ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba qaramin tsorata mami tayi ba da ganin zahariyya kwance male male cikin wani mawuyacin hali,batasan lokacin data isa gareta ba tana kiran sunanta saboda tsabar tqusayinta daya kamata,lokaci guda ta manta duk wani abu da sukayi mata ita da uwarta,kafin ta qarasa gabanta abdallah ya shiga tsakaninsu cikin tsananin nacin rai yana girgiza kai,tuni,idonsa ya sauya kala
”kada ki isa gareta mami ki barta don Allag,wannan shine sakamakon abinda ta aikata a rayuwarta,kallo daya zaki mata ki tabbatar cewa sakamako take karba”
tsawa mamin ta daka masa”matsa daga gabana kafin na tsinka maka mari abdallah,baka da hankali ne?,kasan naquda kuwa?,kasan irin azabar da take ji yanzu haka?,ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne”cewar mamin cikin fushi,ba musu ya kauce ya bata gu don baison bacin ran mahaifiyarsa
Ba qyamata ko tsangwama mami ta tattarota jikinta cike da tausayi,suna hada ido da mamin itama ta fara kiran sunanta,fadi take mami ku yafemin keda abdallah,kuyafemin mami mutuwa zanyi,tuni mamin ta bada umarni aka dauko gado don dorata a ahigar da ita tiyatar gaggawa,ana shirin daujarta tace ta saki murmushi tana kallon mamin
”mami,dama qyaleni kukayi kada ku bata lokacinku,don nasan cewa mutuwa zanyi,kuma ina farinciki da hakan,ta yiwuwu Allah ke sona yayi nufin wankeni daga zunubaina da zai dauki raina ta hanyar naquda,mutuwata a yanzu ta fiyemin rayuwata mami”
tuni hawaye ya cika idon mamin,duk da haihuwa daya tayi amma har yau bata mance zafin naquda
”ki daina fadar haka zahariyya,mata nawa ne suka haihu gasunan lafiya da su,ciwo ai baisan inda rai yake ba saidai idan kwana ne ya qare”sai taga idonta na kallon wani guri ne daban,a hankali taji ta ambaci”habiba”
duka sai suka juya,wadda aka ambata da habiban ce ke qarasowa inda take,zubewa tayi a gun tana kiran sunan zahariyya,ba wanda yasan alaqar dake tsakaninsu don haka mami ta sake bada umarni a dauki zahariyya a wuce da ita dakin tiyata,da sauri zahariyya ta tsaidasu
”mami,na fada muku wallahi a yau zan mutu bazan sake kwana ba aduniya,da tiyatar da zq’ayimin gwara ki barni nayi magana da wanann baiwar Allahn”jikinsu gaba daya yayi sanyi don haka mami ta matsawa habiba ta iso tana zubar da qwalla
”zahariyya,naga sakayya ta daidai abinda na aikata a rayuwata,aahe da gaskene son zuciya bacinta?,ashe da gaske idan baka godewa Allah ba zaka godewa azabarsa?,ashe daidai ne da ake cewa idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere wataqila kai zaka iya fadawa?,tabbas Allah ba azzalumin sarki bane kuma baya zalunci saidai bawa ya zalunci kansa……”
mrs muhammad ce
????????????✍????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers
▶6⃣8⃣
Fiyayyen halitta dan gatan Allah Annabi muhammad S A W yace:((idan wanda kuka yarda da addininsa da halayensa/dabi’unsa yazo muku(neman auren ‘ya’yanku)ku aura masa,idan ba haka ba☝????(kuka hanashi),FITINA DA FASADI MAI GIRMA ZAI YADU/WANZU A BAYAN QASA))
Juya kai kawai zahariyya take don ta qagu taji me ya faru da hqbiban duk da azabar da take ji,cikin kuka habiban ta dora
”na koma gaban mama na da baaba na,ba qaramin farinciki mahaifina yayi ba don ga zatonshi sace ni akayi tunda mamana tace masa bata nayi,haka nan itama mama tayi farinciki,tace nayi shiru da bakina kada na sanar da kowa halin da na fada da sanadin shigata wanann rayuwar da nayi,da na murmure zan koma gidan mijina,haka kuwa akayi bayan na soma murmurewa da wata biyu aka mayar da mi gidan enginer abubakar,a lokacin da aka maidani baya nan ya tafi umara,kada kiso kiga farincikin da fatima tayi,sai tausayin kaina ya kamani,naso ma cuceta amma da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai ya kareta daga sharrina ba tare da ita din ma ta sani ba,yarona wallahi fes da shi kamar sauran ‘ya’yanta bashi da wata damuwa,sati na daya da komawa kafin enginer ya dawo na fara wani zazzabi mai zafi,wasa wasa sai tari,ba’a jima ba quraje suka feso min,idanuna suka canza kala,fatima ita ta tambayi engineer ya bata dama ta rakani asibiti”
sai habiba ta tsaya ta fashe da kuka tana tuna irin bala’i da tashin hankalin da ranar tazo mata da shi,da qyar ta saisaita nutsuwarta sannan tace
”abin takaici da baqinciki zahariyya gwajin farko aka gane ina dauke da cuta mai karya garkuwan jiki cutar sida wato HIV”kusan tare suka fashe da kukan wannan karon dom tuni zahariyya tqyi amanna itama da cutar ajikinta,tunda babu shakka habiba ta samo,cutar ta ne daga jikin malam na hayi,to kuwa dole itama ta kamu da ita babu shakka,kuka sukayi sosai kana habiban tace
”hakanan fatima babu yadda zata yi badon taso ba sai don kare lafiyarsu ta sanar da engineer ,bai bari ya dawo ba ma ya aikomin da saki uku qwarara,ban boyewa fatima komai ba kan dalilin fadawata wanan haki,wallahi baiwar Allah kuka ta dinga yi cike da tausayina ,hakanan tamin alqawarin riqe min yarona riqo irin na amana,da kanta ta daukeni ta kaini har gida,bqn boyewa mama komai ba din tana daga cikin wadanda sukaui silar fadawatq wanan mummunar rayuwar,abun mamaki qarara mama ta nuna qyamata atake agun,harda saiya mazauni sabanin wanda take a dazun da nazo gidan
Tun daga ranar na fara ganin tsantsar tsana da qyama daga gurin mama na hatta da qannena ba’a barsu a baya ba,duka babana baisan me ake ciki ba shidai ya san cewa an sakeni kuma ya nemi engineer amma yaqi sam ya sanar masa dalilin da yasa ya sakenin,yanzu nan da kika ganni na taho ne domi amsar magani da yin jinya,saboda kaucewa idon jama’a da maganganunsu yasa na baro yaho garin da babu wanda ya sanni,don nan din ya fiyemin rufin asiri”kuka sosai zahariyya takeyi nadama kam babu kalar wadda batayi ba game da bitewa son zuciya da tayi,yanzu gashi ta kaisu ta barosu,ganin haka ua sanya mami tayi aumarni a dauketa a shiga da ita don yi mata aikin,haka aka dauketa aka turata zuwa dakin
jira na kimanin awa guda sukayi wata nurse ta fito da yaron cikin zanin mamartashi saidai tuni rai yayi halinsa ya mutu sajamakon tun fari uwar bata samu kulawa mai kyau ba lokacin cikinsa da kuma wuyar da yasha lokacin haihuwa,ba qaramin haushi mami taji ba don bata iya shiru ba sai da tayi fada sosai,minti goma tsakani aka turo zahariyya iyama zuwa dakin hutu,da tambayar abinda ta haifa ra farka a bakinta mami ke gaya mata ya rasu,ajiyar zuciya ta saki
”gwara da Allah yasa ya mutu,haqiqa ya samu gata mai kyau da ya mutu din”mami ce ta tsawatar mata
”kada ki kuma fadin hak,kul”mirmushin yaqe tayi tace
”mami don bakisan dan waye ba,ta yaya aka sameshi ba,amma tunda kince haka bazan kuma fada ba,amma mami don Allah ku yafemin,ba shakka mun cika azzalumai,ba muyi muku sakayyar data dace ba,haqiqa samun mutum irinki mami sai an tona,mai saka sharri da alkhairi,mai saka mummuna da mai kyau,ke mutum ce mami,a yanzu nake kwadayin inama ace tun fari kece kika haifeni,na tabbatar da tuni yanzu ina rayuwa ingantacciya ba irin wadda nake kai ba yanzu”
”ya isa duka mun yafe miki,ko Allah muna masa laifi ya yafe mana ballanta na mu ‘yan adam”
”na gode mami,ko yanzu na mutu nasan
”da ikon Allah zan samu wani sassaucin”
”ba na ce miki ki daina maganar mutuwa bane zahariyya”
”na daina mami”ta fada kana taja idanunta ta rufe ruf tana saukar da ajiyar zuciya