ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

murmushi ya fidda mai dan sauti ya dukin turaten mamin yana sake fesawa
”haba mami,ba irinmu kerasa macen aire ba ko shekara sittin sukayi a duniya,ki kwantar da hankalinki ina nan ina duba miki,kinsan sai na zaba na darje”
”garin ruwan ido kuma fa…”
da sauri ya tare ta
”wayyo mami….yi shiru don Allah,you will be suprise in sha Allah”
”hmmm,Allah yasa….maryam ina zuwa?”ta tambaheta ganin ta miqe
”zanje ne na dora girkin mami”

”abdallah maka lunch ne?”
”kai kuci kayanku kawai mami ni zan wuce gidan baffa mu gaisa”
”to yayi kyau,ka gaishe min su da kyau,muje maryam nima saukar zanyi,kada a shigo a yita nema na”

tare suka sauko dukansu abdallah na gaba,mami na bayansa maryam na binsu a baya
”banza a banza kawai,maras kunyar qarya,gidan da kike taqama da shi ina cewa ‘yar karo ce ke”
surutan wata matashiya kenan lokacin da take shigowa falon,matashiya ce ‘yar zamani wadda shigarta kadai ta isa nuna maka hakan,sanye take da fitted gown wadda tabi lafiyar jikinta,kanta daure da roses sai swagger dinta mai sarqa rataye a kafadarta,takalmin qafarta kuwa kai kace sama take shirin tabowa saboda tsininsa,fuskarta tasha fente fenten kwalliyar zamani
”a’ah salma,ke da wa kuma,hali zanen dutse”inji mami da ta tsaya tana kallonta

”ni da waccar agolan gidan taku mana,duk randa nazo gidan nan sai ta nemi raina min hankali,wallahi abdallah ka ja mata kunne ni ba sa’arta bace,ni na hana ka sota da zata dinga neman huce haushinta akaina,ina ruwan biri da gada,nafsi nafsi kawai”
kafadunshi ya daga yana ware hannayenshi????????‍♂
”ina ruwan abdallah ya taku,kina da baki kema fa”ya fada cikin ko in kula
ta yamutse fuska
”baka fa da kirki wani lokacin wallahi,watsamin to qasa a ido,mami kina jinsa ko”
murmushi tayi
”bismillahi Allah,ai kun fara kuma kenan”

ya dubi mama
”manta da ita mami,ni zan wuce masallaci”
”ni matsalata da kai waqanci wlh,ka sani fa sarai saboda kai na zo,shine zaka wani fita”ta fadi mishi tana kallonshi bayan ta zauna tana sabule cogen qafafunta
”sai na fasa sallar juma’a saboda sarauniyar matan duniya ta zo”ya fada yana yin gaba abinsa
”a’a,ni bance ba amma sai yaushe zaka dawo?”
”qarfe biyar,bit ban tabbas ina iya wuce hakan,idan zaki iya jira na fine”
”ina jira sai ka dawo”
ba tare da ya amsata ba ya qarasa ficewa
maryam na kichen take jiyo su

tunda ta shiga kitchen din bata fito ba sai da ta kammala girkin,lokacin da ya fito mami bata falon sai baquwar da taji an kira salma dake kwance dai dai kan three sitter,kanta ta dago tabi maryam da kallo,hada idon da sukayi bak sata dauke idonta ba
”sannu maryam,kada dai ace har kin kammala?”
inji mami dake saukowa daga saman bene
”eh na gama mami”ta amsa mata bayan ta tsagaita daha tafiyar da takeyi
”sannunki”ta amsa mata sannan ta juya don shigewa dakinta,tana jiyota tana tambayar mamin wace ita?saidai bata ji amsar da mamin ta bata ba

kiran da mamin ta yi mata ne ya sake fito da ita tun bayan shigarta dakin wanda wanka kawai taui ta saiya kayanta tayi salla,biyi taga ‘yan matam sun zama,saidai iya wannan sanhe take da riga da wando wadanda suka bayuana surarta,inda Allah ya taqaita siririya ce sosai,
tadan dauke kanta zuwa sashen da mamin ke zaune
”gani mami”
”yauwa maryam,baki fito kinci abincinki ba,ga baqi yau agodan amma kin zauna a daki”
”mami na qoshi ne sai anjima”
”to zauna muyo hira,bana son kina zaman dakin nan ke daya,na gaya miki nafison ki dinga jin a ranki ke diya ta ce,wannan sunanta salma ‘yar qanwata ce,waccan kuma sunanta saddiqa ita kuma ‘yar yaya na ce,dukansu sunzo yoma abdallah sannu da zuwa”
”sannunku”ta fada cikin sassanyar muryarta

amsawar ganin dama suka mata tamkar wadanda aka tilasta,wanda hakan sam bai,mata dadi ba,har taji zamansun ma guri daya babu marching,don sam bata son wulaqanci,maca ce ita mai karamci shi yasa ako yaushe take tsammanin karamci daga gurin duk wanda zata mu’amaleshi
”am…mami da wai kitchen zan koma in dora abincin dare”
”baki gajiya maryam,a qa’ida ai kin gama girkinki na yau tunda sau biyu ne a rana ko”
kanta na aqasa tayi murmushi
”ba aikinta kenan ba,ki barta mana mami”inji saddiqa wadda ta dora qafa daya kan daya tana danne danne waya da bai wuce tana charting ne

”ba komai mami,ai ba wani qa’ida tsakanin mu,kuma ko ba haka bama ai kinga baqi aka yi,kuma aikin ya abdallah nake,tunda aikinsa nake kinga ba laifi na giwa wadanda suka zo gunshi abinci”
sosai ta burge mamin,tana son mutum mai sauqin kai,wanda ta fuskanci halin maryam ne
yayin da salma da,saddiqa suka dago kai suka kalleta,salma ta kasa shiru
”hmmmm,lallaikam,dadin abun ma biyanka ake ba”

sai abun ya bawa maryam din mamaki,to meye kuma hadin kaska da kifi,me haka kuma,me tayi mata,gaza bawa kanta amsa taui don ita dai yasan yau ta fara ganin salma,babu kuma abunda ya hadata da su balle tace ko ta mata wani abun ne
”salma,bana so fa irin wadan nan halayyar naki kin sani sarai ko”mami ta fada cikin dan hade gira
”yi haquri mami,nima ba wani abu nake nufi ba”
”jeki maryam ki hutar da kanki kiyi iya cikin abdallah kawai,shima din kiyi simple kada ki dauka da wuya”
”to”
ta gada sanna ta miqe ta shige kitchen dinmami ta nita da kallo,yanayin yarinyar na burgeta,sanyi sauqin kai da kawaic yakanah da danne abu cikin rai

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:51 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

    ▶1⃣6⃣

jallop din couse couse ta hada mishi wadda ta wadata da carrot grean beans da piece,sai qoda da hanta a madadin nama,qamshin curry da tyme kadai ke tashi a ciki,yayi shar gwanin sha’awa,sannan ta hada banana apple anda strawberry juice,baaba uwani ta barwa gyaran gun ta wuce ta shirya dining,duk suna zube a falon kowacce da abinda take,ko saahen da ‘yar uwarta ke zaune bai isheta kallo ba tamkar ba ‘yan uwa ba,taji dadi da bata tadda mamin cikin falon ba don haka tana kammalawa ta ahige daki don ko alama bata buqatar zama acikinsu

mutum ce ita mai jan mutuncinta da gudun wulaqanci,

har magariba abdallah bai shigo ba hakanan basu fasa jiransa ba,ana kirayen kirayen sallar isha’i sannan salma fa fara hada tarkacenta tana yima mami sallama,bata kai ga fita ba abdallah ya shigo

sanye yake da jeans baqi da red din t.shirt hannayensa soke cikin aljihun wandonsa,kan sa yasha gyara sai qyalli yake sumar ta masa kyau sosai,ma’abocin qamshi ne hakan yasa turare ke masa rakiya duk ta inda zai gifta

duk yadda salma ta dauki zafi ganinshin da tayi sai taji sakayau tamkar ma bai mata komai ba,ta saki ajiyar zuciya wadda har sai da ta fito fili
”a’ah,yaushe ka shigo gidan?”inji mami
”b fore isha,na shigo nayi wanka ne zan fita sallar isha ne waccar yarinyar ta tsaidani zubaida take ko”
dukansu babu wadda bata shaqa ba,mami ce ma ta dan tare masu don ba dadi
”amma dai kasan ana jiranka tun dazu ko”
ya karuar da wuya yana kallon mami
”hakan ne yasa ma na shigo yanzu mami,don nasan kaskar nan na jirana”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button