ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

teburin mamin yayi zamanshi yaja laptop dinta yana danne danne ya barta nan a tsaye,a haka mamin ta kammala sallarta ta shafa addu’o’inta
”sannu maryama ya akayi kunama ta sami abdallah?”mamin ta fada cikin kulawa tana linke sallayarta
”tsautsayi ne mami”taji abdallah ya amshe zancan yayin da tayi duru duru tana tsaka da neman amsar da zata bawa mamin
”Allah ya tsare gaba to,amma ya kamata ka daina zuwa gun da ta samekan,don nasan bazai wuce cikin garden ba”ta fada tana hada allurai cikin syringe

maryama tsayawa kawai tayi tana kallon yadda abdallan keta marairaita kamar qanqanin yaro,ita abun ma kunya ya dinga bata,amma shikam ta fuskanci ko ajikinshi wai an tsikari kakkausa
”wannan matarshi zata sha fama da shagwaba,mami duka ta sangartashi”tayi gulmarshi cikin zuciyarta,da sun hada ido sai ya maka mata harara hakan ya sanya ta dauke kanta ta maida kan dan wani qaramin frame me masifar kyau dake kafe kan table din mamin,hoton wani yaro ne wanda bazai haura shekaru takwas ba cikin shigar tazarce da hula da takalmi sawu ciki,ko shakka babu wanna hoton abdallah ne lokacin quruciyarshi,kyawunshi ba loka in girmanshi ne kawai ba kyawu ne na tun usuli

ya lura hoton take kallo don haka ya miqa hannu ya tuntsurar da shi,ya dan bada qara sakamakon haduwarshi da table din har sai da mami ta dago ta dubeshi sannan ta dubi frame din,ta fuskanci abunda yake nufi don haka murmushi kawai tayi can qasan ranta taci gaba da abunda take

bayan mamin ta kammala bashi duka wani taimako na kashe radadi da kuma tsaida dafin sai ta hada mishi da magani,minti goma tsakani mami tace ya taahi su wuce amma sai ya marairaice kan cewa bari ya huta,wayarshi dake gefan system din mami ta dauki kida,kamar bazai daga ba amma yana dubawa yayi hanzarin dagwa
”sir,munga alhj haladu uba mai qusa yanzu cikin asibitin nan”abinda aka fada kenan da ya sanyashi hanzarin miqewa,mami ta dubeshi
”lafiya abdallah?”
”mami ina zuwa,just twenty minute”bai tsaya sauraron komai ba ya fice daga office din,yayin da mamin ta bishi da kallo cikin ranta tana masa addu’a,ita kanta mqryam din binshi tayi da ido cikin mamakin me ya sanya masa kuzari haka lokaci guda,mutumin da anyi anyi ya tashi a tafi gida ya qiya?ya tsaya shagwaba

shudewar kusan sa’a biyu har mami ta soma nuna damuwa sai gashi ya dawo,zufa duka ta wankeshi,cikin kulawa mamin ta dubeshi
”lafiya dai abdallah?”ta sake tambayarshi karo na biyu
”mami na samu nasarar kama alhj haladu,saura alhj hamza naira”ya bata amsa yana tsiyaya ruwa mai sanyi cikin tambulan na glass

ba mami ba,hatta da maryama dake zaune can gefe ba qaramin burgeta yayi ba,tana tsammanin dazun nan taji uana zancan neman mutumin amma har ya sami nasarar cafkeshi cikin abunda bai gaza awa daya da rabi ba,fuskarta qunshe da madaukakin murmushi take fadin
”masha Allah masha Allah,lallai dana daya da daya ne,baka tsinta aqasa ba abdallah,fata na Allah ya tsaremin kai yaci gaba da yi maka jagora,ya baka ikon ci gaba da tsayawa akan gaskiua,ya rabaka da aikinka lafiya”

yana kurbar ruwan sanyin yana ratsa qwaqwalwarsa sannan sanyin dadin addu’ar mahaifiya na sake shigarshi
”ameen ummi na,kullum addu’arki ita ce sirrin nasarata a rayuwa”
cikin mintina gona suka bar asibitin harda ummin don lokacin tashinta yayi

Sashensa ya wuce mami ta haura sama itama don kintsawa yayin da maryam kuma ta koma kitchen don kammala masu abincin dare tunda tuni an fara ahirye shiryen kiran salla,fashin sallar da take ne ya bata damar ci gaba da ayyukanta
shigarta kenan ta kunna gas tana shirin aza tukunya samanshi taga kamar anyi wuf an fice daga kitchen din,da sauri tabi hanyar fitan itama tana dube dube,bata ci nasarar ganin kowa ba sai adnan yayan zubaida dake shigowa cikin waiting room,wanda sairan qiris suyi karo da shi tayi saurin ja baya atsorace

kallo yake qare mata hade da wani shu’umin murmushi wanda hakan ya sanyata ta tsargu,ta tsani namini mai kallo don a aqidarta takan fassara mutum ne kawai da dan iska
”yi a hankali mana baby kada ki jiwa wannan kyakkyawan jikin ciwo ko”babu abunda tace da shi sai juyawa da tayi cikin sassarfa ta koma kitchen shi kuma ya mata rakiyar idanu,sai da ta bace ya wani lashe labba kana ya shige bangaransu

nene tayi saurin damqo wuyan rigarshi don ta fuskanci baima gansu ba a inda suke labe ita da zahariyya suna gano farfajiyar waiting parlour wucesu zaiyi,a razane ya juyo
”banza solobiyo kawai,harka wani tsorata,amma ka iya tsayawa kana qarewa jikin yarinya kallo”
kansa ya shafa yana fadin”to ai nene ba laifi bane”
”kaga ni ba wannan ba,kaga alamun yarinyar nan ta fuskanci an shiga kitchen dinsu ne?”
”eh to,ni dai na ganta a gurguje da alamu wani ta biyo”
”hanyar ina kaga tayi?”
”hanyar valcony”
ajiyar zuciya nene ta saki
”Allah na gode maka bata ga ko waye ba,kuma da alamu bata fuskanci komai ba”

”ya?nene?”adnan ya tambaya yana dagawa uwar gira
”mun aiwatar da aikin mu,saidai mu jira sakamako kuma,indai kuwa sakamako yazo da kyau,to mafarkin kowannen mu ya gama cika,don wannan karon indai aikin mu yaje inda ake buqata to babu makawa burinnu sai ya cika”
tsallen murna yayi
”that’s why nake sonki nene,amma….”
ya katse maganar jin takun saukowa daga saman bene,zubaida ce,itama dubansu tayi kamar yadda suka dubeta,ganin yanayin fuskartq bai sauya ba ya tabbatar musu bata ji komai ba,gurin t.v ta nufa ta kunna sanna ta kamo tashar da take da buqatar kalla ba tare da tace da su komai ba,haushinsu duka take ji don dazun sun dqn haura sama kan yadda take son abdallah yana yarfata

kuyi haquri da wannan sakamakon na wuni gurin mama na da bata jin dadi sosai,muna buqatar addu’o’inku,na gode

mrs muhammad ce????

???? ????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:52 PM] 80k: ABADAN20
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Gab da isha’i ta kammala tuwon semovita miyar busashshiyar kubewa,kan dining ta jera konai yayi net sannan ta barwa baba uwani gyaran kitchen kamar ko yaushe ta shige bedroom dinta,wanka tayi ta shirya cikin atamfa doguwar riga ta haye gadonta don ba salla zata yi ba
research ta shiga yi kamar yadda al’adarta take lokaci bayan lokaci idan ta samu kanta free kamar yanzun
takwas da rabi da mintina hudu kiran mami ya shigo wayarta,a ladabce ta daga
”maryamu an kammala abinci ne?”
”eh mami na kammala”
”ok,taimaka don Allah ki shirya abincin cikin folding basket ki kawo nan sashen abdallah anan zamuci,nazo bashi magani kuma ya ruqeni”
”to,amma mami ban san inda saahen yake ba”
”idan kika fito cikin balcony gefen hannun damanki zaki miqehar sai kinzo qarshenta”
”to gani nan”
tsaf ta shiryasu cikin basket din mai kalan ja da fari,hijabinta ta zura mai hannu ta sanya slipper ta dauki basket din ta fito
a hankali take taka balcony din tana sake qara kallonta don bata taba yin area din ba tunda tazo gidan,sai taji kamar kada tafiyar ta qare saboda dadin da yanayin yayi mata,iskace take busawa mai mai sanyi hade da qamshin qasa wanda hakan ke alamta lallai yau wani sashe na cikin garin kano yana samun saukar ruwan sama,kasancewar shigowar yanayin damina,duk da cewa har yau tasu area din basu samu ruwan ba saidai yawaitar haduwar hadari da bajewarsa
Qiris ya rage ta bangajeta Allah yasa tayi saurin cin burki,zubaida ce tsaye a gabanta tana huci,a zaton maryama bata da case don ita don haka tayi qoqarin gewayeta ta wuce,binta ta sakeyi ta sha gabanta
”lafiya?”maryam ta tambayi zubaidan cikin sanyin nan nata
”kiyi qoqarin kame kanki daga cikin lamuran abdallah,don na fuskanci wani rawa kanki yake,bari in tuna miki idan kin manta,ke ba kowa bace cikin rayuwar abdallah face ‘yar aiki wadda bata da maraba da baiwa,babu abunda abdallah zaici dake,gargadinki kuma nake ba shawara bace”
ta mata kallon sama da qasa hade da bangazarta ta wuce,da kallo ta bita harda waiwaye,sai da ta bacewa ganinta sannan ta dawo kallon gabanta
sam abun vai bata haushi ba sai ma dariya wanda hakan ya sanyata murmusawa hade da kada kai ita daya,idan banda abun zubaida ina zata kai abdallah?,me zata ci da shi,sam ko kadan ma ita dai dai da second bata taba qyasta wani abu wai tsakaninta da shi ba
da wannan tunanin ta qarasa sashen,da qyar ta samu ta iya shiga saboda tun daga qofa ta soma ganin bambanci,hamshaqin parlour ne wanda zata iya cewa bata taba tozali da makamancinsa ido da ido ba saidai ko cikin hotuna
kusan shima komai na parlour din fari nesai ratsin maroon kadan da baqi
kujeru set uku ya lamushe don shi din ma ba baye bane gun girma da kuma tsari,kowacce kujera na rukuninta daban,girmanshi baiyi yawa ba haka nan baiyi kadan ba,bisa can dining area din dake daura da matattakalar bene ta hangosu wanda hakan ke nuna mata sunyi ready ita suke jira
a nutse ta qarasa ta soma serving dinsu mami da abdallanta na hirarsu,ta turawa kowa plate din tuwo da miyarshi ta sona kiciniyar bude flask din patatoes balls din
”meye haka?,wani sabon salon raini ne haka,ta yaya zaki raba mana plate ko yau kija fara sanin tare muke cin abinci?”
abdallah ya fada cikin hade gira yana typing saqo a wayarshi
ta saki flask din da niyyar hade masu abincin a plate guda mami tace
”rabu da shi fitananne kawai,kalna mai sauqi kace hada mana sai ka ja wani dogon magana?”
”wallahi mami ke ke shagwaba yarinyar nan da yawa,shi yasa kullum sai ta yima mutane shirme”
”Allah ko,ita ce ma kai”inji mamin
da daidai ta soma jera patatoes balls din cikin plate,saidai duk wanda ta dago ssi taga ya rabe biyu,tayi tsammanin tauri yayi da yawa yssa yake haka,don haka a hankali ta lallabashi ta gama jerawa cikin plate din ta tura musu,tana shirin sauka qasa mami tace ta zauna ta saka hannu suci tare,ce mata tayi taci nata ta qoshi
”kunyanki yayi yawa maryam,har yau kin kssa daukan kanki a matsayin diyata ko?,shikenan tunda ba zaki ci da mu ba zauna muyi hira tare idan na kammala mu wuce”
tilas ta koma ta ja kujera daya ta zauna kanta na sunkuye a qasa,lokaci lokaci mami na jefata cikin hirar don ta sake cikinsu saidai kaifin idanun abdallah ya hanata,duk tunda ta zauna din qurar da ta kwasota ma bai duba ba duka ya tattara hankalinshi kan maminshi da plate din abincinsu
abdalla ne ya soma tsame hannunshi yana fadin
”mami turomin daya plate din”ta tura masan tana ci gaba da cin tuwonta don ita duka wadannan yame yamen basu dameta ba
hannunshi ya saka ua dauki guda daya,lokaci guda wata matsananciyar faduwar gaba da sameta,rashin yarda da patatoes balls din ya kamata cikin tazarar lokacin da bai wuce second biyar ba
kai balls din bakinsa yayi daidai da saukar hannun maryama kan nashi hannun ta buge da qarfi har yaji zafi,ba 6ata lokaci balls din ya fadi saman teburin cin abincin ya wargaje,wani ruwa yellow din ruwa ya soma fita daga tsakiyanshi wanda idan ba sani kayi ba zaka yi tsammani ruwan curry ne,wannan shi ya taimaka daga abdallah har mami basu kula da shi ba
zuciyarta taci gaba da tsananin bugu,tsoro qarara ya bayyana cikin fuskarta,tana tuna giftawar data gani dazu cikin kitchen da ta rasa ta waye?,sa’an nan ta dawo da tunaninta kan dalilin daukota don kula da abincin abdallah,guba ne fa?guba abdallah yaci sau biyu a baya,kada fa ayi amfani da damarta a aikata wani mummunan abu,a zafafe abdallah ya kalleta,ranshi yayi tsananin bacin da har ya gaza tambayarta sai mami ce tace
”a’ah,ya haka maryamu?”
”barta mami,ai dama daga ganin wannan yarinyar bata da kunya,in banda tsabar rashin mutunci ya mutum yana…..”
dakatar da shi tayi tana kallon maryam wadda ke qoqarin daidaita natsuwarta don lalubo dalilin da zata bada wanda har ya kai ta aikata abunda ta aikata din yanzun
ba shiri ta tsinci bakinta na fadin
”mam…mi na manta ne ba gishiri da magi cikin balls din,da muka tafi asibiti ashe ban zuba ba,kada kuma yaci yaji babu dadi a bakinsa”
”amma banda abun maryamu ai sai kice mishi kawai kada yaci,next time ba haka ake gyara ba kin fahimta?”
da sauri take gyada kai tana cewa”eh mami,kayi haquri”
ta fada tana kallin abdallah,fararen idanunshi da ya zuba mata yana kallonta shi ya kuma sakata rudewa har ta rasa me zata aiwatar,ba shiri ta shiga tattara fasashen balls din dake gabanshi tana niyyar kwashewa taji ya riqe tsintsiyar hannunta
a razane ta dago idanunta suka shiga cikin nashi,ta danyi kusa da shi hakan ya sanya yaji kaifin idanun nata har qwaqwalwarshi
”daina kallona da idanu sai kace na mage”maganar ta subuce masa
ya maye gurbinta a dan tsawace da fadin
”qarya kike,wannan bai kai dalili ba,na gano wani abu daban cikin ranki,akwai dalili amma ba wannan ba”
tuni qwalla suka cika mata idanu,cikin son kare kanta tace
”da gaske nake,ba qarya nayi ba ka yadda yaya abdallah”
”akan me zan yarda dake,bayan ire irenki biyu sun so ganin qarshen numfashi na a baya,kema kin biyo sahu ne?”ya fada yana huci
tuni qwallan da ta tara a idanunta suka cika suka zama hawaye,ba b’ata lokaci suka soma gangarowa kuncinta,kuja ta qwace mata,tsoro da rauni suka mamayeta
”me kakayi haka ne abdallah,sakar mata hannu”mami ta fada cikun fushi
”mami yarinyar nan ban yarda da ita ba,baki ga reaction dinta bane?,aikina kenan mami nasan reaction din masu laifi”
”ina ce nan ba a office din SS muke ba,ai kin naka baka gwadashi a baya ba sai akan maryam,comon bani son sakarci sakar mata hannu tun kafin in sabar maka”dolenshi ya saketa amma duk da haka bai barta ba binta yake da ido
”oya maryam,tattara kayan nan ki tafi kije ki kwanta gani nan tahowa”jikknta na rawa ta dinga hada kwanukan,tausayinta fal zuciyar mami tana ganin abdallah ne ya tsoratata
”abdallah,ka saurareni da kyau,ba da ka zan dauko maka maryam a matsayin cook ba,nayi bincike mai kyau game da ita,nasan halayenta gaba da baya,baya ga haka nasha yin istihara game da zamanta da mu jikina na bani alkhairi ce ita,saboda haka ina mai tabbatar maka maryam ba zata taba iya cutar da wani dan adam ba balle mu,ni maminka nake gaya maka wanna maganar ba wata ba ka fahimceni?”a ladabce ya amsa mata
”kada ka sake mata irin haka,gaba daya ka tsoratata,ka kiyaye gaba,”
”insha Allahu bazan sake ba”tafiya taso yi amma ya kasa ya tsare ya hanata,sai da ya sata dariya kana ya mata rakiya har bedroom dinta sannan ya dawo bangarenshi
maryam kuwa jiki na rawa ta isa dakin baccinta bayan ta tabbatar ta yiwa patatoes balls din mugun boyon da babu mai ganinshi sai ita,sam bata qaunar tashin hankaki a rayuwarta,kuka ta zauna tanayi riris a bakin gadonta,lijaci mai tsawo ta dauka a haka kafin ta gane cewa kuka babu abunda zai amfanar da ita,ta tabbatar da cewa rayuwar cikin gidan akwai wani qulli da su su mamin basu san da shi ba,fargabarta daya kada wani abu ya samu abdallah ta sanadinta,idan ta fada wannan shingen wazai fiddata
bata da wannan gatan saidai yadda Allah kawai yayi da ita
har kusan uku na dare ta kasa runtsawa,sai da wayarta ta buga alarm na qarfe uku da rabi wato dai dai lokacin tashibta sallar dare kenan sanna ta shiga toilet ta daura alwala
kusan dadewarta ta yau tana addu’a tafi ta kullum har sai da kiran assalatu ya rusketa,sallar asuba tayi ta dora da azkar zuwa qarfe bakwai ta fita kitchen
sam jikinta babu kuzari kamar yadda zuciyarta babu dadi,fuskarta kadai ka kalla ta isheka amsa saboda ja da ta hada da kuma tasawa da idanunta suka danyi,a kasalance take hada musu break din wanda ya kaita har qarfe goma bata kammala ba saboda rashin qwarin jiki
goma da minti ashirin da shidda ta ji sallamar mami cikin kitchen din,a hankali ta dago tana amsa mata kafin daga bisani ta rusuna ta gaidata bata damu da amsawa ba ta dora da tambayar maryam din cikin fuskar rashin jin dadi
”maryam,lafiya?,me ya samu fuskarki?,kada kice min kwanan kuka kikayi?,abdallah ne ko?”
zuciyarya ta danyi rauni amma sai ta dake,ta dan murmusa kadan hadi da kada kanta
”ko baki fada ba na sani shine,kiyi haquri kinji maryam na mishi fada kuma insha Allahu haka ba zata sake faruwa ba,ni zan fita,ga wannan albashinki ne na wannan watan”ta fada tana zaro rafar kudin daga jakarta sababbi kar da su
hannu biyu ta saka ta amsa sanna ta mata godiya
”nice da godiya maryam,inajin dadin zama dake,kina da kyawawan halaye da mutane da dama suka rasashi a wannan lokacin,fata na Allah ya baki miji na gari maryam wanda zai riqekibisa gaskiya da amana”
kunya maganar ta bawa maryam wanda yana daya dqga cikin halayenta dake burge mami
lura tayi da akwai magana a bakin maryam din
”kamar kina son cewa wani abu ko?”
”dama yau inason inje gida ne”
”hoo,maryamu,wannan din ne kika kasa fada,banda abunki ai kinyi kara ma wata guda baki gansu ba,babu matsala zan yiwa driver magan ki shirya sai ya kaiki idan zaki dawo ki masa waya yazo ya daukeki,idqn baki dawo da wuri ba ma babu damuwa ni da wuri zan dawo gida yau in yaso sai na mana dinner dinko,ki gaishemin da mutanan gidan da kyau kinji,zan ajjiye miki saqo a parlour idan kin tashi tafiya ki tafi musu da shi”
godiya sosai ta yiwa mamin tare da yaba karamcinta,tana kammala breakfast din ta shirya a gurguje cikin baqar abaya wadda ta sake fidda sirrin kyawunta ta kuma haska farar fatarta wadda ta sake fresh saboda zama gu daya da kuma sanyin a.c,kitchen ta koma ta juye duka patatoes balls din cikin leda bag ta daure ta jefa shi cikon jakarta,sai da ta tabbatar ta qulle duk inda tasan idan an shigo shi za’a iya samun matsala gun abinci ko abunsha da zasuyi amfani da shi sannan ta fita,hatta da breakfast sai data nemi alfarmar baba uwani ta kula da shi kafin abdallan yazo yaci
cikin motar ta zaro wayarta ta lalubi number din raliya,har tayi ringing ta katse ba’a daga ba sai da ta sake kira,bugu daya ta daga
”sorry sis,fadil ne ya rudani da kuka na kasa daga kiran”sama sama suka gaisa,tana shirin tsokanarta taji muruarta ba yadda ta saba ji ba sai kawai ta share
tambayarta tayi zata iya samun nasir abban fadil a asibiti ko bai fita ba
”tun dazun ya fita,ina tsammanin ma yakai awa uku acan”godiya ta mata ta kashe wayar,kamar ta tambayeta lafiya?sai kuma taga bai kamata ba,idan da buqatar taji maryam ba mai boye mata bane,a mutunce ta cewa driver din zooroad zasu fara zuwa ya amsa mata sanna ya sauya akalar motar
*mrs muhammad ce
[9/17, 12:52 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? *ABADAN*????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
*WRITTEN BY*
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
???? ▶2⃣1⃣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button