ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

yar fadakarwa

shin ko kinsan gwalagwalan kwanakin da muke ciki ‘yar uwa?,kwanaki ne masu matuqar tsada da daraja har agun Allah madaukaki,kwanaki ne da ayyukan alkhairi suka fi soyuwa agun ubangiji a cikinsu,kwanaki ne mafi daukaka cikin kwanakin shekara,an karbo hadisi daga imamu bukhari r.a,annabi s.a.w yana cewa(babu wasu kwanaki da kyawawan ayyuka sukafi soyuwa agun ubangiji kamar kwanakin goman farko na watan zulhijja,sahabbai suka ce da annabi hatta jihadi saboda Allah?,annabi yace eh har jihadi,saidai mutumin da ya fita jihadi da ranshi da dukiyarshi bai dawo da komai ba),shin me kike aikatawa na neman lada?,kada ki yarda su shude ba tare da kin amfana da komai ba,baki da tabbacin ganin na wata shekarar,Allah ya karbi ibadun mu yasa mu dace ameen

????????????????????????????

Minti talatin suka isa asibitin da nasir ke aiki,ta taradda marasa lafiya da suka rigata zuwa,hakan yasa tabi doka itama ta hau kan layi,don ta sani indai tace masa ta zo babu makawa sawa zaiyo ta ahiga kawai ita kuma ba zata so shiga haqqin wani ba

ko kafin azo kanta tuni ta qosa,jira ne na tsawon awa guda da rabi kafin ta samu shiga,da mamaki yake dubanta tare da fadin
”yau kuma an tuna da mu kenan”
dan qaramin murmushi tayi kan ta haye kujerar da masu buqatar ganinshi ke zamansa
gaisawa sukayi yaso ya dan tsokaneta yadda auka saba sai kuma ya fuskanci yanayonta ba yadda ya saba ganinta bane

madaidaiciyar handbag dinta ta zuge ta fidso da leda bag din ta dorata saman table dinshi
”taimako nake buqata daga gurinka nasir ko zaka iya yimin shi?”
”me zai hana maryam indai ba kaucewa addini ba”
”abunda ke cikin nan nake da buqatar a duba min ko akwai poising a ciki?”
ido ya dan zuba mata kamar mai buqatar qarin bayani,gganin bata da niyyar qara masa haske yasa ya kauda idonshi kana yace
”ok,ba damuwa,ga kujera can zauna bari na kira lab azo a dauka”

cikin mintina uku kacal wani matashi ya shigo sanye da farar labcoat ya dauki ledar ya fice

mintina arba’in din da yayi kafin ya dawo jinsu tayi kamar awa arba’in ne,tuna ni babu kalan wanda bata yishi ba,dawowarahin tayi daidai da kammala ganin patiente da nasir yayi,hakan ne ya bawa matashin damar zama tare da miqawa nasir result din ya ajjiye ledar a qasa yana duban fuskar nasir din

nuni ya yiwa maryam din da hannu kan ta taso idanunshi na cikin takardar,a sabule ta iso gaban teburin ta samu kujera daya cikin biyun dake gun ta zauna
”maryama….taya aka samu irin wannan mummunar gubar cikin abinci?,kinsan nau’in guba iri wannan bamu da ita ma sosai cikin qasar nan?,guba ce da ke iya kashe mutum cikin mintunan da basu gaza biyu ba,baya ga haka hatta da gawarka ma bata qyaleta ba sai ta narka duka kayan cikin mutum,dubi yadda ta maida wannan dankalin”ya mata nuni dashi dake cikin ledar da yasa matashin ya bude

A hankali ta maida firgitattun idanunta kan ledar,dankalin ya zagwnye ya koma kamar ruwan kunu,hakanan gabaki daya kalarshi ta sauya zuwa kore da baqi,kumfa ce kawai ke tsattsafa a samanshi tamkar ya ahekara ne da sarrafawa ba kwana daya ba,wani irin tsoro ya sake kama maryam,da sauri ta maida idonta kan nasir,cikin rawar murya tace
”ko zan iya ganinka kai daya?”
”why not?,sadam dan bamu guri”

office din ya rage daga ita sai shi,a hanakli ta zayyana masa dukkan abunda ta sani,ya jima yana jinjina kai kafin yace
”maryam akwai hadari mai girma tattare da gidan,saidai abu guda da ban goyi bayanki ba barin gidan da kike shirin yi,barinki gidan ayanzu dai dai yake da mutuwar abdallah da maharfiyarshi,bayan kin gano matsalar da su basu san da ita ba,shawarar da zan baki shine kawai ki zama mai matuqar kula da takatsantsan,abu na gaba shine ki riqe addu’a,qarfinta da kaifinta ya sha gaban duk wani kaidi da zalunci”

sun shafe fiye da mintuna talatin yana bata shawarwari wadanda syka sa taji hankalinta ya kwanta,nutsuwarta ta dan dawo,da kanshi suka zagaya can bayan asibitin sukayi haqa ya binne ledar patatoes din
”yanzun kuma sai ina?”ya tambayeta bayan sun isa bakin get din asibitin
”gida na nufa inje inga mama”
”gashi wani aikin yanzu zan koma ciki na qarasa kinga ai da na kaiki”
”ba damuwa,zan hau adaidaita sahu yanzun zaka ga naje”

a gabanshi ta hau napep din ya biya mata ta wuce bayan ta masa godiya,murmushi kawai yayi
”kada ki damu,ke da raliya duka abu daya ne”

har qofan layinsu dan adaidaitan ya direta saboda babu damar shiga layin nasu,ba dob matsi ba sai don yawan kwatoci da suke da su budaddu wadanda ke wa ababan hawa cikas gurin wucewa,sannu a ankali take takwa har ta isa qofar gidansu

Ba laifi akwai ahige da ficen al’umma wanda baka rasa gidan da shi sakamakon yawan ‘ya’ya da sana’a da auke da shi,musamman a irin wanna lokaci da ake shirin tada sallar azahar masu neman abincin rana nata hada hadar siya,wanda ayanzun huwaila ce kadai keyi don inna hadiza na ganin yanzun ta girmewa haka

da ”zan wuce zan wuce”ta samu shiga cikin gidan saboda yawan mazan dake soron suna dakon a miqo musu abincinsu,can tsakiyar yara ta hango lubabatu da daurin qirji tana zuzzuba abincin a kwano tana mita,alamu dake nuna cewa inna huwaila bata nan kenan ita aka bari da aikin abincin,qofar dakin inna hadiza kuwa labule ne asake qarar music na fita,kada kanta tayi cikin zuciyarta tana fadin”fidan mu,gidan mu kenan,ya Allah ka daidaita shi kamar kowanne gida”ta cire takalmanta tashige dakin mamanta

daidai lokacin da maman ta fito daga dakin da suka maida kitchen dauke da farar roba da ta zuba shinkafa danya aciki,da alama girki take wato yau baban nasu yayi tsiyar kenan kowa kansa yau zai ciyar
murmushi ya subucewa maman kamar yadda ya bayyana fuskar maryamu,wani farinciki dukkansu suke ji wato da da uwa ba wasa ba,ta isa gaban maman tana niyyar amsar robar hannunta yayin da mamar ke cewa
”maraba,yau kece atafe,a’ah barmin kayana yanu zan kammala ai,daga ahigowarki ko hutawa baki yi ba”dole ta qyale maman ta fita waje ta wanko shinkafar ta ta zuba sanna ta dawo ta zauna

hira sosai suke da mamar nata har ta kammala shinkafa da wake da an quli hade da salad tumatir albasa da cocumber,zasu tada sallar kenan hindatu ta shigo,murna kamar ta cinye maryam,cewa tayi itama ba zata zauna ba bari ta fara sallar,ta yada takardun jarrabawarta saman kujera ta fita ta yo alwala

Dari biyar maryam ta fitar ta bawa hindatu da kanta taje ta aiyo musu serdine soyayye suka zauna hankali kwance suna cin abincinsu suna hira,hindatu sai santin maryam take
”wallahi adda maryam kada kiso kiga yadda kika koma,kin zama wata hajiya skin dinki tayi wani freah,qiba ce kawai baki qara ba,kinga kiwa da kin dada qiba tsawon nan naki raguwa ziyi”
dariya ma ta basu mama tace
”to sarkin zance,kiyi a hankali dai kada ki qware”cikin nishadi auka kammala hindatu ta guara gurin ta dawo suka sake bude sabon babin hira,da daidai da daidai take jin matsalolinsu,sai taji dadi jin cewa basu da wata matsala mai yawa,mama tana cikin lemonta sosai don haka sai dan abunda ba’a rasa ba,wanda shina mafi yawa kan karatun hindatu ne

duka albaahinta ta fidso ta damqawa maman tana fadin ta fadi abunda ya dace ayi da su
”um um maryamu,ke din mai hankali ce,na tabbata ko bance komai ba zaki yi duka bunda ya dace din”
tana lissafawa mama abunda takeso tayi din maman na sa mata albarka,ciki harda aiyqn kayan abinci ta ajjiye agidan nasu tunda albaagin nata ya tasamma dubu dari

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button