ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

qyashin bata wayarshi yake,sai ya saka handsfree kawai ya dan tura ta gabanta kadan
”maryam,ya akayi”cikin rawar murya tace
”wallahi mami ba da niyya bane kaw….”
”manta da abdallah kinji,kici gaba da aikinki,but ki kula da shi kinga bani nan,hakanan sai kinyi haquri da tabarar abdallah don na….”
cikin hanzari ya dawo da wayar gabanshi bayan ya kashe handsfree din yana cewa
”omg mami”
batasan me tace masa ba ta dai ji yace
”ok bye take care”
daga bakin falon ake sallama,bai dubi gun ba yace
”comone guy,idan zaka shigo ka shigo duk ka cikawa mutane kunne da sallama”
matashi ne kusan sa’a,ne ga abdallah
”kaifa baka da mutunci wallahi”
”kai shine da kai ai”
dariya ya saki bayan ya iso ya bashi hannu suka cafke,kujera daua ya ja ya zauna yana leqen flate din dake gaban abdallan
”kai mutumina,irin wannan liyafa haka,rabona ne kawai ya rantse shi yasa na qaraso kenan,da har nayi fushi nace bazan shigo ba”
”kanka ake ji sarkin kwadayi,yi sarving dinshi”yace da maryama wadda ke goge gun da abincin ya taba
sam bai kula da ita ba sai da abdallan yayi magana
”ina kwana”tace masa idonta na kan flaye din da take zuba masa hadin salad
fuakarsa dauke da mayalwacin murmushi ya amsa
”lafiya lau ‘yammata ya gida?”
”lafiya”tace masa ataqaice don ta qagu ta kammala ta bar gun,tun dagowar farko ta lura da yadda yake faman kallonta
tana sauka daga stares din dining atea din taji yana tambayar abdallah
”fatabarakallahu ahsanul khaliqin,abokina wanna fa,cikin family dinku take?”
a qufule abdallan yace”dan iska ban sani ba,kaga wannan tayi kamar da ‘yar dangin mu ne,dan rainin hankali?”
”pls guy yimin bayani don Allah”
sai da ya gama shan qamshinsa kafin yace
”cook dina ce,mami ce ta kawota”
har wani dan zullo hisham yayi
”wow,gaskiya ta qeru wallahi ba qarya,kai….man ba cook mami ta kawo maka ba,matar aure ce wallahi wannan”
abincin bakinsa ya tofar bayan ya dalla masa harar kamar zai cinye shi
”allah ua,isa tsakanin mu kawai hisham,wanna ai cin fuska ne,house girl fa,ni abdallah,i think ka manta waye abdallah ne ko,ya kamata kayo gaggawar tunawa,har yau ba’a qera matar abdallah ba,ni,mai ysada ne don,haka mace mai tsada ce matar abdallah,ban tsammanin ma zanyi aure cikin jinsin hausa fulani,sai na shiga cikin larabawa,i hope ka fahimceni?”
dariya hisham ya qyalqyale da ita kafin yace
”nasan waye abdallah,d expensive man,amma ina tsammanin man ka makance ko?,bana zato ko cikin larabawa kowa ke da irin halittar babe din nan”
”kaga malam ni ba ganewa nake ba,u know ni ba irinka bane mayan mata,kai da ka gano,sai kaje ka qarata ai ko”
”is ok…is ok,ni na gani to ina so”
cikin i dont care yace
”ok,ba laifi,amma daga ranar ka cire abdallah daga list din abokanka”
”why?saboda me ?”
goge hannunshi da tissue kana ya tire kujerar da yake kai ya miqe yana duba agogon hannunshi
”coz babu mai zubda min class,kaga nifa ina da wani aiki,ina da bincike cikin unguwar tudun maliki,so bana buqatar securities su rakani saboda is screet,idan ka gama zub da mutuncin naka ka fito mu wuce”
daga haka yayi saukanshi,hisham na daroya ya miqe ya bishi
maryam dake saman kujera ta tabe baki
”lallai,Allah ya tsareni da da tarayya da ire irenku,kai din ma baka min ba bare abokanka,mai girman kai kawai,kudi ai ba sune mutunci ba”cikin zuciyarga take zanta hakan,ta jawo wayarta ta kira raliya don kada ma ta batawa kanta rai a banza
mrs muhammad ce????
????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:51 PM] 80k: ABADAN18
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
assalamu alaikum wa rahmatullah,ina miqa godiya ta ga dukkanin mutanen da suka yimin ta’aziyya wadanda suka kira ni da wadanda suka turamin saqo sms da watsapp,na gode Allah ya saka da alkahiri ya bada lada,akwai wadanda suka turomin saqo ta watsapp ban musu reply ba su yimin afuwa wayar ce tayi misbehaving duka saqonnin sun goge na gode Allah ya bar zumunci
can cikin uwar dakin suke a zaune su biyu rak,a haka idan ka kallesu sai kayi zaton maganar arziqi suke
”huwaila kenan,ai ni na dade da ganin baikenki,kin kima bani mamaki wallahi”uwani ta fada bayan ta dora qafarta daya kan daya daurin dankwalinta a goshi
”abunda ya faru ya riga ya faru uwale,yanzu meye abunyi mafita nazp nema,tunda na fiskanci abun nata ba na mutunci bane”
”abunyi kuwa akwaishi….”
”cewa nayi kawai mu koma gurin boka mai gayya ya warware aikin da yayi mana da farko,tunda ta inda aka hau ta nan ake sauka”ta gada cikin katse hanzarin uwale
bakinta ta kama tana kallonta
”ai kinji irin wautar taki,ina ke ina dosarsa,ko kin manta cewa yanzu hadiza sun fiki kudin da,zasu biyashi ya musu aiki nan take,ai hannu zamu sauya,ina da wani boka na da ya jima yana min aiki,amma fa sai kin shirya,kudadenki zaki fito da su ajjiyayyun nan”
”amma fa uwale na tarin auren lubabatu ne,na fiddo su kuma a kashe?”
”a aha,to zauna mana kiga idan zasu maganta miki,kin manta cewa idqn aiki yaui kyau wanda zata aura din mai arziqi,ne?,shi zai mata komai da komai ba damu bace ai”
baki huwailan ta washe”kuma fa hakane,kinga ke kin fini hangen nesa,to shikenan babu damuwa,yanzu kina ganin idan na raba su biyi rabi zai yi?”
tabe baki uwale tayi
”kinga malama,idan dqi kina son aiki gangariya ko fiddo da kudi kawai,wai tsoron me kike yi ne?ke da,zaki zama surukar mai arziqi,idan kuma kina ganin abar maganar shikenan sai na barki”
da sauri ta tareta
”a’ah,ba za’ayi haka baai,yanzu kina ganin yaushe zamu tafi?”
sai da ta dan nisa sannan tace
”jibi,jibi laraba kenan,ta bawa ranar samu ba,don mu samu dacewa”
dariya huwailan ta qyalqyale da ita
”gaskiya ne fa,kai Allah ya bar min ke qawata,bari na tashi na tafi kada su fuskanci wani abu,sai Allah ya kaimu kenan”
”to shikenan,Allah ya nuna mana”
tana gama ficewa uwale ta sheqe da dariya
”wawiya kawai,sai na gama tatseki tas,kuma naci halas tunda ba aikin Allah bane,idn banda ke cikakkiyar shashasha ce waye yaqi gidan hutu da jin dadi,nima fa ‘yan matan nan gareni na hadashi mana da wata daga ciki,ai ba ke ladai ce mai son dadi ba”ta ja dogon ysaki kana ta miqe tana gyara daurin zaninta hadi da cewa
”ai ni kuma na samu sana’a har gida ina kwance kudi zasu dinga shigowa
ta waiwayo hannunta dauke da plate cike da tsiren tukunya wanda ya ji kayan hadi ta miqawa abdallah wanda ke tsaye qiqam a bayanta hannayensa harde bisa qirjinsa yana ta zuba mata surutu
”ungo,ai yanzu kam ka qyaleni na fita ko”
yasa fork guda biyj cikin plate din sannan yace
”kin gama wannan mami na,sauranki ci,don kin sani tare zamu ci”
girgiza kai tayi tana goge hannunta da doster din kitchen
”haba abdallah,me yasa wani lokaci kake da rigima kamar yaron goye?,kace tsiren tukunya kake so nace maryama tayi ma kace baka so nawa kake so,yanzun kuma kace sai na zauna munci tare,kaci naka ka ajjyemin nawa,idan na dawo sai naci,ina da patient da nace yau suzo su same ni”
”yau througout ba inda nake so ki fita,duk sun maida min ke kamar wata engine,weekend din ma ba za su barmin ke ki huta ba,kuma ma ni mami bazan iya ci ba idan babu ke”
”alright,ga maryama nan ta wakilceni sai kuci tare”ta fada tana daukan mauafinta dake saqale kan qofan kitchen din
ya kalli maryama ta wutsiyar ido wadda ke fasa qwai cikin bowl zata hada potatoes bolls sannan ya harareta kadan ya dauke idonshi ya maida kan mamin
”mami kina ragemin matsayi gunki,babu wanda zai iya replacing dinki a guna”
”to tunda ba zaka kaci da maryama ba sai na turo maka zubaida,ita ai na zaka qi ba tunda masoyiyarka ce ko”ta fada tana ficewa a kitchen din
maryam wadda kanta yake sunkuye tana kada qwan bata san lokacin da dariya ta ciyota ba don tuna dramer din da suka gama shi da zubaidan dazun da safe,bata snkara ba dariyar ta subuce ta fito
hannayeshi harde bisa qirjinshi as usual,a hankali ya dora kyawawan qwayar idanunsa gefen fuskarta wanda dimple dinta ya fito radau saboda motsawar fuskarta,sai taji duka ta sha jinin jikinta duk da ba kallonshi take ba,cikin second daya tayi qoqarin mai da fuskarta yadda take
hijabinta taji an damqa hade da jawota wanda har hakan ya haddasa fadowarta jikinshi,cikin zafin nama taji ya ja hijabin ya cireshi sannan yayi wurgi da shi,cike da azama tayi gaggawar barin jikinshi,a tsorace take kallonshi tare da takure jikinta guri daya,sanye take da fitted gown na atamfa wanda yabi lafiyar jikinta,a qa’ida dinkin ya mata kadan amma son da takewa atamfar yasa ta kasa bayar da ita,dalilin da yssa kenan duk lokacin da ta sakata hijabi take sawa
tuni oily eyes dinta suka qara sheqi kan wanda suke da shi a da sakamakon taruwar qwalla cikin idanunta,zuciyarta bugu take wanda a take jin ya wuce qa’ida,tama kasa hada ido da shi kamar yadda ta kasa motsawa,saboda idan tace zata motsa din tofa ko ina na jikinta zai motsa din ne
hucinsa taji a gabanta,a hankali ta dago da kanta don kallin abinda ke gabanta,tafin hannunshi ne mai dauke da zara zaran yatsu bude,tsakiyarshi kuma kunama ce qatuwa,saura kadan nunfashinta ya dauke,da sauri ta ja baya sannan ta daga kai ta kalli fuskarshi
gumi ne sosai yake hadawa yayin da idanunshi suka soma sauya kala bisa dukkan alamu ta hahharbeshi bama sau daya ba,a gigice ta koma gabanshin taci burki ganin yana tsaye qiqam yana kallon abunda ke hannun nashi tamkar ba wani abu bane mai cutarwa,hannunta ta saka ta tankwabe hannun nashi kunamar tayi tsalle ta sauka gefanshi,takalminshi ya sanya ya taketa
batasan ta kama hannunshi ba tana lalubar inda dafin yake ba sai da taji ya fisge hannun yana fadin
”mtswee,sakemin hannu dafi na shigar mutum sai ua masa illa kin tsaya shashanci”
hannunshi ya saka ya riqe inda yake tsammani iya nan dafin ya tsaya
zaune yake a falon tunda ya fito a kitchen din,da alsmu xafin harbin na damunshi sosai,duk da ‘yan dabarun da yayi,duk sai ta shiga damuwa tana jin itace sila,ta rasa da me zata taimaka masa,duk sanda ta matso gun da yake sai ta kasa tabuka komai saboda kwarjinin da yake mata,qarshe sai tq koma kitchen din ta dauki wayarta ta kira mami ta sanar mata
sosai mamin ta rude tace ta gaya mishi ya taho asibiti yanzun lallai
kwance ta sameshi saman doguwar kujera
a darare ta matsa kusa da shi kadan cikin sassanyar muryarta
”mami tace ka sameta a asibitinta”
sam bai ji isowarta gun ba sai saukar siririyar muryarta
jin shiru ya sata sake maimaitawa
kusan minti uku kafin yace
”leave me alone pls,bani son naci tunda ni ba kurma bane,sannan bani son gulma,har kin kirata saboda tsaban gulma,bace min a gun”
bata damu ba tunda ta isar da saqon mamin dai,kitchen din ta koma ta fara soya patatoes bolls din duk da rabin hankalinta na ga abdallah wanda bata ji motsin tafiyarshi ba,dalili kenan da yasa taa kammala suyar ta sauke man ta leqo falon,yana kwance abinshi yadda ta barshi,sai ‘yar nutsuwar da ta samu tayi qaura,waishi wane irin mutum ne da ciwo ke cin jikinshi amma bai damu ba
cikin dan qwarin gwiwar da ta tattara ta sake nufarshi da nufin tunassr da shi koda qila ya manta,saidai kafin ta qarasa wayarshi dake ruwan cikinshi ta dauki sassanyar ringing alamun shigowar kira
da alamun kasala ya dauki wayar ya duba mai kiran nasa ya amsa bayan ya maidata handsfree ya dorata saman cikin nasa
”abdallah yaya me na jika shiru?,ko maryama bata sanar maka saqona ba?”
cikin murya mai kama da ta mai bacci yace
”ta gayamin mami,kawai….”
”ya isa bana buqatar uziri,na baka minti talatin in ganka a office dina ok?”
”yes mami”ya fada daga bisani wayar ta katse
cikin sanda ta juya don komawa da baya tunda bai ganta ba
”dakata a nan”ya fada cikin kaurara murya,cak ta tsaya din yayin da shi kuma ya miqe a hankali
”sai ki fito amma zan sake maimata miki ni bani son shishshigi”daga haya ya juya yayi waje
motoci hudu ne baqaqe masu azabar kyau a jere,tun kafin ta qaraso taga abdallah tsaye jikin daya,xubaida ce ke fuskantarta bisa alamu magana suke,isowarta ne ya sanyata jin maganar qarshe da abdallah ke fadi
”nacinki kullum sawa yake ina dada tsanarki,bana son shishshigi bana son naci kuma bana son takura,ki tambayi nene tun asali ke ba type dina bace,bazan taba auran macen da bata yimin ba,ba ko wacce irin mace nake so ba,for now ya kamata ki gane hakan”
ya sanya hannunsa ya janue hannunta data tokareshi da shi ya bude bayan motar da kanshi
”naji abdallah,amma atleast dai a yanzun ka barni na raka ka asibitin bai cancanci ka tafi kai daya ba”
ko kallo bata isheshi ba don tuni ya gama maganarshi da ita
ya juya bayanshi yace da daya daga cikin security dinshi su rage biyu daga cikin motocin da biyu za’a tafi,ya rufe maganar da fadin
”ko kun manta muna bincike kan alhj haladu uba mai qusa,kuma banson yasan ina cikin garin nan,ku kiyaye”
”yes,sir”ya fada cikin girmamawa
kusan tare shi da zubaida idonsu yake kan maryama dake tsaye daura da su
”me kika tsaya kina wa mutane a gurin?”
cikin tattausan muryarta tace
”bansan wacce mota zan shiga ba ai”
”saikiyita sanqamewa anan har a tashi qiyama”ya fada yana shirin shigewa motar
”amma abdallah wannan ita kuma fa?”
wani kallon biyu babu ya mata cike da quluwa da tarin tambayoyin da nabu macen da isa ta masa su idan ba maminshi ba,tsaki ya ja mata sannan ya ja motarshi ya bame
sun gama reverse suna shirin ficewa maryama dake motar baya cikin gidan baya a takure saboda su uku ne maza biyu ita ta ukun taji an dakatar da su,abdallah ne ya fito ya qaraso har gaban motar,glass din duka motar yasa suka sauke ya qare musu kallo sannan yace da na gaban motar
”you are verry stupid lawal,oya getout ka koma baya,ke kuma ki fito ki dawo gaba saunar yarinya kin shige cikin maza kin wane qwame”
yana tsaye akayi hakan sannan ya bisu da tsaki ya kona tashi motar duka direbobin suka ja suka fice a gidan
ABDULLAHI SPECIALIST HOSPITAL shine abinda ke rubuce jikin wani makeken allo dake maqale a goshin ginin benan asibitin,wanda ko daga ina ka taho zaka gani saboda girman allon da rubutun da kuma tsahon benan,gini ne na alfarma tamkar ba asibiti ba,komai neat bisa tsafta tsari da kuma qwarewa,tun daga parking space ma’aikatan dake cikin harabar asibiti leburori da masu gadi suka soma tururuwar zuwa gaida abdallah,ga mamakin maryam hannu yake basu suna mudabaha cikin fara’a da sakin fuska
a haka suka ratsa cikin asibitin har zuwa sashen da office din mami na musamman yake
”wonderful,abdul dama kana nigeria?”suka ji an fada,wani matashi ne wanda ke nufosu yake fadar haka,sanye yake cikin qananun kaya wanda kallo daya zaka mishi kasan dan birni ne yasan gayu gayu ya sanshi,ba wani mugun kyau ne da shi ba amma iya adonshi ya bashi sunan kyakkyawa
da fara’a sukayi musabaha da abdallah
”idan ban manta ba shekaru biyar rabona da kai abdallah,yanzu laifin kudrat sai ya shafi mansur?”
dan qaramin murmushi ya saki kana yace cikin basarwa
”manta kawai friend ya bayan rabuwa?”sai alkhairi abdul,hala wannan ce madam din tamu?”
wani haushi ya kama abdallah don yasan ba kowa yake nufi ba sai maryam,sai ya zuba mata ido yaga yadda zata karbi maganar,babu abinda ya fuskanta tattare da ita don kanta a sunkuye yake jinta take kamar ta,zura a guje,ta takura matuqa cikin tafiyar nan
maida kallonshi yayi gun mansur
”kada ka sake fadi,cook dina ce,nazo ganin mami na ne ta shigo cikin sahun bodyguard”
murmushi mansur din yayi
”tofa wannan karon babu rabuwa abdul,bani adress dinka,zan sameka har gida,ina da magana da kai”
saboda yanayin aikinshi yasa bai bashi adress din gidan ba kai tsaye sai ya amshi phone num din mansur din yace zai nemeshi duk lokacin da zasu hadun,sukayi sallama kana suka nufi office din mami
duka a waje suka tsaya abdalla ne ya shiga ciki,fitowar mamin kenan daga toilet ta daura alwala
”ina maryam din”ta tambayeshi tana shimfida abun sallah
”suna waje”
”kana nufin har ita din”
”eh mana mami,har da ita”
”koma ka shigo min da ita”
cikin shagwaba yace
”yanzu mami a gabanta za’a min treatment din bayan da zafi kuma salon ta raina ni”
ita dai mami bata kulashi ba ta tayar da sallarta,tilas ya koma yace da lawal ya shigo da ita
mrs muhammad ce
[9/17, 12:52 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
???? ▶1⃣9⃣