ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Tuni abdallah yayi gini gini mai kyau da tsari mai dauke da part biyu,cikin tsarinsa da halinsa maryam sam batasan ginon waye,ba sai bayan da ya kammala taji ana gayyatarta tariya,gida ne da ya mallakawa mahaifin maryam wato malam ahmadu wanda aka fara kira da alhj amadu dalilin kaishi umara da yayi shida mama,godiya tazo ta masa ya rufe bakinta da zafafan kises yace bai buqatar kowacce godiya daga bakinta,shi a rayuwa sun gama masa komai mama da baaba da suka haifa masa ita
Maama da baaba huwaila ne kawai suka tare a ciki don a taohon gidan aka bar inna hadiza da jamila da bintu,don tuni malam amadu ya tsawatar wa dukka wacce take jin zata ci gaba da wasa da aurenta tana jeka ka dawo,matuqar kuwa ta kashe auren nata to saidai ta nemi gidan zama ba gidansa ba,yabi kowacce da jari daidai qarfinsa,suntsota kuwa don bai taba musu bore irin wanan ba don haka kowacce tayi luf a gidanta,abun dama akwai raahin kwaba da hantara tunda sunsan idan sun dawo din ana maraba da su,musamman yaran inna huwaila wanda itama bayan babansu yayi nashi jan kunnen itama ta dora da nata
Hisham kuwa da lubabatu tuni zance yayi nisa,don tuni ma har manya sun shiga maganar an kai kudin aurensu,hakan,na qaramin dadi ya yiwa baaba huwaila ba,girma da qimar maryam da mama suka dadu cikin idanunta,babu shakka sanin masoyi sai Allah,wanda ka tsana kake ganin bai sonka wani lokaco baka gane cewa ashe masoyinka ne sai tafiya tayi tafiya
????????????????????????
kamar kowanne lokaci kafin dawowar abdallahn da awa daya ta kammala komai,haka ma yauma take ga maryam,bayan ta kammala ayyukanta ta fada wanka,lokaci ta bata mai uawa gaban madubi tana tsara kwalliya kana ta fidda wata iriyar riga mai bazar,tafe take da breast,cup daga sama hakanan hannun shimi gareta,bayan rigar kusan rabinsa a wawake yake,dududu rigar iya karta gwiwa,kusan kullum shigar maryam kenan don qa’idar abdallah ce,bata sanya manya kaya sai idan zasuyi baqi koda rana idan baya nan,amma ko dawowar rana yayi tofa sai anmasa kwalliya da shigarsa ya gani kana zai koma,saidai ko idan zasu fita unguwa,wannan kam harda hijabinta don baya taba barinta ta fita da mayafi koda wasa
Alarm da taji shi ya tabbatar mata ya dawo,ta sake duban kanta ta tabbatar komai yayi daidao,ita kanta tayaba irin kyawun da tayi,ta rasa me yasa take dada wani kyau tare da cika,har wani kumatu ta fara yi,tayi azamar sake fesa turare da gaggawa ta fito,saidai tana zuwa bakin qofar falon ta sauya taku
Zaune yake cikin motaf kamar kowanne lokaci shi daya ne,dama idan taji alarm din ta san cewa security dinsa sun tafi saura shi kadai sai ta fito,a bayan motar yake a zaune da alamu yauma driver ne ya tuqashi,sometimes idan suka taho da securityn nashi yakan karbi driving dinne ya ja suna zaune,wannan na daya daga cikin abinda ke sake burge maryam game da abdallah
Tunda ta taho din ya zuba mata idanu ko qiftawa bayayi,a kullum kwanan duniya sake linka masa qaunarta ake cikin zuciyarshi,har ta qaraso bai sani ba sai data sa bakinta ta hure masa ido,ya saki murmushi ya jawota ta fado cikin motar ya rungumeta
”hala yauma a gajiye kake shariki hayateeygaskiya idan basuyi wasa ba kwanan nan zan hana wa kowa ganinka,akan me za’adinga wahalmin da zuciyata”ta fada a shagwabe
ajiyar zuciya ya saki yana murmushi
”sosai kuwa baby,amma wai…baby ina da tambaya?”yayi maganar yana bin loko da saqo na jikinta yana shanshanawa saboda irin qamshinta dake gigita shi
”uhmmm,shariky ina jinka”tayi maganar itama tana sake qwaqumeshi
”wai don Allah ya zanyi na ragewa kaina sonki cikin zuciyata ne,yana neman fa ya hallakani”dariya ta qyalqyale da ita tana sake nadewa cikin jikinsa”saidai a qara maka wani son kan wanda kake min my”ido ya dan zaro,cikin wasa yace
”baby…..idan naci gaba da yi miki irin wanann son ai sai ki hanani qara aure”sai ta hade rai ta zame jikinta daga nashi ckkin fushi ta fara qlqarin fitowa a motar,riqeta yayi yana dariyq ciki ciki don yasan ya gama tabota
”ki jirani mana baby mu tafi tare”·
”ka bari ifan ka sake auren sai ta jiraka,tunda ni nayi maka kadan”ta zame da squri ta fice,shima da sauri ya fito yana dariya qasa qasa yadda ba zata ji shi ba,sai ya jingina da motar yana qare mata kallo yadda take tafiya da sauri sauri,abun sai ya burgeshi,’yar figigiyar rigarta ta mata kyau,hakanan yaga ta sake wani cika duk wani hips nata ya fito,sai da ta qaraci saurinta cikin takun da basu gaza biyar ba ya damqota,cak ya dagata tana eutsil wutsil dq qafa tana tureshi ya shige da ita
ya sani a bisa al’adarta kafin ya dawo ta hada masa ruwan wanka don haka ya wuce da ita kanshi tsaye toilet din,tuni ido ya soma raina fata don ta gano qarshen zancan,yau kam kwalliyarta saidai ta sake wata,da sauri tace da shi
”nifa na gane wasa kake min,pls bawan Allah ka saukeni,zan tayaka ma wankan”dariya ta bashi ya dubeta
”ai kin riga kin makara,kin manta ne babu fushi a zamanmu,you break the rule,and the rule will break you as usual”yana gama fada ya sanyata tsundum cikin bathtube kana ya fidda takalmin qafarsa da safa ya cire suit din jikinsa ya bita ciki,sai da suka gama shan qaunarsu kafin suyi wankan su fito
Yana baje saman carfet din falon maryam tana hidimar zuba masa abinci don a qasa yake cin abinci abinsa yace yaa samu ladan sunna na irin zaman da ma’aiki yakeyi idan zaici abinci(irin zaman yana taimakawa qwarai wajen hana mutum yin mugun qoshi daya sabawa addini,haka yana hana yin tumbi)bayan sun gama shiryawa sanye yake da gajeran wando shi kadai ne ajikinsa sanyin a.c na ratsashi,ta riga data saba da kallo irin ma abdallah,indai yana kusa to fa dukkan idanunsa na kanta,bata damu ba hasalima jin dadin hakan takeyi don ya sanshi farin sani,ba macen data isa ya tsaya yana kallonta to din me ita din halaliyarsa zata hanashi more kallonta,bayan ya gaya mata ba sau daya ba basau biyu ba kallonta ba qaramin jefashi yake cikin nishadi da sabuwar duniya yake ba
Sai data lakuce masa hanci sannan tace ”mr kallo”
”na amince”ya fada yana murmushi,ta tura masa plate din abincin wanda ta cika da lafiyayyen alkubus da yayi kyau ya taahi yayi shar,da kwanon tangaran mai kyau dauke da miyar taushe wadda tasha tantaqwashi da naman kasuwa da manshanu ita kuma ta jawo wani jug na plastic tare da wani kwanon tangaran da abun zuba sugar ta bude ta fara hada garin kwaki da suger da soyayyar gyada,cak ya tsaya yana dubanta ita kam batasan yana yi ba har wani tsinkewa yawunta yake kamar wadda taga wani abin dadi,sai da ya kira sunanta sannan ta dago kai tana amsawa,ganin yadda fuskarsa tayi kicin kicin ya sanya jikinta yin sanyi,don ko kusa bata qaunar ta zama sanadin bacin ransa
”amma yaya mukayi da ke kwana ukun da suka wuce a jere…..ranar farko kika cemin sha’awarsa kike na barki kika ci kayanki,rana ta biyu kika ce min bakinki ba dadi da kika ci na jiya kinji dadi bana so amma sabida farincikinki na barki,shekaran jiya harda magiyarki da qwallarki na barki kici,jiya kuwa da kika tashi sai kika shaqeshi kika cika cikinki taf da shi kafin ma na dawo,da na dawo saboda tsabar qoshin da kikayi loma daya na abinci kika ci kika fara amai,sanann yauma dai a gain kice min shi zakici?”sai ya girgiza kai
”bazai yiwu ba maryam,sai kace wanda ake ciwon yunwa a gidansa,aiko wani ke neman taimako a guna bazan bashi garin kwaki ba bare iyalina”tuni qwalla ta cika idonta,ga qoshi ga kwanan yunwa,tana son ta kyautatawa abdallah amma wlh idan taci abincin ji take kamar numfaahinta zai dauke,ba bata lokaci hawaye suka fara silmiyo mata,idonshi ya runtse don babu abinda yaqi jinin gani irin hawayenta
”ya salamullahi,daga magana sai kuka?”
”Kinga matsonan muci abincin ko yaya ne,idan muka gama sai ki gayan meye damuwarki,idan ma duka nau’ikan abincin ne baki so ki lissafa irin wadanda kike so kona wacce qasa ne in sha Allahu ni abdallah mai nemo miki ne kinji dear,amma wanann hawayen qona min zuciya yake”ya fada yana daga mata hannu alamum ta taho,ba musu ta matso jikinsa tana goge hawayen kanta a qasa,cike da son ta faranta ransa tasa cokali ta fara ci,loma biyu kadai tayi taji wani abu ya dunqule mata sai amai tun tana yinsa tana fidda abincin da taci,da garin kwakin da tasha dazun har ya koma bata iya harar da komai,gaba daya hankalinshi a tashe yake gani yake shine sila da ya takura ta,haka ya dauketa cak yagyarata ya gyara gurin,bai samu nutsuwa ba sai da yaga bacci yayi awon gaba da ita,duk son da yakewa alkubus din da qyar ya iya cin yanka uku