ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Rikice mata yayi kamar wancan karon sai hakan ya tsoratata,shima kuma ahankali sai ya dinga qoqarin daidaita nutsuwarshi ganin ta fara tsorata,cikin salo da qwarewa na namijin da yasan abinda yakeyi ya dinga tafi da ita,tamkar wani corse yayi a tafiyan tashi,saidai ba wani corse tsabar iya soyayya ne da tattalin mace,wata duniya ya jefasu wadda basu taba koda tunanin akwaita ba,soyayya ta gani zallah madararta daga gun abdallahn nata,soyayya ya gwada mata mai sanyi da tsayawa a rai,duk wahalar da take zaton shanta sai abun yazo mata da sauqi,duk da ba laifi ta dan jigata amma bai yi wani yawa ba
Tunda suka fito daga toilet yake zaune daure da towel,duk inda tabi idanuwansa na kanta,shi kadai yasan me yake ji game da ita cikin zuciyarsa,gaba daya ya hanata sakewa da mayen kallonshi,ga kunyarsa dake nuqurqusata,maganganun da ya dinga gaya mata kawai dazun idan ta tuna sai ta rasa inda zata saka kanta saboda kunya,sarai tasan ita yake kallo amma taqi kallonshi,sai da ta gama sharce gashinta ta saka hand drayer ta busar kana ta zo zata giftashi don ta dauki ribbom dinta dake kan gadon ta daure gashinta,baki daya ya janyota ta fada jikinsa ya dorata saman cinyarsa,cikin kunnenra yake rada mata
”baby Allah yayi miki albarka,banu shakka kin cika alqawarin,ki shayar da ni mamaki,ke din yar aljanna ce Allah baby kamar yadda kike yar baiwa”boye kanta ta dinga yi cikin gashin qirjinsa,yasa hannu ya sake maida mata gashin kanta baya
”amma baby yauma kamar nayi hurting dinki ko?”ya tambayeta a tausashe cikin tausayawa,kai ta gaya masa
”kadan ne ba yawa,kuma ba damuwa a haka ake daina jin zafin baki daya,zan dinga shiga ruwan dumi ne kawai”kissing nata yayi a goshi kana yace
”Allah ya miki albarka,ya bamu zuriyya ta gari,qarasa shiryawa ki rakani naga mami na,bazan iya kwana ban ganta ba”murna ta kamata sosai don itama tayi missing nata,duk da kunya na taba can qasan ranta
Har ta miqe ya kuma riqo hannunta
”baby kin kashe jiki da yawa,ko zaki iya taimakin na shirya?”girarta daya t dage masa kana ta kashe ido
”why not my”
kai ya girgiza fuskqrsa qunshe da murmushi
”lallai a shirye kike baby,get ready for d second round idan muka dawo,irin wannan kashe ido haka”hannu tasa ta rufe tafin fuskarta kana ta janyo wani dan towel din ta fara tsane masa jiki da shi,sai da ta gama shiryashi tsaf kana shima ya shiryata cikin wata doguwar riga mai hade da hijabi
Dadi gun mami kamar ta goyesu haka ta dinga ji,cooler uku ta yiwa mamin na duk abinda ta dafa wa abdallan,kusan awa daya suna hirarau tare daga baya ta tasgi don basu guri su gana su biyu,don tsakanin da da uwa akwai sirri(qalubalenmu mata,sai kuje gaida uwar miji keda mai gida ki musu qifi qifi a tsakiya idan kika san uwar miji mai kawaici wadda ba zata iya ce miki ki matsa ki basu guri su gana ba,ke kuma ba hankali,na minti goma ba zaki iya matsawa ki basu guri ba,ta yiwuwu akwai maganar da alokacin takeso suyi da danta,don Allah mata mu gyara,koke ya yiwa haka keda mahaifiyarki ai bazakiji dadi ba)
mamin ce ta tambayeta ina zuwa
”zanje mu gaisa da mero ne”
”to…to,bata kuwa dade da barin nan din ba,sai da na korata ma tukun”tana murmushi ta sulale ta fice
Fes ta taras da meron da bangarenta,bisa dukkan alamu training na mami ne,tayi kyau da ita ta fara gogewa,haka nan fatarta ta qara kyau,kallo ta tarar da su sunayi ita da labaran din,suka gaisa sai ya miqe ya fice ya basu guri,murna mero ta dinga yi sosai ta dauko wannan ta kawowa maryam,ta rakito wancan ta bata har sai data ce ya isa,sun dan jima suna hira tana sake wayar mata da kai kan wasu abubuwan da tasan ta fita waye wa akansu,sai da ta kusa awa guda sannan labaran ya shigo yace mai gida na magana zasu wuce,kamar kada ta tafi haka mero taji tace amma zata zo itama taga gidan takwaranta,dariya tayi tace shikenan sai tazo din
A waiting parlour ta taddasu tsaye da mami,sai data rakasu har bakin mota,abdallah ya dubi mamin
”badai wata matsala ko mami zamanku da su labaran”murmushi tayi
”wallahi ko kadan,basu da matsala kam,ina jin dadin zama da alhamdulillahi”ya gyada kansa yace
”masha Allahu,mami sai da safe,muna ta missing dinki mami”murmushi tayi
”gwara ai kusan gurma ya kamaku da haka zaku saba ai”ta dube maryam da kanta ke qasa tace
”diyata ku gaida gida tinda qarfi da yaji sai kinyi surukuta da ni bayan nace ni bana surukutar,ki kula da kanki,kaima ka kulamin da ita,Allah yayi muku albarka”ameen suka amsa baki daya
Sai daya tsaya da ita a hanya ya mata siyayyar kayan maqulashe,qememe yace tayi zamanta a motar basai ta fito ba
”zan iya hadiyar zuciya fa idan kika fito wani ya kalleki,ke Allah zan iya mutuwa maryam a kanki,kishi ne da ni sosai,qaunarki ce tamin yawa,ba qaramin kamu ta yimin ba fa”dariya ta qyalqyale da ita”anya my kishin nan naka bai yawa ba”
ido ya zaro
”waya gaya miki?,bakisan yadda sahabbai keda kishi bane?,duk kishin nan nawa baikai nasu ba,kuma ma ai dole na kasance mai kishi saboda annabi muhammad S,A,W,yace maras kishin iyalinsa (addayyus)bazai shiga aljanna ba”kai ta gyada ta saka tafin hannunta a nasa tace
”gaskiya ne,sadaqa rasulul kareem,zan taya ka kaucewa duk wani abun da zai sanya kishinka motsawa RUHINA”
”na gode RAYUWATA”ya bata amsa cike da shauqinta
Sai kusan sha daya da rabi na dare suka koma gidan,da wani kasalallen tuqi ya dinga yi suka dinga hirar soyayya abinsu cikin motar kafin sukai gida
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶6⃣7⃣
Daga abu zarril ghifari R.A yace:Manzan Allah S A W yace da ni:((ka ka wulaqanta wani abu daga cikin kyakkyawan aiki komai qanqantarsa,koda haduwa da dan uwanka ka sakar masa fuska ne(kayi masa murmushi)
Daga barraa,dan Aaazib R.A yace:Manzan Allah S A W yace:((babu musulmai biyu da zasu hadu suyi MUSABAHA face sai Allah ya gafarta musu zunubansu kafin su rabu))
Gida ne suka taru suka ginashin mai cike da ni’ima qauna soyayya da kwanciyar hankali,wanda tsabar kula da haqqin juna wanda Allah ya dorawa kowannensu shine sila,kowa na qoqarin sauke haqqin dan uwanshi a kansa ua kuma qara da kyautatawa jin qai qauna da rahama irin wadda Allah ke sanyata tsakanin ma’aurata,kamar yadda abdallah ya sake tabbatarwa kanshi yahi dace da macen qwarai wadda har ABADAN bazai iya rabuwa da ita ba haka itama maryam anata bangaren,tabbas babu shakka abdallah kyautar Allah ne,hikimar ubangiji mai yawace,wato alkhairi ke tafe da ita,jinkirin auren da ya mata ashe shi kadai yasan manufarsa ta yin hakan,ba shakka shine sarki gagara misali,komai da yayi kan bawansa akwai manufarsa a ciki,saidai kai ajizanci da son zuciya irin taka ya hanaka gani
BAYAN WATA SHIDDA
Haka rayuwa taci gaba da jujjuya musu cikin hikima ta ubangiji,rayuwa ce suke yinta mai cike farinciki da qaruwar arziqi,tsantsar qauna da fahimtar juna a tsakaninsu,hakanan ci gaba kala kala suna ganinshi,albarkacin tsaftatacciyar zuciya taimako da qaunar jama’a da suke da ahi wanda raino ne irin na MAMI kusan a gurinta suka nashi wanann aqidar