ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Bata kai ga ajjiyewa ba kiran shamsiyya (qanwarta yar inna hadiza)ya shigo,suna gama hira zara ta kira sai bintu kamar hadin baki,dukkansu taya ta murna suke kan zuwa ta daya da abdul_ahad yayi,taji dadi sosai kan yadda kullum Allah ke dada hada kansu suka fuskanci gaskiya suka zamo tsintsiya madaurinki daya,tana cikin addu’ar bacci ne jin shirun na abdallah yayi yawa kiran hindatu ya shigo,tana kaiwa kunnenta abdallah ya shigo dakin yana sakin hannun rigar baccinsa da ada ya nannade,dariya ya bata cikin zuciyarta tana cewa hala dambe akasha kafin amatallah ta yarda
”ke kam baki duba agogo?mufa anan qarfe sha biyu na dare”
”tun dazun nake kiranki naji busy wayar taki”
”eh wallahi muna ta waya da su azara”
”lubabatu ai ta haihu,shegiyar gari,dazu naje gidan na gama yi mata tsiya ai,can na samu su shamsiyyan ma….”maryam din na shirin tambayarta tsiyan me abdallah ya wafece wayar ya kara a kunnensa
”sai da safe,a barmin gimbiya ta ta huta hakanan”ya fada,dariya hindatun tayi tace
”ranka ya dade,girman kujerarka,ai kafi gaban haka ma,Allah ya bamu alkhairi”
”ameen,ki gaida min boss(haka yake kirab jabir idan yaso tsokanarsa) da duka yaran”daga haka ya katse wayar yana jifan maryam din da wani shu’umin kallo
Bayanta ya fada kana ya janyota ya rungumeta tsam a jikinsa dukkansu suna murmushi yace
”idan na barki da wannan hindatun yauma saidai na haqura”
murmushi ta saki a boye cikin son jan tsokana
”yanzun ma haqurin zakayi,tunda jibi zamu koma so nake nayi bacci sosai don gobe wuni nakeso nayi a harami ina da addu’o’i sosai”bai bi ta maganarta ba ya fara aike mata da saqonni sannan yace
”wacce buqata kike da shi haka,tunda kika sameni ai baki da sauran matsalar rat
yuwa”murmushi ta saki kaina ta juyo suka koma fuskantar juna numfasinsu na,haduwa guri guda,fuskanta qunshe da kyakkyawan murmushin daya bayyana fararen haqoranta,kasa daurewa abdallah yayi har sai da ya shafi fuskartata yana fadin
”maryam diyana”wani murmushin ta kuma yi ta kwantar da kanta cikin qirjinsa,don duk lokacin da ya mata irin haka din tssan ta taba zuciyarshi sosai,sai data saki ajiyar zuciya sannan tace
”ba shakka bawan Allah ka gama tare min komai,na tabbatar da cewa na gama samun aljannar duniya tunda Allah ya mallakamin miji kamar kai,ya bani baiwar ‘ya’ya nagartattu,ya bani suruka irin mami,ya bani mahaifiya irin mama,nikam Allah ya gama min komai babu abinda ya rage gareni face inta miqa godiya ta agareshi tare da neman lahira ta kuma”kai ya jinjina yana sake jin qaunarta a ranshi,duk da ni’ima da daular da take ciki hakan bai hanata tsayawa,bautar Allah ba ka’in da na’in,hatta da abdus samad dan shekara goma sha biyu ta koya masa azumin tadawwu’i,su amatul jabbar ne kadai basa yi suma jira take sukai shekara goma goma,mace ta gari kam ya riga da ya gama mallakarta sai godiya ga madaukakin sarki
”dazun bayan fitata kai amatullah mukayi magana da abdur rahim,shikam yace mai binta mai sunan mamana yarinyar inna hadiza ta masa duk duniya so yake du Allah a bashi aurenta,adda ta taimakeshi kada ta hanashi”
”ok….abdur rahim abokin hadin bakinka ko?”dariya ya qyalqyale da ita itama ta tayashi,din duk lokacin da suka tuno da moments din a yanzu nishadi da dariya yake sasu
”kinsan kuwa sanda yana zuwa mini zance idan yazo din yadda kikasan na mutu sabida kishi,zirga zirgar da nake muku fa take hanashi sakewa maza maza yake tafiya,zaki ga yana yawan duba waya nike masa tex nace ya gaggauta tafiya hakanan fa,ke kuma kiyita jin haushi ke a lallai saurayinki abdur rahim baya dadewa yake tafiya,bakisan abdallah bane a rigar abdur rahim”
dariya ta saka ta kama dogon hancinsa tana ja
”bansan so yakan iya farawa da qi da fada ba sai a lokacin,sam bansan sonka ke yawo cikim jinina ba,a lokacim nayi zaton qinka ma nake ashe wani bala’e’en so ne ya dabaibayeni”wani dadi yakeji,har kullum yakanji sanyi na ratsa zuciyarsa idan maryam na fallasa masa sirrin zuciyarta bai gajiya da jin irin son da take masa,ya dan hade fuska kana yace
”amma fa har yau ina sha’awar in qara aure,mata biyu nakeson nayi”kicin kicin tayi ta motsa mata kishinsa da takeyi mai bala’in yawa,bai ankara ba qwalla ya gani na shirim zubowa,babu shiri ya sanya halshensa ya shanye abinsa tas kana yace yana mai girgiza kafadarta yana murmushi
”haba uwar ‘ya’yana,aini tun daga kanki uwaye mata basu sake haifar mace ba,har yau ke kadai nakewa kallon mace a duniya”murmushi ya subuce mata ta boye fuskarta tana cewa
”nikam ban hanaka qara aure ba idan Allah ya riga da ya rubuta cewa qadararka ne,amma ka sani ina tsananin kishinka haka yake cikin jini da halitta ta bazan iya kankarewa ba”
”please mu bar ma wannan maganar kinji dear na”yayi magabar yana sake boyeta cikin faffadan qirjinsa tare da nuna mata zallar soyayya
????????????????????????
Sai kusan sha daya suka fito falon masaukin nasu,tun takwaa suke jiyo,hayaniyar yaran amma abdallah ya duqunquneta ya hanata fitowa,ko breakfast ya hanata fitowa ta hada musu yace kowa yau yaci haquri sai ya gama hutawarshi shima,haka nan ya biye masa suka sha baccinsu kafin su tashi suyi wanka su fito
Duk sun hautsine falon da kayan breakfast abdul ahad nata kai kawon gyarawa,haka yaron yake da qwazo tamkar mace ya iya aiki bakin gwargwado,don sau tari shike kamawa maryam wani abun idan aiki ya hade mata,misali idan zasu tafi makaranta da safe,ya iya hadawa kowa abincin tafiya makaranta cikin lunch boxs dinsa wanda bai wuce chips waina da indomie,hakanan shi zai hadawa kowa ruwan wankansa yaje yayi,wankan ne kawai bata barinsa ya yiwa su amatallah(hakan kuma nada kyau sabida koyawa yara kunya da sanin mutuncin tsiraici tunda akwai bambancin jinsi tsakaninsu shi namiji ne su kuma mata ne),abdus samad ke riqe da gorar ruwa ya hana amatul jabbar sha,sai binsa take suna kewaye falon,da sauri abdul ahad ya cafkoshi ya riqeshi kana ya tsugunna gabansa
”bata tasha abdys samad,bakasan cewa babu kyau ba?,akwai matar data tsare mage ta hanata ruwa da abinci har sai data mutu ta sanadin haka Allah ya sanyata a wuta,hakanan akwai karuwar da ta shayar da kare ruwa ta sanadin haka Allah ya gafarta mata ya sanyata a aljanna,ka sowa dan uwanka abinda kake sowa kanka kaji,ka hana kanka abu ka bawa dan uwanka matuqar ya fika buqata sai Allah ya saka a aljanna”jikin abdus samad yayi sanyi ya miqawa amatul,jabbar ruwan yana cewa kiyi haquri
Ba qaramin burge abdallah da maryam yaron yayi ba,abdallah ya dubi maryam
”kin gani?,rainonki,ne fa uwa ta gari abar alfaharin miji da ‘ya’yanta”sai ta dora kanta bisa kafadarsa tana murmushi kana tace”harda gudunmawar jajirtaccen uba kamar kai”amatul jabbar ce ta fara ganosu da gudu ta qaraso tana abdallah yasa hannu ya dagata sama yana zagayawa da ita,abdul ahad da abdus samad suma suka qaraso suka kai har qasa suna gaidasu kamar yadda suka saba,hannu suka dira saman kansu suna amsawa kamar yadda suka saba sannan suka sumbacesu suka sa musu albarka(manzan Allah s a w yace duk wanda bai sumbatar ‘ya’yansa babu mamaki Allah ya cire rahama tausayi da jin qai daga zuciyarsa,sumbatar ‘ya’yanmu sunna ce mai kyau suna ce ta annabinmu bata yahudawa ba,musamman yara qana na tunda a wannin zamani da al’ummarmu bazaiyu ka sumbaci danka babba ba,fitina tayi yawa cikinmu,saidai fatan samun sauqi)
abdul ahad ke gaya musu mami da amatul lah sun tafi harami,tace sa biyosu a baya,karyawa suma kawai sukayi suka tasa yaran a gaba sai harami don babu nisa can da yawa tsakaninsu hakan yasa a qafa suka tafi