ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Manzan Allah S A W yace:((babu abinda yake maida qaddara sai addu’a

LITTAFIN NAN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA DUK WATA BUDURWA DA AURE YA MATA JINKIRI ,DA KUMA DUKKAN WANI MUTUM DAYA TSINCI KANSA KO YA TABA TSINTAR KAN NASA A HALIN SIHIRI,MU SANI CEWA SHI HAQURI WANI ABUNE DA FARKONSA MADA CINE AMMA QARAHENSA ZUMA NE,BABU WANDA YA TABA YIN HAQURI INGANTACCEN HAQURI DAGA QARSHE YA TASHI BABU RIBA,BABU SHI,SAIDAI BA HAQIQANIN HAQURIN KAYI BA

BAYAN SHEKARA GOMA SHA HUDU

Abdallah ne a gaba riqe da hannun matashin yaron dan kimanin shekara goma sha hudu suna magana qasa qasa,shi da yaron dukkansu sanye suke da doguwar riga yar asalin saudiyya,kansu lullube da hirahi da kewayayyen abun nam mai siffar zero,a bayansu kuma mami ce riqe da hannun wasu kyawawan ‘yammata guda biyu wadanda ba zasu wuce shekara biyar biyar ba,kallo daya zaka yiwa yaran ka bawa kanka amsa da cewa ‘yan biyu ne suna tafe suna tsalle tsalle irin na yara,maryam na a gefansu riqe da wani yaron wanda shima irin shigarsu abdallah ce ajikinsa,dukkanau su kuma baqar doguwar riga ce ajikinsu kansu lullube da wadataccen mayafinta

Kana kallonsu ko ba’a fada maka ba kasan cike suke da farinciki,haka yake domin shekaran jiya aka fidda sakamakon gasar karatun qur’ani da akayi ta qasa baki daya wadda aka gabatar a qasar saudiyya,ABDUL_AHAD ABDALLAH ABDULKAREEM da ga MARYAM da ABDALLAH shi ya samu zuwa ta daya,abun ya girgiza qasashe da,dama ya kuma bada mamaki,yaro mai qarancin shekaru kamar wanan ya samu irin wanan baiwar ta haddace qur’ani kana ya zubar da duk sauran abokan takararsa da suka fishi shekaru ya daga tutar ta daya

Wannan abu ba qaramin daukaka ya sake ja musu ba,kai ba abdul_ahad kadai ba,hatta da maryam ta samu qarin soyayya da qauna daga bangaren mami harma da abdallahnta,kyaututtuka kuwa babu kalar wadda abdul_ahad bai samu ba,ko a yanzun ma sun fito ne somin amsa gayyatar da sarkin saudiyya ya musu don cin abincin dare tare da su


Basu suka dawo,ba sai misalin qarfe goma na dare agogon saudiyya,a gajiye suka isa masaukinsu abdallah na sabe da yan biyu da sukayi bacci,abdul_ahad wanda shine babba kuma na riqe da hannun ABDUS SAMAD wanda keta faman gyangyadi,sai da suka isa qofan dakin mami abdul ahad suka ahige shida abdus samad kasancewar dukkansu tare da kakar tasu suke kwana,maryam ta bi bayanau abdallah shima ya bita,kan gado ya sauke yan biyun a hankali,husaina ce ta fara farkawa wadda suke kira da AMATULLAH,tuni ta riqe abdallah da suke kira da ABBU,sarai ya gane me take nufi,so take tace a gunsu zata kwana kamar jiya bayan yau ya riga da yaci burin cin amarci da mamansu
”ya akayi rigimammiya”ya tambaya
”abbu ni a gunka fa zan kwana”
”a’ah ki kwanta anan,baki gani AMATUL JABBAR anan zata kwana?”maqale kafada tayi
”nidai a gunka zan kwana abbu don Allah”duk yadda yaso lallabata ta qiya,maryam na jinau tana sauyawa abdus samad kaya zuwa na barci,dariyarta take a ciki don yasan amatullah ta gama karya masa budget a yau kam,tana lura tun rana da irin kallon da yake jifanta,har tex ya mata ya kama musu hotel tazo suje sharp sharp yanzun zasu dawo amma ta qiya,don duka wunin ranar suna tare da yaran har ma da mamin,anata ude gifts da abdul ahad ya samu

”ummi ki yiwa diyarki magana,tafa matsanta min”ya fada qasa qasa yadda abdul_ahad dake sanya socks a qafarshi yana shirin nacci da mami dake cikin toilet tana dauro alwala duka ba zasu jishi ba
baki ta tabe cikin tsokana tace
”meye nawa?,itaku,ina cewa dazu ka siya mata ice cream ka hanamu kace mamarka ce?”
kai ya dan sosa don kada ta gansu a rana su masu dariya ya sunkuya yana daukarta bisa kafadarsa yace
”haka ne fa,mama na tafi ta kowa ai”ya juya ya fita maryam na qyalqyala musu dariya,ganin yaaran na kallonta saboda dariya da suka ha tanayi da basu san dalilinta ba yasa ta daidaita natsuwarta,ta kammala shirya abdus samad ya haura gadon da abdul ahad ke kai,ta dubi abdul ahad
”idan ka kammala addu’anka ka karanta masa shima kafin ya sake komawa baccin”
”to ummi”

gadon mami ta koma ta sake gyara mata gami da shimfida mata abun sallah don ta riga ta saba bata kwanciya sai tayi sallah raka’a biyu,har ta koyawa maryam din ma,saida mamin ta fito sannan ta shiga itama ta daura alwalar

tana bisa abun sallan mami na zaune gefan gadon tana laranta azkar da bata samu damar yi ba,wayarta na hannun abdul ahad yana danne danne,bata fiye damuwa don ya dauki wayarta ba don ta san hakin yaron indai kaga wayar a hannunshi wani abu mai mihimmanci da zai qareshi yake dubawa,Allah ya zubawa yaron tsantsar basira,hankali da nutsuwa,uwa uba ya samu ingantacciyar tarbiyya ta buga misali,ba qaramar tsaiwa maryam tayi kan tarbiyyan ‘ya’yanta ba musamman abdul_ahad wanda dama danka na faro kusan shine tubalin sauran ‘yan uwansa,irin tarbiyyar daka nashi to sauran ma idan ka haifesu zasu taahi ne kan aninda suka ga na gaba da su nayi wato babban yayansu,saboda ko yaushe suna tare,suna ganin irin abubuwan da yakeyi suma zasuyi qoqarin yin koyi da shi,hakann idan gurbatacciyar tarbiyya ya samu,da sun fara girma zasu bi sahunsa

Ta shafa addu’o’inta kana ta miqe ta ninke abun sallar,mami ta dubeta
”ya kamata kam ki tafi haka ki kwanta maryamu,kullum ace sai kin tayamu hira zaki tafi daki ko kwanta,banda abunki ai bani,kadai ce a dakin ba balle kice kewa zata dameni,ga mai gida na ma baiyi bacci ba”
murmushi maryam din tayi cikin kunyarta din nan da har yau bata canza ba,har yau babu wani abu da ya ragu daga qaunar da mami ke mata sai ninkuwa ma da yayi
”kije ki,kwanta maryam kinji,Allah yayi miki albarka,haqiqa har ABADAN bazan daina alfahari da ke ba,kin cika uwa ta gari mai fidda kyakkyawar yabanya,fata na ubangiji ya cika rayuwarku da haske farinciki da kwanciyar hankali,kin haifa min jikoki maryam hudu ne amma inaji sunfi miliyan,sabida samun yara kamarsu wallahi ba don suna jikokina ba sai an tona,Allah ya miki albarka,Allah ya miki albarka”kanta na aqasa take amsawa da amin zuciyarta cike da farinciki da qaunar mami

Wayar tata dake hannun abdul ahad ta dauki tsuwwa wanda tun tana cikin yin sallah ta ji tanayi,abdul ahad ya dubi umminsa
”ummi,abba ke kira tun dazun”yana saukowa daga gadon ya miqa mata wayar,ta riga da ta horesu,sam basa daga mata kira sai sun kawo mata ko sun sanar mata,ta daga kana ta kanga wayar a kunnenta
”please dear ki taho haka don Allah,i nedd you”murmushi ya subuce mata,kunyar mami tasa ta kana magana sai kawai ta katse kiran,minti biyu tsakani saiga tex dinshi
”gaskiya fa ina alkunya da yawa,na baki minti biyar matuqar baki taho ba da kaina zanzo har,gaban mami na sungumeki,kin sani zan iya ko?”murmushi ta sake saki taci gaba da duba agogo

sai da ta minti biyar din sun cika daidai sanan ta miqe ta yiwa mami sallam,a bakin qofar dakinsu mamin taci karo da shi dauke da amatullah,dariya ta subuce mata
”gaskiya kun samu aikinyi,ta yadda kenan zata kwana cikin ‘yan uwanta”
”me ruwanki da mu?,kedai ki kuka da kanki,yau sai kin biya dukka bashin da kika ci”kai ta girgiza tana murmushi ta wucesu shi kuma ya shiga dakin

Bandaki ta fada kai tsaye bata zauna ba,sai data yi wanka mai kyau kana tazo ta mulke jikinta da turaruka masu dadi wadanda ta siyosu dazu da rana da suka fita yawin miqe qafa,dukkansu na kamfanin alharamain ne masu dadi qamshi,daya daga cikin kayan baccin data siyo ta cira,doguwar riga ce har qasa mai hannun shimi mai azabar yauqi da santsi tana da dan duhun kala kadan ta sanyata,ta feshe kanta da turaren gashi kana ta rage hasken fitilar dakin ta haura gadon ta kwanta,jin shiru bai dawo,ba ya tabbatar mata yana can ana tataburza wata qila da amatullah,kiran da ya ahigo wayarta ne ya katse mata zancan zucin da take yi,lubabatu ce da hanzarinta ta daga don tana sa ran jin daddadan labari saboda sun baro nijeria hindatun nada tsohon cikin haihuwarta ta biyu ita da hisham dinta,ai kuwa abinda ta zata dinne ta sauka dazu qn samu baby girl da take ta sha’awar haifa,don haihuwar fari namiji ne ABDULKAREEM wanda yaci sunan mahaifin abdallah
”adda na haifawa abdul_ahad mata,din gaskiya tun yau na mata miji,ina son absul_ahad adda wallahi dama yaya abdallah zai barmin shi,amma na sani bazai iya ba don ya fimu qulafucinsa”dariya maryam ta saka tana cewa
”Allah ya tabbatar,zanso haka lubabatu,Allah ya raya mana baby”
”adda sunanki taci fa,nayi alqawari dama ina fatan Allah yasa ta dauko halayenki,maryam sunanta saiki zaba mata nickname”ba qaramin farinciki maryam taji ba take tace
”mu dinga kiranta AMEERA ai yayi ko?”
”yayi adda,Allah ya qara girma,kinga mama ce a gurina(maman maryam din)ga maijidda(kulu,da yake haka suka koma ce mata) ta takuramin sai na bata ta tuna kiki tsarabar da tace tana so,kuma wai abdus samad ya cika mata alqawarin da ya daukar mata”dariya ta saki kana tace
”kice mata sunfi kusa,don abdus samad yanzu,haka,ma ya jima da yin bacci amma gobe zan kira na hadasu”,ta karba suka gaisa kana ta hadata da mama ma suka gaisa sannan sukayi sallama

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button