ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk da ya bata kunya amma sai da ta sa masa kukan shagwaba”amma daga yin sati daya sai kace zakayi tafiya?kasan bazan juri rashin ganinka ba har kwana gona?…..nidai gaskiya…..gaskiya…..”ido ya lumshe shagwabarta na sake rudashi ne sosai
”nima haka my dear na,nasan halina,indai naci gaba da zama din bazan iya jurewa ba,idan kuma kin amince muci gaba da darasi to”sai kuma tayi luf bayan ta noqe kafada,dariya yasa mata yana fadin
”you see”
hannunta ya kama ya dora a qirjinsa daidai zuciyarsa yace
”kada diya na ta ta damu,kin manta zuciyarmu guda daya ce,nisan dake tsakaninmu ne kadai zai raba mu amma muna tare ne,koda mutuwa dayan yayi to muna tare,after all ma gwara nayi tafiyan tun yanzu,saboda idan aka wuce yanzu gaskiya bazan iya yinta ba,kinsan ni ba ragon malami bane,dali barce dai na samu raguwa”kai abdallah na kasheta da salonsa,sai ta kasa ce masa komai,ranar bara baro bangaren ba sai kusan sha daya

????????????????????????

Washegari sai ganin lubabatu tayi yasa andauko mata ita,tayi murna kam qwarai duk da cike take da kewar tafiyar tasa,mami ma da ya gaya mata cewa tayi idan maryam ta yarje masa yaje shikenan,don ta riga da ta sani tafiyar tasa ce kawai zata sa yabar mata maryam din ta warke yadda ya kamata

Kuka take sosai sai taji zuciyarta tayi matuqar quntata batason tafiyar tashi,bata taba sanin rabuwa da masoyi haka yake da daci ba sai yai,ashe haka matan da mazansu ke tafiye tafiye suje ji,tun hisham na matsa masa horn har ya gaji ya daina don ya bararraje a gabanta yanata faman aikin lallashi,so yaje yaga ba hawaye ko daya cikin idanunta amma hakan ya gagara,daga qarshe ya dubeta cikin karaya
”anya dear na ba haqura zanyi da tafiyar nan ba”da sauri ta girgiza kai
”nikam gwara kaje,sai gaba kuma mun sake watanni kace zaka je?,tab,aikam,nazan yarda ba”dariya taso bashi,sai ya hade hannayensu
”is ok,indai kina son na tafi to ki share hawayen kinji”da kai ta amsa masa ta fara sharewar yana tayata,sai da yaga fuskar tata tayi fes sanann ya ciro mata hijabi ya saka mata,ya kama hannunta suka sauko,ya dubi fuskarta yadda tasha kuka sai yayi sha’awar tsokanarata
”ashe maryama ta abdallah ce,ashe maryama na mutuwar son abdallah,ashe rabuwa da masoyi da daci”yayi maganar cikin salo na waqa,sai ta fara diddira qafafunta cikin shagwaba,baya yadan ja kana ya kama baki
”iyeeee,naga fa alamar yammata kin warke,irin wannan tsalle haka,kodai na fasa tafiyar nan na zauna aci gaba da daukan darasi mu tsinki fure sosai”ba qaramar dariya ya bata ba,abdallah badai iya tsoka na ba idan yaso,sai ta fada jikinsa cikin dariya,shima baiyi qasa a gwiwa ba ya tarbeta ya rungume abarsa tsam yana jin duminta da qamshin azababben turarenta,sai da ya gama bata hot kisses sannan suka fito

Tana kan kafadarsa daya kafadar tata rataye da briefcase dinshi haka suka jero har harabar gidan,bai damu da securities dinshi ko hisham dake tsaye agun ba ya sake qwaqume abarshi,duk da kunyar da take ji amma ya hanata motsawa a haka har suka isa motar da zasu tafi din,ko kallo hisham dake waje a tsaye shida lubabatu yana zabga masa harara bai isheshi ba,sake janyita yayi ta mata kiss a kumatu da goshinta,yasa dan yatsansa yana dauke mata hawayen da ya fara silalo mata
”no baby,no,hawayenki karyamin duk wani qwarin gwiwa yake,ki bar kukan nan haka,bari na gaya miki abunda zaki min qwaya dayq da zaisa na kuma gamsuwa lallai kina sona kuma kinyi kewata bayan tafiyata”bakinsa ya sanya a kunnenta cikin kashe murya da iya salon sace zuciya da tada tsohon miki yace
”kimin wani kyakkyawan tanadi yadda zamu bargaje amarcinmu sosai bayan dawowata,idan so samu ne ma mami taga alama,ki mata guzurin jika”wayyo kunya kashe maryam,sai ta maida kanta kafadarsa tana dariya qasa qasa
”zan baka mamaki kuwa,kasha kuruminka”itama ta maida masa cikin nata salon
‘ido ya dan zaro yana murmushi
”Allah tawan,kai wlh ke ta musamman ce dear na”dariya suka saki tare a hankali

”kaga malam,idan an fasa tafiyar nan ne ka gaya min,don me zaka shanya mutane kuzo ku bude wa mutane filin soyayya”kunu abdallah ya dan sha
”kaga malam,ya zaka shiga haqqin masoya,miji da mata fa sai Allah,musamman ma ni da maryam kafi kowa sanin cewa mu na musamman ne,don haka ka shafa mana lafiya tsohon gauro kawai”dariya hisham ya fashe da ita
”dududu yaushe Allah ya ‘yantaka,naga tare muke fama da gaurancinmu,har gwara ni na fika qarfin zuciya ma…..”
”ko yanzu Allah ya ‘yantani dai na fika”yayi sautin katseshi don kada ya masa tonon silili yana yafito lubabatu dake can gefe tana kallonsu tana murmushi
”amana zan danqa miki,ki kularmin davrayuwata,idan har kika bata kulawa yadda ya dace ni kadai nasan tukuicin da zan miki,zan baki wannan tsohon gauron ki taimaki rayuwarshi”dukkansu sai da abdallahn ya basu dariya,itakam lubabatu hannu tasa ta rufe fuskarta

Wani dogon hot kiss ya bata wanda sai da yasa hisham da lubabatu dauke kan don kunya kana ya kama hannunta yana fadin
”ki kula min da kanki,zanyi kewarki fiye da kike tsammni ko hasashe,kana ki cikamin alqawari na idan na dawo”kai take daga masa kafin daga bisani itama ta juya tafin hannunshi ta sumbata,ita da lubabatun na tsaye har motocin suka kammala ficewa daga gidan security ya maida get din ya rufe.

. By

mrs muhammad ce???? BH

????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

    ▶6⃣6⃣

An karbo daga abu hurairah,R.A yace: Manzan Allah S A W yace:((MUSULMI DAN UWAN MUSULMI NE,KADA YA HA’INCESHI,KADA YA MASA QARYA,KADA YA TABAR DA SHI,KADA YA WULAQANTASHI,KADA YA ZALUNCESHI,KADA YA TOZARTASHI,KOWANNE MUSULMI A KAN DAN UWANSA HARAMUN NE(YA TABA)MUTUNCINSA,DA DUKIYARSA,DA JININSA,TSORON ALLAH ANAN YAKE,(SAI ANNABIN RAHAMA YAYI NUNI DA QIRJINSA SAU UKU)YA ISHI MUTUM SHARRI YA WULAQANTA DAN UWANSA MUSULMI

Allah ka tsaremu,Allah ka tsaremu,Allah ka tsaremu ????????

qarin haske

ANTY SIS ta janyo hankali na game da wani abu cikin page din baya,wato da yawa makaranta sun dauka ina nufin sixs hours abdallah yayi a first night dinsu,ba haka nake nufi ba,ina nufin after sixs hours ya fahimci barnar da yayi,abinda nake nufi kenan,don bazaiyiwu mutum yayi sixs hours din yana abu daya ba kamar yadda anty sis kika ce,hakan yake,GODIYA NAKE

Tana zaune saman yagalalliyar daddumarta bayan ta gama karanta fatiharta da suka yi alqawarin karantawa malam na hayi duk salla ita da habiba,shiru tayi tana nazarin rayuwa,wato duk lokacin da Allah ya maka baiwa kaqi gani to idan ya tashi baka zato ba bakayi aune ba zai rabaka da ita rabuwa ta har abada,ba duka mutum bane yake wasa da damarsa ba karon farko bayan Allah qwace ya sake dawo masa da ita

bankado jibgegen labulen ta,da akayi ne ya sata dagowa da sauri,habiba ce tsaye tana haki tana fadin
”taso zahariyya,taso,ina zaton yau Allah ya karbi addu’armu ne,zoki ga malam”ko nauyin jikinta bata ji haka tayi wuf ta miqe suka fice a sukwane,kai tsaye dakin nan nasa mai azabar kyau da shi kadai ke shiga suka kutsa,kusan dukka mata da yaran na tsaye ne daga waje suna leqensa,gaba daya an sauya masa kammanni ya koma wani abun tsoro,kwananshi dama bakwai baida lafiya a cikin dakin,sai wani fisge fisge yake da surutai marasa kan gado da ma’ana,jini ne kawai ke fita daga bakinsa,duk shimfidar dakin ya tuttujeta saboda azabar da yake dandana,ya kusa aqalla awa guda cikin wannan halin babu wanda yayi yunqurin taimaka masa don gaba daya sun kasa motsawa kamar wadanda aka kafe a gun,abu na qarshe da yayi shine wata gigitacciyar qara da qwala wadda dukka gonakin dake maqotaka da su saida suka amsa kana kuma jikinsa ya saki baki daya bisa dukkan alamu ya wuce gidan gaskiya(haka mala’iku ke tsiga suke fisgar ran fasiqi kafiri wanda ta bijirewa umarnin Allah,haka Allah ya gaya mana cikin qur’aninsa,sabanin mumini mai biyayya wa Allah da manzansa mala’iku kan cire ransa ne cikin nishadi da tausasawa suna zara suna barinsa yana hutawa har su kammala cirewa,Allah ka sanya mu cikin muminan bayinka),mutuwa abace maisa kashe jiki da zuciya hakan ne yasa kowanne cikinsu jikinsa yayi matuqar yin sanyi suka hau kallon kallo sannan suka fara komawa tsakar gida suna shawara ya za’ayi da gawar tunda tuni suka amince cewa ya riga da ya mutu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button