminiya ta ahankali”
”oho dai abanza tinda yau gaku a rana”ya fadi yana yiwa motar key tare da cillawa raliya gwalo
”wlh a inuwa ka ganmu,kuma duk qwaqwqwafinka ba zaka taba ganinmu a rana ba,ku sauka lafiya,sister am sorry,sai munyi waya”

koda ta koma gidan cikin al’ajabi suke tattauna zqncan da mama,maman ta kuma yabwa qwarai da irin qaunar dake tsakanin maryam din da raliya,ta musu addu’ar Allah ya dorar har tsufansu
sai a san nan ne maryam ta samu sukunin yiwa maman zancan aikin da hajiya atika ta samar mata,shiru maman tayi kamar yadda maryamun tayi tana jirqn cewa maman,shudewar mintina kusan biyu kafin tace
”ke me kike gani game da aikin,tunda kinga azahjrin gaskiya zamanki babu aikin babu dadi,tunda kin riga kin saba,hakanan zai debe miki kewa,baya ga haka harkar makarantar hindatu wa zqi ci gaba da daukar nauyinta idan har kika daina?,amma ke me kike gani mene ra’ayinki?”
”aini mama banida wami zabi sai abunda kika ce”

”kina da zabi mana maryamu zan tauye miki haqqinki ne?,amma dai abinda yafi kawai shine kici gaba da addu’a,Allah yayi miki zabi mafi alkhairi”
”ameen mama”
da haka suka saki maganar suka shiga kuma wani batun daban kuma,haka rayuwarsu take su uku suke yinta,su kashe su binne abinsu babu maiji,hakan ne ke qara haushinsu,cikin zukatan al’ummar gidan

sati guda da maganarsu da haj atika amma har yau ta kasa yanke komai a kai,kwana bakwai daidai da azahar tana sharar tsakar gida ta jiyo sallamarta,cike da mamaki ta yi mata sannu da zuwa sannan tayi mata jagora zuwa dakinsu

ruwan sanyi na pure water da alalen da sukayi ta ajjiye mata sannan ta zauna suka gaisa
”baki da kirki maryamu”haj atika ta fada tana dubanta
murmushi tayi ta dan sunkuyar da kai
”kiyi haquri mama”
”tashi kike abunki da mamanki ma zanyi magana,ko abbanki yana nan?”
”eh,bari na dubo miki”ta fadi tana miqewa,
taci sa’a kuwa yana niyyan fita ta tadda shi,ta sanar da shi sannan ta zura mayafinta ta fita gidan maman fatima maqociyarsu

mintina talatin suna cikin hira isyaku ya shigo yana zumbure zumbure
”ke kije bana yana kiranki”ya juya ya fice abinsa,maman fatima tace
”oh ni Allah,Allah ya kyauta”
”hmmmm,ameen bari naje maman fati sai anjima”maryamu tayi mata sallama ta fice

bata tarad da haj atika ba,sai babanta da mama dake zaune
”baba gani”ya fada bayan ta samu guri gefe da su ta zauna
”maryam”
”na’am baba”
”ki shirya gobe idan Allah ya kaimu ki hada duka abunda kike da buqata hajiya zata zo zaki tafi gidan nan da kukayi magana da ita ta samar miki aiki”
cikin rashin fahimta ta dubeshi
”amma baba ni ina ganin koda zanyi aikin ma ai bani da buqatar tafiya da kaya na,tunda ba wani garin bane ko?”
”ke,bani son sakarcin banza,na riga da na gaya miki,ki hada kayanki,suna da buqatar zamanki ne a can gidan,yo idan kin zauna anan din me zaki tsinana min,illa inyita ganinki baqinciki na ci gaba da damu na?,kije kawai banason kuna sauran qorafi kinji ko?”

kai ta gyada hawaye na layi bisa kuncinta,wannan sam bai dadashi da qasa ba ya miqe ya fice abinsa,kai ta hada da gwiwa ta rushe da kuka,duk yadda taso daurewa zuciyarta ta kasa
”wai me yasa baba baya sona ne mama,me nayi masa?”ta tambaya cikin kuka
”kul maryam,kada na sake jin wannan mummunar maganar a bakinki,mahaifinki ya isa da ke,saboda haka nima bana buqatar wani qorafi kibi umarninshi kawai”
bata iya cewa konai ba face miqewa da tayi ta shige dakinsu zuciyarta na zafi tare da jin tsanar wannan sabon aikin,aikin da zai nisanta ta da mahaifiyarta,zai nisan tata da ‘yar uwarta,mama binta tayi da kallo tana jin tausayin diyar tata sosai na sauka cikin zuciyarta,addu’a kawai take mata cikib ranta Allah ya yanke mata wahala,ya kawo lokacin da zata zauna ta huta cikin dakin mijinta

????????????????????

jikinta duka a sanyaye take shirya kayanta cikin sabon dan trolly dinta mai kyau pink wato ruwan hoda,hindatu ce ta rufe mata sannan ta jawo mata shi cikin parlour don bata da kuzarin da zata iya janshi

tsaye tayi cikin falon ta kasa cewa maman nata komai,don hawaye ne fal cikin idanunta da suya da zuciyarta ke mata,ji take kamar ta bar gida kenan,tana jin tamkar ta bar mamanta kenan,sai maman ce tace
”kuje hindatu jiranta suke,Allah ya bada sa’a,abu guda zan fada miki,ki riqe mutuncinki a duk inda kike,ki tsarw ksnki maryam ki kuma ji tsoron Allah,don babu wani abu da zan iya yi miki a lahira,iya kacin amfani na a duniya ne wajen tunatar da ke bin hanyar Allah,ki riqe amsna ki zauna da kowa lafiya”
kuka ta saki ta fada jikin mama,sai da taci kukanta sannan a sabule ta fice hindatu tabi bayanta da akwatin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button