ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

✊????✊????✊????✊????✊????✊????✊????????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
????????????????????????????
cike da girmamawa mutuntawa da qauna tare da qasqantar da kai nake miqa wanna shafi a gareku
IBAADALLAH wato duk wani mai suna ABDALLAH
musamman mahaifina,abin qaunata abin alfahari na,jigo na
ALHJ ABDULLAHI MUSA HUGUMA
haqiqa kai mahaifi ne daya tamkar da miliyan,mahaifine da samun kamarsa sai an tona,mahaifine daya da daya,mahaifi ne da babu kamarsa,Allah ya shige maka gaba,ya maka jagora cikin lamuranka,ya zama jinka ganinka,ya rabaka da sharrin mahassada magauta da maqiyanka,Allah ya cika maka burinka duniya da lahira,Allah qara maka lafiya da tsawon kwana mai amfani,ya cika rayuwarka da farinciki nutsuwa da kwanciyar hankali,yasa kayi kyakkyawan qarshe,babu shakka ka gama mana komai a rayuwa,addu’arka garemu na bin mu har kullum muna ganinta,Allah ya jiqan magabatanka ya maka jagoranci tare da dukkan nagartattun iyaye kamar KAI????????????????????????????????????❣
Komawa tayi taci gaba da rubuce rubucenta kafin allurar tabi jikinta tabar abdallah nan a tsaye maryam a kwance ta nutse cikin kogin kunya,cikin mintina da basu wuce takwas zuwa goma ba baccin ya fara dibar maryam,babu bata lokaci lokaci kuwa yayi awan gaba da ita ta fara anccinta sadidan dama kuma ga baccin jiya data ci bashinsa bata yishi cikakke ba
Mami ta waiga taga ta fara nisa a baccin,sai ta ajjiye biron hannunta,ta jawo wayar girke ta tafi da gidanka ta danna wasu lambobi,bayan an daga ta lissafa kayan aikin da take da buqata,ba acika minti goma ba kuwa sai ga nurse ikilima wadda ya baiwa short note ta kaiwa doctor farida,ya faki idon mami ya watsa mata harara sai ta sadda kanta don batasan laifin me tayi ba,amsar kayan mamin tayi ta nufi drower din kusa da gadon ta ajjiye saita waiwayo ta dubi nurse iklima data ci gaba da tsaiwa
”da wani abun ne?”mamin ta tambayeta tana saka hands glove,da sauri ta girgiza kai
”a’ah,ban sani bane madam mo kina buqata ta akusa”kai ta girgizw mata tana fadin
”a’ah jeki abinki,personal issue ne”
”ok,to”ta amsa mata ta fice kamar zatayi tuntube saboda yadda abdallah ke zabga mata harara,bayanta mami tabi ta sakawa office din key kana ta dawo ta soma bincikar maryam data dade duniyar bacci
Sosai mamin ta tausaya mata don ta lura ba qaramar barna yaron nata yayi ba,har sai da ta daga kai ta dubeshi don ta sake tabbatarwa abdallahn ta ne?,suna hada ido ya sunkuyar da kanshi wata kunya na jibgarsa ta ko ina,sai ua sake miqewa zai fice don ya rasa inda zai tsoma ransa
”kada ka budewa mutane qofa malam”haka kawai tace masa cikim dakiya,dole ya dawo sum sum ya zauna,ta fidda kayan yin dinki don dama ta tsammaci haka shi yasa ta bada order din a hado mata da su,shi kansa sau dqya ya kalli yadda ake dinkin ya dauke kan ya dauke kansa taigar jikinsa na tashi cike da tausayi,sannu a hankali cike da qwarewa ta gama dinkin tsaf,ta jawo paper ta rubuta sunan magunguna kana ta zare safar hannunta ta koma kan kujerarta ta zauna tana kallon abdallahn
”duk yadda zakaji kunyar maminka dai baka da kamarta,yanzu ba don Allah ysa mun hadu da nurse halima ba na amshi takardar nayi musanyan office gun farida zaka kai case din?,kana da tabbas bakinta zaya yi ahiru kan abinda taga kayi,this is d lasr warning kada ka sake irin wanann ganganci,ni mamarku ce abokiyar sirrinku ka fahimta?”kansa a qasa ya amsa mata yana sake qaunar mamin nasa,batason kowa ya zama mai jibantar lamuransu idan ba ita ba,shikam Allah ya bashi uwa ta kere sa’a
Gyaran murya ta sake yi sai da gabansa ya fadi
”and then…..”sai kuna ta danyi jim shima yayi shiru yana jiran cewarta
”is ok”kawai tace tana maida glass din idonta,takardar hannunshi ta miqa masa
”ka fita wani clinic ka siyo wadan nan magungunan,kana ka biya reception ka biya kudin ganin likita”sai da ya dago ya dubeta,kudin ganin likita kuma,shi tunda yake bai taba jin koda wasa ance ya biya din ba,dubanshi tayi ganin yayi shiru
”yadai?,ko ka taba ganin ana aiki kyauta a sibitin private,likita doctor farida kazo gani kuma na maka aikinka kaga you must to pay”sai ya sosa kai ya matsa daga inda yake din yana cewa
”ni ban taho da kudi ba doctor,atm ne ajiki na”
gira ta daga sanann tace
”ok,ai suna da p.o.s ka basu su cira,ko da yake akwai kudi hannuna bari na ranta maka ka biyani”ta fada tana jawo hadaddiyar hand bag dinta dake saman table din too match da kayan jikinta ta zaro sabbin yan dubu dubu ta miqa masa,hannu biyu yasa ya amsa kana yace
”na gode Allah ya bani ikon biya”saura kadan ta fashe da dariya ganin yadda ya wani koma duka kalar tausayi amma sai ta dake,tana son koya masa lesson ne,haka ya juya ya fita ita kuma ta saka dan labulen nan na da ake rufe mara lafiya mai tayoyi ta kare inda maryam ke kwance taci gaba da duba patient
Har qarfe biyu maryam na baccinta shi kuma mami ta shanyashi a reception yana jira,sai da ta gama da dukkan patient din nata kana ta tura wata nurse ta kirashi,kan abun sallah ya tadda mamin zaune da alama sallar azahar ta idar
”kayi salla ne?”ta tambayeshi
”ah….ina shirin…ina shirin zuwa nayi kika kirani amma bari naje nayi sai ma dawo ko?”ya fada a daburce,tsakanin uwa da da sai Allah,ganin yadda yau ya maidata kamar ba maminsa ba yasa ta dan sassauta masa
”da toilet anan shiga kayi alwalar ga abun sallah kazo kayi”
”to”yace kana ya nufi toilet din yana satar kallon maryam dake bacci har yanzu
Satar dubanshi take yana sallar,gaskiya ne maganar hausawa dake cewa da sannu wataran yaro zai zama ango,yau abdallahn ta ne ya zama ango,turo qofar dakin akayi wani matashine baqi sanye da unifaorm mai dauke da tambarin sunan asibitin ajiki,hannunshi biyu riqe da kwanduna yayi sallama mamin ta amsa tana fadin
”bashir,har an kawo”
”eh hajiya”ya fada yana dire su a gabanta,ta jawo,kwandon tana fadin
”sannun baaba uwani kaima sannunka”ya rusuna cikin girmamawa ya amsa kana ya juya zai fice wata matashiya ta shigo itama dauke da leda baqa,ita dinma fuskarra dauke da murmushi da girmamawa ta ajjiye ledan tana fadin
”mami gashi”ta ciro canjin tana miqa mata
”a’ah zainaba riqe kyasha ruwa”murmushi tayi tace ”na gode”
”a’ah nice da godiya”ta ja musu qofar ta fice mami ta janyo ledar tana dubawa,abdallah ya dan saci kallon mamin
”wo…mami…mami,wato kudin da tasa ya kai reception na ganin likita ashe sawa tayi akaje aka siyo kayan amfani da su,irinsu tea flask,rigar sawa daya cup plate sabulun wanka turare da silifas sai abin sallah duka daidai,saidai baisan me zatayi da su ba,tunanin da ya fado masa ya sanyashi yin addu’ar Allah yasa ba kwantar da su zara ce zata yi ba
motsin maryam ya ja hankalinsu,sai tayi saurin maida idonta ra rufe tana fadin dama bata farka ba cikin zuciyarta,mamin ta qaraso tana mata sannu tare da tambayarta akwai wani pain da take ji,idanunta a rufe take fadin a’ah
”to sauko a hankali ki je toilet ki wanke bakinki kiyi alwala kizo kiyi sallah azahar tayi har taso to gota,kiyi a hankali fa banda gaggawa da dinki jikinki kada ki ja masa matsala”
”wayyo Allah na,abdallah ka gama da ni,yanzu mami ce tamin dinki ma”take fada azuciyarta,mamin ta gama karantarta don haka tace
”ki saki jikinki maryamu,ko baki yarda ni maminki bace?,tamkar nina haifeki kinji”kai ta gyada sannan mamin ta kamata ta taimaka mata ta sauka