ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

har waiting parlour haj bintu ta taka mata sannan ta dawo,da murmuahin dai nata ta dubi maryam
”taso,maryam na nuna miki daki,don fita zanyi asibiti ina da C S har mutum uku,Allah ne ma yayi ba zamu samu sabani ba”ta gaya mata lokacin da tayo gaba ta bita abaya,wani labule mai kyawun tsari ta daga daga sashen hagu na falon,saiga gajeran corridor ya bayyana,dakuna uku ne a gun,ta tura daki na uku ya bude tace
”bismillah maryam,ga dakinki,ni,zan fita ki zauna ki huta kafin na dawo mu shirya yadda lamuran zasu kasance,yau dai babu aiki,don Abdallan ma baya gari,amma gobe zai dawo”
”to,mami sai kin dawo”ta fada cikin girmamawa

tabi dakin da kallo bayan mami ta fita,daki ne wadatacce shimfide da carfet mai taushi,sai gado cupboard ta jikin bando da madubi hadi da dressing chair,curtains,dukkaninsu pink da fari,cikin dakin akwai toilet,sai a c daura da window din jikin gado,gefan gadon ta ajjiye kayanta sannan ta shiga toilet din ta dauro alwala ta gabatar da sallar la’asar sannan ta soma jera kayanta cikin sif din

sama sama take jiyo sallama a falon,ta miqe ta maida hijab dinta tayo hanyar falon,budurwar da suka gani ce dazu tsaye tana kalle kalle
”sannu”maryam tace da ita don jawo hankalinta ta fuskanci ta fito
a dage ta kalleta
”ina mami?”
”ta fita aiki”
bata tanka mata ba ta juya ta fice itama maryam ta juya ta koma dakinta

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:51 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

     ▶1⃣2⃣

Har gefin magariba tana gyaran kayanta cikin drower din,dakin tsaf yake don haka bashi buqatar wani sabon gyaran na daban,ta maida qofofin cupboard din ta rufe dai dai lokacin ta jiyo kiran sallah sama sama saboda haka ta shige toilet

har isha’i tana kan abun sallarta,sai da ta bada faralin isha’in sannan ta nannade ta,zaman shirun ya mata yawa,sai kewar gida ta soma damunta,ta jawo wayarta ta lalubu number din hindatu ta kira,ba bata lokaci ta daga
”wayyo ya maryam dita,i missed you wlh wuni guda kawai”
ta gatsine fuska tamkar tana gabanta
”hmmmm,ba wani nan,kinyi missing din nawa kika gaza kira na sai da ni na nemeki”
”ayyah anty na,kinsan dai halin student,wayan,ba credit,am sorry ya maryam”

”shikenan,ya gidan ina mama ta”
”gata kusa da ni bari in bata”
kusan minti goma suna hira har aka fara mata warning kudinta sun kusa qarewa sannan sukayi sallama
toilet ta koma ta hada ruwan dumi tayi wanka ssnnan ta sauya doguwar rigarta mai kauri ta bacci ta dora hijab,tsna maida kayan da suka fadl daga cikin sif din ta jiyo sallaman mami

kan kujerar falon ta taddata a zaune tana cire agogon hannunta
”sannu da dawowa mami”cikin fara’ar nan dai tata tace
”yauwa maryama,ya baqunta,na barki ke daya ko,gurin nawa ba yara ni daya ce,gun haj laura kuma basu sanki ba bare ki shiga,sannan na manta ban nuna miki kitchen ba,ina fata yunwa bata takura ki ba”
murmushin itama tayi
”banjin yunwa ma mami”
”a’ah,ban yarda ba,bari na shirya na fito saiki dafa mana wani abun mai sauqi”
”to mami”
miqewa tayi tana nuna mata jakar da ta shigo da ita
”taimaka ki shigo min da brief case din nan”inji mamin ta haura sama maryam din ta bita a baya tana mamakin sauqin kai irin na mamin,tamkar ita ba wata bace,tsabar sanin qima irin ta dan adam

saman ma wata duniyar ce,komai nashi fari ne tun daga parlour har bedroom din mamin sai dan ratsin baqi kafan wanda bai taka kara ya karya ba
”hmmm,wani aikin sai likitoci”maryam ta fadi a zuciyarta

a falon qasan suka sake zama bayan sun kammala cin abincin daren
”gaskiya maryama my son zai morewa girkinki,haka kija iya abinci”a kunya ce tayi mata murmushi
cikin seriouse tone tace
”maryam kamar yadda na fadi miki dazu inason Abdallah so na haqiqa saboda shi kadai Allah ya mallakamin,cikin irin abinciccikan da Abdallah keso akwai irin namu na gargajiya,sannan yanason kayan snacks,aikinki zai kasance ne ranar weekend zaki dinga breakfast lunch da dinner,amma ragowan kwanakin breakfast ne kawai sai dinner,amma idan ke kina da buqatar ci zaki iya dafawa,saidai majority idan da wuri abdallah zai fita yana tafiya ne da breakfast dinshi

sannan anan zaki dinga shirya masa saman dining dina anan yake karyawa,ina fata nima za’a dinga sammin idan an dafa din”ta qarashe cikin sigar tsokana,dariya ta baiwa maryam
”me zai hana mami,ai sai kince ya isheki ma”
”to godiya nake,amma please maryam ki riqe min amana don Allah,na yarda da muta ne da dama akan Abdallah na amma sun ha’inceni,and pls feel free ke ‘yar gida ce”
taji dadin bayanin mamin sosai har zuciyarta

kadan kadan mamin ke janta da hira bayan ta nuna mata store da kitchen din nasu,tace ta duba idan da abunda take buqata ta fada zuwa gobe da safe a siyo tunda da yamna take tunanin zuwan Abdallan
girgiza kai tayi
”komai yayi mami”
”to masha Allah,sai waj…..”
maganr tata ta katse sakamakon shigowar kira wayarta qirar iphone 7
murmusho maryam taga tayi har haskrn haqorin makkar ta ya bayyana
”dan halak,yaqi ambato”mami ta fada a bayyane tana shirin daga wayar
”salamu alaikum my son yanxu nake zancenka”
”mami na ke da wa?”
”sabuwan mai dafa abinci nayi maka abdallah”
sai da ya danyi jim
”anya mami ba za’a haqura haka ba?”
”kada ka damu son,insha Allahu wannan karon ba za’a samu matsala ba kaji,saboda hankali na ya kwanta da ita fiye da wadancan”
”tunda kin aminta mami shikenan”maryam dake tsaye sai ta danji ba dadi,duk da bata jin abinda yake fadi amma ta fuskanta kamar bai marhabin ne da zuwanta gidan

”insha Allahu ba damuwa,yanzun ma muna tare,muna tsara tarbarka gobe”
ya narkar da murya tamkar qaramun yaro
”ayyah mami na,abinda nakw ta fargabar gaya miki kenan tun dazun,aikin ne mami bai kammalu ba sai nan da kwana uku,kinga ya zama dole na qara kwana hudu kenan,bazai yiwu na taho na barsu ba gudun samun matsala,but….i promise mami na nan da kwana hudu a gida zan kwana kiji mamina,kuma pls kada ki saka damuwa cikin ranki”
ta danji a ranta kam don tana matuqar son Abdallah,amma sai ta share
”shikenan my son,Allah ya kaimu ya kuma kare min kai,ya bada sa’a,ka ci gaba da addu’a don Allah banda wasa”
”insha Allah mami na,i love you”
sai da tayi murmushi sannan tace
”i love you too my son”

daskarewa maryam ta kusa yi a tsaye,tana sake jinjina soyayyar dake tsakanin mami da dan nata
”kinji ma maryam,abdallah ya hutashsheki,sai nan da kwana hudu zai dawo”tace da maryam wadda ke duba,cikin wani dan qaramin oven dake gabanta wanda a badini duniyar tuna ni ta tafi,ta dan washe fuska
”ayyah,Allah ya nuba mana”
”ameen ameen,mujeko sai kiyi kwanciyarki abinki”
tare suka fito falon sai suka tadda ta a zaune saman kujera,budurwar dazu ce
”sannu mami”tace tana dan murmushi hade da kallon maryam da hakanan tun ganin farko taji ta tsone mata ido,ko don kyawun da take hangowa baro baro ne kwance a halittar maryam din oho?
”yauwa sannu zubaida”
”na shigo ai dazu baki nan sai waccar na gani”
mami ta juya tadan kalli maryam
”sunanta maryam….ya akayi zubaida?”
tadan murmusa
”zuwa nayi na amshi key na part din ya abdallah zansa a gyara,naji kamar gobe zai dawo ko?”
” damuwa jeki abunki zubaida zan gyara miahin da kaina,tunda kinga waccan karon yayi fada”
”to zan gyara da kaina mami”
”kada ki damu zubaida,jeki abunki”raahin,kin dadi qarara ya bayyana a,fuskarta,amma sai ta juya zata fice
”am….zubaida”mami tayi kiranta
ta juyo a sanyaye,kana ta amsa
”ku tafi tare da maryam ta gaida nene,ma’aikaciyar da na daukarwa abdallah ce”
dif zubaida tayi a ciki ciki tace ”to”ta juya tqci gaba da tafiyarta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button