ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

a zaune tayi sallar gogan sai kallonta yake,mamin ta ganshi amma sai ta dauke kai ta jawo plate guda daya babba ta zuba musu abincin,shinka fa ne da miyar kifi da salad da tumatir da cocumber,saukowa tayi qasan gun bayan ta shimfida sabuwar abun sallar ta saka hannu ta fara ci bayan tace musu”bismillah”
tsuru maryam tayi abu goma da ashirin itamakam bata iya cin abinci tare da mamin abdallag kuwa tuni ya tsoma hannunshi dama shi sabonshi ne tare suke ci,ga kuma uwar yunwa dake addabarsa dama tunda baici abincin safe ba,rabonsa da abinci tun jiya da daddare,ganin har sun fara ci bata sanya hannu ba yasa mamin yi mata magana
”saka hannu mana ‘yata,baki ga abdallah bane”kanta aduqe ta saka hannun suka fara cin abincin gwanin sha’awa,da wanann damar tayi amfani cikin hikima da hila take dada jan hankalinsu kan zaman aure
Sai da suka qare tas tasa abdallah ya gyara gun,nurse ta kira tace ta saka cleaners su gyara aminiyy one zata ajjiye oatient,ta juya ta fice bayan ta amsa mata,sai abdallah ya zura mata ido yana neman ba’asi
”daina kallo na haka nan,anan zan ajjiyeta sai gobe zaku koma gida”
”ni wallahi dama sati biyu kika ce mami”maryam ta fada azuciyarta,fuskarsa ta dan sauya tana kure da shi
”yes,ko kuma in dauketa mu tafi gida bayan one week ta kom”da sauri ya saki fuskarsa tare da fadin ”a’ah” cikin zuciyarsa yace”da asara ai gwara gidadanci”tilas ya sawa zuciyarsa haquri yana ji yana gani
Sai bayan isha’i mamin ta barosu ta koma gida tace zata turo baaba uwani,bai ce wa mamin komai ba don yasan yanzun da yayi magana cibi zai zama qari,qari ya zama qaabaaba amma ya riga ya qudurce babu wani baaba uwani da zata kwana masa da mata
kiransa tayi a waya bayan ta fita din,a bakin mota ya taddata tana tsaye bayan ta bude side din da zata shiga,fuska a hade tace da shi
”abdallah….ka shiga taitayinka kana jina ko?,banason ci da zuci da rashin hankali,ba qaramin cutar musu da yarinya kayi ba,bana sin rashin haquri makamancin haka ya sake faruwa kaji na gaya maka,idan na haka ba matakin da zan dauka maka bazai ma dadi ba”shidai kansa na qasa har takammala ya shiga bata haquri,bata ce komai ba ta shige motarta ya fufe mata yana fadin”a sauka lafiya”bata tnaka masa ba ta kunna motarta tayi gaba,da sassarfa ya juya ya koma cikin dakin don ya qagu yaji dumin maryamansa,wuni guda yana ganin yayi qoqari
ya iso gareta inda take kwance kan gadon dakin,qafafunsa na qasa daga cikinsa zuwa kansa yana saman ta ya daudaitafuskarsa da tata
”kin ga abinda kika jawo mana ko?,haka kawai daga fara amarci zamu bige da jinya a asibiti?”
fuska ta bata tana zumburo baki
”na jawo mana?,bama kai ka jawo min ba,duka ka gama bami kunya gun mamin haka kurum”
Dariya ya qyalqyale mata da ita kana ya kama lebanta da ya burgeshi ya dan ciza a tausashe
”bake kika ce kamar mace yar uwarki kike kallo na ba,i hope kin banbance tsakanin aya da tsakuwa ko?,kin yarda abdallah ba rago bane,a karo na farko yasa an baki gado?”
kunya ta kamata ta tura kanta qasan kanshi,har yau tana iya tuna lokacin data fadi maganar,a lokacin faduwar gaba take ji da bugun zuciya sosai tattare da ita,amma sam taqi kawowa zuciyarta abdallah take so,yasan ya sata jin kunya don haka ya dora da fadin yana ya jujjuya kansa
”nima nasha kunya maryam na fiki shan kunya ma,gwara ke bacci kike abinki,ni fa har fada aka yimin”dariya ta kamata ya ja hancinta yana fadin
”ni kike ma dariya ko,zamu hadu ne,an shiga haqqina ma baki damu ba ko,yau fa ko dumin jikinki banji ba gaba daya dear na”ya fada ya na lalubarta
ganin abinda yake yi ne ya sanya ta cikin shagwaba tace
”dinkina fa zai farke”zaro ido yayi kana yq daga ta don yasan matuqar ya farke din shi da mami Allah ne zai rabasu,kujera ya janyo ya dawo gaban gadon kamar zai shige cikinta hannunta cikin nasa ya dora kansa saman gadon suna fuskantar juna
Sauya salon muryarshi yayi cikin rada rada yace”yanzu ya za’ayi baby,nifa gaskiya mayen abun nan ne,yanzu ma a kame nake”ya qarashe maganar yana wani kashe mata ido,sai ta bata rai cike da tsoro
”dole ki zama jaruma baby,idan kuma kinsan ba zaki iya ba ki gayan tun wuri na fara neman aure”ya fada cikin salon jan fada,ai kam sai ta fasge masa da kukan shawagwaba,shi kuma ya lalace gurin rarrashi daganan ya samu ya rage zafi abinsa,bata hanashi wannan ba kam,saboda ta fuskanci cikin sahun da yake a amzaje,idan ta hanashin ba shakka ta shiga haqqinsa sosai tunda jinya takeyi ba zata iya masa abinda ya wuce hakan ba
Allah ya rufa asiri yana shiga bayi baaba uwani ta shigo,nan ta zauna tana yiwa maryam sannu da jiki,cike da kunya take amsa mata,lokacin da ya fito sannu da zuwa kawai ya yiwa baaba uwanin ya fice bayan ya jefi sahibar tasa da wani kallo mai cike da qauna da bege,baifi minti goma da fitar tasa ba siga wata nurse ta shigo,tace baaba uwani ta taso a nuna mata dakinta inda zata kwana,nan din akwai mai kwana da madam maryam din,bata musa ba ta bita don ba sanin tsarin asibitin tayi ba batasan duk plan din abdallah bane,sai data fice kana ya dawo dakin harda maida key kana ya shigo ya fidda kayan jikinsa ya bar singlet da three quater ya qarasa gaban plasma din dake jkkin bangovya dauki remote na reciever din,kansa tsaye ya dale gadon da maryam din ke kai a kwance bayan ya bata magungunanta ta sha,jikinsa ya janyota ya rungumeta tsam bayan ya sauya musu tasha zuwa mbc bollywood cikin sa’a suna film din geet,lumshe idonta tayi ta sake narkewa cikin jikinsa,don tana bala’in son film din,hakan ya qara mata shauqi ya kuma hanata cewa abdallah komai tana jinsa yana ta rage zafinsa a zafafe kamar zai hadiyeta,saidai data fuskanci zai sauya akala zata dakatar da shi,shikam ko hakan ma ya masa,ya fi masa ace baya kusa da ita
????????????????????????
qarfe goma mami ta iso ta sallamesu bayan ta sake dubawa ta tabbatar da komai normal,gargadi kam abdallah yasha shi,har ya kasa daurewa ya dafe kansa qasa qasa ”abdallah ka shiga uku,Allah ne kadai gatanka”
”baka shiga uku ba sai ka sake ganganci na dauketa gaba daya lokacin zaka tabbatar ka shiga tara ma ba uku ba”bai zaton zata ji ba din haka ya fece ya bar musu dakin
Da wannan dama abdallah yayi amfani ya shirya tafiye tafiyensa don gyara duk wata harka ta kasuwancinsa da ta samu baraka kamar kamfanoninsa da sauransu,wadda su nene da ahalinta suka so yin tsallen badake a kanta,kwana goma ya tsara zaiyi,din baijin zai iya zama guri guda da maryam bai tsallake sharadin mami ba,ya tabbata kafin dawowarsa aidai ra warke,idaan yaso yaci duniyarsa da tsinke son ranshi,don da baaba uwani ra hadosu saboda ta kula da maryam din ta warke sarai kamar wata me jego inji abdallah
Ana jibi zai tafi yayi niyyar gaya mata,ita ke kawo masa abinci har sashensa,kamar ko wanne lokaci taci kwalliyarta tsaf cikin atamfa fitted gown,babu wata sura tata da bata bayyana ba,qamshin ta kawai ya isa ya daga maka hankali,yana cin abincin ne kawai amma duka hankalinsa na gareta,daga qarshe ma fita yayi daga kansa abinci ya tureshi ya miqa mata hannu,take ta taso cikin taku na daukar hankali ta qaraso gareshi,kan cinyarsa yayi mata masauki kana ya mannata da jikinsa ya saba aikin nasa na rage zafi,luf tayi tana karbar saqonnin da duk yake aika mata,cikin salo na jan magana yace
”ke kanki kina karbar saqonni na,amma yanzu da zance zamu fara lacture saikiyi tawaye”
aikam tuni ta zaro ido don har yanzu bata manta wuyar baya ba,narkewa tayi ta marairaice masa,cikin wata shishshiqa ta kissa tace masa
”amma ka sani fa my ban warke ba”
”i know,shi yasa nace gwara na danyi nesa duk da zuciya bafa so”sai tayi hanzarin juyowa ta dubeshi
”kayi nesa kuma,kamar yaya?”
girarsa ya dage mata ya kashe mata ido daya
”zanyi tafiya inje in gyara kamfanoni na da aka so durqusarwa,kwana goma in sha Allahu na kammala,kafin na dawo nasan kin warke kinga sai shiga aji da daukar lacture ko?”