ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

tana shirin amsa mata wayarta ta dau ringing
ta kara a kunnenta kai tsaye tace
”ya akayi abdallah”
cikin kwantar da murya yace
”mami yunwa nakeji,wayyo cikina mami”
dariya tayi
”kajimin shi don Allah,yaron goye ne kai,ka soma ci gani nan fitowa na shigo in taho da maryam ne don muci abincin tunda tare muke ci bayan baka”
”wace haka?”
”sabuwar mai girki kuma diyata”
”ayyah mami,ayyah….,nikam nasan kin rage ji da ni,banda haka daga dawowata mami yau inason musha hirarmu mu biyu kuma saiki yo gayya,nidai mami ki taho ke daya abinki kamar yadda muka saba ko inzo in taho dake”
”naji ya isa sarkin qorafi,kada ka shigo mana daki gani nan fitowa”
”thank you my mammy,ki sauri na qagu ki fito”
dariya ma ya bata,abdallah kenan,ko yaushe idan yana gabanta daukan kanshi yake kamar qaramin yaro
sai da ta dan kalli maryam ta gefan ido dake zaune gefan gado kanta a qasa tana fatan bata ji ba,ta riga da taji amma sai ta nuna kanar bata ji din ba saboda bata ji komai a ranta ba don itama batason ta shiga tsakanin wannan uwa da dan masu azabar shaquwa
”kinci abincinki e maryam”
”sai anjima,amma dai na shigo da shi”
”to shikenan ki kwanta ki huta,Allah ya huta gajiya,sai gobe idan Allah ya kaimu”
”to mami”
har ta kusa ficewa maryam din tace
”a cewa ya Abdallah ina masa barka da zuwa”
murmushi mamin ta saki don har cikin ranta taji dadin kulawar da maryam din ta nuna kan tsoka daya a miyanta
”zaiji insha Allah”
ta fice bayan ta ja mata qofar
kayanta ta cire ta sauya na bacci ta ja abincinta ta danci sannan ta kwanta baki daya
Qarfe takwas a kitchen tayi mata,tana cikin hade haden abinda zata tanadar musu na bre fast taji an shigo kitchen da sallama,ta waiwayo tana amsawa,mace ce wadda a qiyasce zata doshi shekaru hamsin,ta qaraso kusa da maryam,a ladabce maryam din ta gaidata,itama ta amsa mata cikin fara’a sannan ta dora da cewa,ni suna na uwani,ma’aikaciyar haj bintu ce,naje hutu na ne da take bani na shekara sai yau na dawo,kin ganni da wuri ko?,qauyen mu ba mai nisa bane shi yasa na fito dacwuri gasji Allah ysa na iso da wuri,ni daga qauyen sumaila nake”
murmushi maryam tayi jin cewa suna da maqwaftaka da qauyukansu
”sannu baaba,ni kuma suna na maryam sabuwar ma’aikaciyar data dauka ce saboda kula da girkin yaronta,ni a cikin gari nake saidai asakin mu yan qauyen gaya ne”
cikin jimami da ‘yar fara’a tace”Allah sarki kice maqota ne mu,kingawadancan ma’aikatan hajiyan maha’inta ne,da su aka hada baki aka zubawa yaron nan guba wallahi,Allah ne yayi da sauran shan ruwansa a gaba,don Allah mero ki riqe amanar hajiya saboda mutuniyar kirki ce”
dariya baba uwani ta bata jin ta ambaceta da mero
”insha Allahu baba,Allah ya bamu ikon riqe amana”hira baban ta shiga zubawa maryam tana maida mata labarin yadda lamarin ya auku,taso ta karbi wani abin ta taya maryam din amma ta qiya don hirar ma kadai da take mata tana debe mata kewa da sata jin qwarin gwiwar aikin,da haka har ta kammala hada fried plaitain with sauce,ta dafa tea da ya wadatu da kayan qamshi lemon grass,kimba da ginger,ta jada da coconut flour pancakes saboda tea din
da yake ba mai yawa tayi ba duka kadan kadan ne daidaisu hakan ne ya bata damar kammalawa da wuri,ta zubawa bab uwani tana ci tana santi maryam na dariya,cikin haka mami ta shigo suka gaisa itama ta shiga dariyar santin da baaba uwani take bayan ta yi mata sannu da isowa,itama tayi mata barka da dawowar abdallah gida,mami tace ta bar baaba uwani ta gyara kitchen din ta wanke kwanukan don dama aikinta ne
cikin kitchen din ta barsu ta shiga dakinta ta gyarashi kana ta shige wanka bayan ta wadati shi da freshner,koda ta fito karyawa tayi ta kuma kwanciya,babu dadewa kuwa bacci ya sureta,sai sha biyu da rabi ta farka,agogo ta duba da hanzari ta shiga toilet ta wanke bakinta da fuskarta ta zura hijabinta dan zuwa saman mamin ta tambayeta a dora girkin rana ne
mrs muhammad ce????
????????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:51 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
▶1⃣5⃣
A qofar falon ta tsaya tayi knocking,daga can ciki taji mamin na tambayar wane,ta amsa mata sannan ta mata izinin ta shigo
A bedroom ta tarad da ita tana gyaran wadrob dinta
”sannu da aiki mami”
”yauwa maryam,sannu”
”mami ai da kin kirani na miki aikin”
”haba,kina bacci maryam ya zan tada ke”
”mami dama cewa nayi me za’a dora,naga rana tana ta yi”
tana zuba wasu kayan cikin sif din tace
”indai don ta Abdallah ne rabu da shi,don ko breal fast din ma baici ba,yana can yana yawon bacci,na yi da shi ua tashi ma ko laruawar ne yayi ya koma kinga yaqi,baqi sai ziwa suke masa sannu da dawowa amma kinga yaqi fitowa wai ramuwar bacci yake,saidai kawai ki dan dafa wani abun ba mai hawa ba saboda ke da baba uwani,ga baqi kuma don nasan yau ba za’a rasa baqi ba”
”to,mami”ta amsa tana shirin juyawa ta fice
”tsaya ki dan taya ni hira,ai yayi wuri a dora shi yanzu mamin ta dakatar da ita tana murmushi
kadan kadan suke hirar tasu har soma taya mamin aikin,tana shirya kayan ta miqa mata ita kuma ta zuba acikin drower din
Bata shirya kallon qofar dakin ba amma tilas tayi hakan,sallama akayi cikin wata murya mai cike da dadi da kwarjini wadda ke bayyana cikar haiba da halittar mamallakinta,second daya da yin sallamar qamshi ya baibaye dakin gadon mamin duk da cewa an dan turo qofar ne kadan an kuma boye a bayan qofar daga waje ba’a kai ga shigowa ba
hannun wanda ya bude qofar mai daure da agogon rolex ne kawai da barin jikinsa zaka hango
”mami na shigo ko na koma?”
”taya zance abdallah ka koma,bismallah qaraso”ta bashi amsa tana kallon qofar fuskarta qunshe da murmushi
ya qarasa turo qofar a hankali ya bada wata ‘yar qara kadan,ya sako farar qafarsa mai dauke da zara zaran yatsuda maau qunshe da gargasa saman kowannensu,sanye yake da shadda fara qal babbar riga da ‘yar ciki da wandonta,baqar hula ce zanna ahannunsa wanda da alama yana tafe ne yana mata kari bai qara sa ba ya iso dakin,fuska cike da qayataccen murmushi yake fadin
”nayi zaton kinyi fishi saboda banyi break ba”
”banyi fushi ba amma banji dadi ba”
”Allah ya bako yawan rai mami na,nima banso nayi missing daddadane n break fast ba,saboda na tabbata zaiyi dadi kamar abincin jiya”
”to ai ga mai girkin nan,sai ka mata sannu”ta fada tana nuna maryam wadda ke,daskare gu guda,kallo daya ta masa ta kasa yin na biyu,ba don komai ba sai wani kwarjini da cika ido da taga yayi mata,duk kyawun mami da take gani aahe nafila ne,wannan tabbas idan da mace ne saidai a hanata fita zuwa ko ina saboda fitar ba qaramin hadari bace tattare da ita da ssauran mutane
ya dan dubeta a fisge atill,kanta na duqe yace
”sannu fa”
ba tare da ta dago ba tace
”ina wuni?”
”lafiya”
ya amsa yana diban mami
”uhm,sai ina kuma”
yana ci gaba da karin hularsa yace
”masallaci mami,kin manta yau juma’a”
”haka ne,ka ci wani babban riga kamar gaske”
”kamar ranar daurin aure na ko mami”ya fada yana qarasawa bakin mirror yana dai daita hular a kanshi
”gafara can,mutumin da ya kasa fidda mace shike zancan ranar aurenshi,kaci gaba dai da zama a tuzurunka har a rasa mai aurenka”