ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????????
kwanansu biyu hudu da dawowa nijeria suna fama da ‘yan taya murna,hakana suka gama yanke shawarar bayan abdul ahad din ya kammala secondry dinshi zasu barshi ya tafi madina ya qarasa karatunsa a can don hukumar qasar ta dauki nauyin karatunsa daga matakin degree har illa masha Allahu
kwana biyar suka gama watstsake gajiyarsu wanda yazo daidai da lokutan da suke warewa don ziyarar yan uwa da dangi,mami kadai aka bari a tamfatsetsen gidan da abdallah ya narka gari guda ya dauko maminsa ya dawo da ita cikinsu wancan ya barwa mero wadda tuni ta koma maryam dinta ko muce maman sayyid wadda a yanzu yaranta uku,bintu ce ta fari takwarar mami suna kiranta walida,sai hamza wato sayyid sanann zainab,mero ta zama babbar mace sosai itama,don mami bata barta da dubun jahilci ba sai data zuba kudade sosai meron tayi karatu ta koma maryam kabiru hamza sak ba mero ba
wasu lokutan da mamin ake tafiyar musamman idan bangaren yan uwan abdallah ne,wannan karon shi ya hana yace ta zauna ta huta hakanan yaushe duka duka suka dawo daga tafiya shikam ba za’a qarasa masa uwa ba,tuni dama ya sanya mamin ta ajjiue duk wani aiki,zaune take kawai aikinta dai research ne kawai kan sabbin cituttuka,tana daga zaune take,bada tata gudunmawar ta hanyar wallafa littattafai da suka shafi bangaren likitanci
kamar kowanne lokaci wannan karon ma sun zafa dangi soasai cikin yan kwanaki inda suka yada zango a gudan lubabatu don ayi bikin sunan takwarar maryam da su,suna kam yayi armashi matuqa,maryam tayi rawar gani sosai wanda komai hassadarka sai ka yaba mata,ta zama uwa yaya kuma matar aboki duka ita kadai,hakanan ta nunawa takwararta gata sabida tulin kayan barka da hidima data dinga yi,da daddare abdallah yazo ya kwashe iyalin nasa sai gida don yace ya gaji da zaman kadaici shi da mami,gidan ya musu shiru babu dadi ko kadan,a sashen mamin yaran suka kwana abinsu dom suma sunyi kewar kakarsu kamar yadda tayi kewarsu,hakan ya bawa abdallah da maryam dinshi damar cin karensu babu babbaka don kullum ganin junansu suke tamkar sabon ango da sabuwar amaryarshi
Tako ina rayuwa ta musu kyau,dukkan wani abun qi Allah ya kawar musu da shi,hakanan ya shiryar musu da zuriyyarsu kan kyakkyawar turba,a yanzu maryam ta zama mudubin gidan baki daya,bama gidan ba hatta family dinsu kowa cikin inuwarta yake,tuni ta aurar da jamila da kulu yanzu a qannen nata baifi mutum hudu ya rage mata ba,kullum cikin sa albarkar iyaye take musamman babansu malam amadu da a yanzu ya samu rufin asiri fiye da zato,girman nan nata wanda ada aka take mata shi a yanzu ya dawo mata,haqiqa duk abinda yayi farko yana da qarshe banda ikon Allah,hatta da isyaku sai da ta maidashi kan kyakkyawar turba darajar addu’a da neman taimakon Allah da sanya Allah ja gaba cikin dukkan lamuranta,don a yanzu haka isyaku da ya koma ishaq ahmad na jami’ar bayero ta kano yana hada degree dinshi fannin kasuwanci wanda maryam din ke saka ran da zarar ya kammala zata dorashi kan wasu sabgogi da shima zai tsaya da qafafunshi,inna wuro ko da tsoho alhaji sunqi fafur zaman maraya don haka abdallah yasa akaje aka rushe gidansu aka tamfatsa musu gini kana aka cika gidan da kayan alatu na more rayuwa,ya ajjiyewa taoho alhaji motocin hawa har biyu baya ga kayan abinci da yake ajjiye muau duk wata da kudin kaahewa,wasu ma kayan saidai su tadda wasu su fitar da su su bayar,don yace bashi da abunda zai saka musu da shi,dukkan gonakin dake bakin rafin malam na dogo ya siyesu ya musu gini na zamani don yace bazai taba mantawa da qauyen ba hakanan bazai iya mantawa da rafin ba a tarihin rayuwarshi,lokaci lokaci idan suka samu wani hutun sukan taho qauyen cikin gidan suyi hutunsu,yaran kansu na son qauyen,wani lokaci idan sunzo abdallah kan tarasu yana basu labarin wasu abubuwa da suka faru tsakaninsa da mamansu a gurin su yita dariya suna tsokanar maryam,tun tana jin kunya har ta saba saidai ayita dariyar tare da ita,musamman idan ya tabo batun yadda tayita kishin meron take kuka aboye da yake sunsa meron momi suke kiranta a yanzu ko mama sayyid wani lokacin ma gurinta suke weekend dinsu suna jin dadin zuwa gidan suyita wasa da su hamza da zainaba
Yanayin zamansu da abdallah kawai koda bai furta mata ba ya tabbatar mata da cewa ABADAN da ita da shi babu rabuwa,wata zazzafar qauna mai tsayawa arai yake gwada mata kamar yau ya fara saninta,ashe samun mijin na garin shine babbar dacewa sa’a gami da farinjinin baki daya bawai gaggawar yin auren ba,tabbas wani hanin ga Allah baiwa ne,hakanan wani jinkirin alkhairi ne
TAMMAT BIHAMDILLAH
????????????????????????????????????????????????
ku saurareni cikin DAURAYAR LITTAFIN ABADAN
tare da ni
safiya huguma
_DA KUMA_
SHARHIN LITTAFIN ABDAN
_DAGA_
QUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION
SUBHANAKALLAHUMMA WA BI HAMDIKA,ASH HADU AN LA’ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA’A TUBU ILAIKA????????????????????????