ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

momy ta kalli maryam”kije ku gaisheta,abokiyar zama na ce tin kafin rasuwan abban abdallah”
to din itama tace kana tabi bayan zubaida da tuni ta fice daga falon nasu har ta isa filin dake cikin bangaren nasu

Tana biye da ita har suka shiga bangaren nasu,ginishi iri, na mamin ne babu maraba sai bambancin furnitures,mutum biyu ne zaune a falon kallo suke na wani american film a M B C ACTION wanda volume dinsa ya gauraye falon,zubaidaida batayi sallama ba sai maryam wadda siririyar muryarta bata wadatar da su sun jita ba,zubaida ta zauna kusa da matar wadda ta kusa ahekara hamsin da biyar tana fitar da numfashi daga bakinta
matar na juya ta dubeta
”um hmmm,ai nasani iska ce ke wahalar da mai kayan kara,ni nasan ba baki za’ayi ba,amma tunda ke kika g….”
”nene ga mai aiki nan mami tace na kawo miki ki ganta”ta katse babar tata don ta lura basu lura cewa ba ita daya ta shigo ba
lokaci daya suka zuba mata ido nenen da daya budurwar dake zaune kusa da ita har maryam din taji faduwar gaba

nenen ta maida kallonta ga zubaida
”mai aiki,kodai baki ji bane sosai”
cikin yamutsa fuska da alamun qosawa tace
”wadda zata dinga wa ya Abdallah girki da ta canza”
nenen ta dawo da kallonta gun maryam,ta dan tara qarfin gwiwarta tace
”ina yini”second kusan biyar kafin tace
”lafiya,Allah ya taimaka”
”ameen,sai da safenku”maryamun ta fada tana juyawa ta fice a bangare nasu,sai da ta fita sannan ta samu nutsuwa,don ta tabbata rakiyar idanu suka yi mata

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:51 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

     ▶1⃣3⃣

cikin kwanaki ukun da tayi da mami ba qaramin dadin zama da ita taji ba,maca ce mai sauqin kai da iya mu’amala,haba haba da jama’a kowa nata ne,duk lokacin da suka zauna bata da labarin bawa maryam da ya wuce labarin abdallah
halayenshi
me yakeso mene baya so
quruciyarsa da shirmensa
tun maryam na daukar abun qarami har ta maida shi babba,lallai qauna ce mai girma tsakaninsu wanda Allah ne kawai yasan iyakarta

takanyi kuka aduk lokacin da mamin ta gama bata labarin mu’amalarta da Abdallah,tana dadewa kafin tayi bacci
me yasa ita bata ganin irin wannan qaunar musamman daga gurin abbanta?
me tayi masa?
wanne irin laifi tayi masa da yasa take samun rashin kulawa da raahin damuwa da ita daga abbanta?
saidai tana godiya ga Allah saboda uwa ta gari da ya bata mai jajircewa kan lamuranta

duk lokacin da zata fito zata tadda sashen nasu tas,ma’aikatan har sunzo sun gama aikinsu sun tafi,saboda mami gwanar tashi ce da wuei ta saba,sai aka hada biyu don itama maryam din haka saboda yanayin aikinta da tayi a abaya

ita daya take wuni bangaren nasu musamman idan mami ta fita,takanyi mamakin yadda gidan yake shiru kamar babu kowa a gidan,don ita dai tun ranar farko bata qara ganin wani ba,daga ita sai mami idan ta dawo,ta saba gidansu cike yake da jama’a,hayaniya kuwa sai dare ya tsala kake daina jinta,wannan yasa ta kuma maida hankalinta kan wayarta,research kan nai’ikan girke girke ya sake zama abokin ta wanda hakan yake sake bata damar qwarewa da samun experience duk kwanan duniya

????????????????????????

ta fito kenan dauke da kayanta kala biyu sukayi kacibus da mamin hannunta riqe da maqullai
pakistan ne ajikinta riga da wando sai mayafinsa da ta yane kanta,yana daya daga jikin abinda ke boye shekarun mamin

tadan rusuna
”barka da warhaka mami,na zaci kin fita da muka gaisa dazu”
fuskarta a sake kamar kullum tace
”ban fita ba maryam,na tsaya gyaran dakunan Abdallah ne,kada ya dawo ya iaheni da mitar na bayar an gyara masa daki”
murmishi itama tayi
”ina fatan diya ta baki mance gobe ne aikinki zai fara ba”
gyada kai tayi
”ina sane mami”
”yayi kyau,kayan meye a hannunki”
ta kalli kayan sanna ta kalli mamin
”waje,zan dan fita ne na wanke su,bana son in tara kayan datti”

dariya tayi
”to wa yace miki bamu da mai wanki maryam?,ajjiyesu,zan baki num din mai mana wanki ki kirashi yazo ya karba,zan fito da nawa duka ya hada”
”to mami”

da la’asar mak wankin yace mata ya iso yana waiting parlour wato falon su na farko,ta jado kayan duka ta sameshi tsaye,yana amsa ya juya zai fice,kafin yakai ga fitar zubaida da zahariyya ‘yar uwarta suka shigo,dukkaninsu dogayen riguna ne ajikinsu masu santsi,babu mayafin da suka yafa yana saqale ne agwiwar hannunsu sunyi fashion da shi,kwatan kwacin irin shigar da ‘yan matan yanzu keyi espicially gurin dinner din biki(wadda a nasu ganin suke kiranta da iya ado ko wayewa,wanda sam ko kusa,tsabar rashin sanin ciwon kai ne,Allah ya yiki mai tsada amma kin maida kanki mai arha,jikin da sai mutim ya biya sadaki zai gani kin raba shi kyauta kowa yagani,tinda hatta dinkunan da akwyi na fityed gown babu shatin abinda bai bayyana ba,ki sani bakya burge mai ilimi sai jahili,duk wanda yace kina burgeshi da irin wannan shigar to qarya yake,jikinki ne yake burgeshi,aqalla nasan bazai bar qanwarsa tayi irin wanna shigar ba bare ‘yarsa,kin fito sak hadisin da annabi ya siffanta irinsu wadanda yace ba zasu shiga aljanna ba baza su kuma ji qamshinta yace kaasiyatin Aariyatin masu tufafi ne amma tsirara suke,maa’ilaatin mumilaat,karkatattu ne masu kuma karkatar da hankalin maza,sadaqa rasulul kareem)

kuma da yaci moriyar ganga zai yada qoranta,tuni zahariyya wadda me qaras qaras da chewing gum ta bangajeshi,sannan ta kuma juyo cikin gatsali da qasqanci
”dalla can malami,saboda ysabar rainin wayo da rashin mutunci kana gani zaka bangaje mutane?”
”Allah ya baki haquri”yace da ita yana sake kauce mata
”wallahi next time idan ka sake ka sake kwatankwacin haka na ranste sai na maka qasqanci,kuma ka tsaya ka jada a namu wankin,aikin banza kawai,mtseew”taja wani matsiyacin tsaki ta wuce,zubaida ma nata tsakin ta ja tabi bayan ‘yar uwarta ba tare da ko sun dubi maryam ba

suna tsaye sai ga zubaida ta dawo dauke da kayan ta watsa masa
”kuma kada su wuce gobe na gaya maka”tajuya tayi shigewarta ciki
maryam ce ta tayashi tsince kayan tana bashi haquri,don duk gaba daya jikinta yayi sanyi,bata son taga ana wulaqanci wa dan adam
murmushi yayi
”ai babu komai hajiya,idan da sabo ai mun riga mun saba,banda darajar hajiya mami ma da tuni cin abincinmu ya qare agidannann tun bayan rasuwar alhaji”

ita dai bata fasa bashi haqurin ba har ya fice,a tausaye ta bishi da ido,wato a fayuwa idan dai kai talaka ne to baka to da kai da banza duka daya ne?,mutane daidaiku ne suka san waye dan adam wanne matsayi yake da shi cikin halittun ubangiji
”aikin banza”
taji am fada cikin dan daga murya
da sauri ta waiwayo,zubaida ce tsaye,cikin valcony din benansu wanda aka yishi ta cikin waiting parlour din,dauke kanta tayi don tasan sarai da ita take,itakam idan wannan ne itama ba naqonta bane,idan da sabo ai ya zame mata ruwan shata tun tasowarta cikin sararin duniya bata huta da makamancin wadannan dabi’un ba cikin mutanen da take rayuwa da su

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button