ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????
tafiya take bata ko ganin gabanta saboda takaici da baqinciki,wai sai yaushe ne burinsu zai cika kan abdallah?,sai yaushe zasu samu nasarar kau da abdallah daga doron duniya,da wannan tunani ta samu da qyar ta maida kanta bangarensu
adnan da zahariyya dake dakon zaman jiranta cike da buri da fatan jin daddadan labari suka taso
”yaya nene?,anyi nasara kuwa?,rashin ganin nashi nada nasaba da aikin mu kuwa?”saida ta fada jabar saman kujera kafin tace
”mun sake fadu wannan karon ma babu nasara,rashin nasarar kuma yafi na kowanne lokaci”
adnan ya sake matsowa gabanta
”yaci dinne bai mutu ba?”
”ina ma yakai ga cin,ai ko ci baiyi ba,kuma hakan baya rasa nasaba da wannan tsinanniyar mai girkin da na rasa inda bintu ta samota,yarinya sai shegen kwarjini”
”oh shit!”adnan ya fada bayan ya dunqule hannunshi ya daki tafin hannunsa,zahariyta kuwa kasa magana tayi face bin sahun uwarta da tayi ta fada saman kujera
a sukwane ya koma shina ya zauna bayan yayi qasa da muryarshi
”nene,nifa na gaji da wannan shirin kisan ta bayan fage,ki barni kawai na tari abdallah na kasheshi da hannuna”
”kai dalla gafara can”nene tayi hanzarin katseshi
”ashe baka da hankali?,waye ya gyamaka kashe mutum kamar abdalla abune da yaje da sauqi har haka?,ka manta matsayinshi?,ka manta wayeshi a nijeria,bama haka ba,ka mance qirar qarfin da abdallah ke da ita,wanda na tabbatar idan aka barka da shi naushi daya zai maka saidai mu dauki gawarka ba kai din ba”shiru adnan din yayi don yasan haka maganar maman tashi take
zahariyya ta furzar da wani rin huci
”tsinanne matsiyaci,ni da zai amince ya auri waccar yarinyar zubaida ai da kinga komai yazo mana da sauqi,mu kasheahi hankali kwance,idan da rabo ma har sai ta haihu kinga tuwo namu miya ma tamu,to amma shegen girman kai da jin ajinsa bazai barshi yaso zubaida ba,to amma nene mai zai hana mu nemi hadin akn ita kukun tashi ko zata amince kamar yadda na baya suka amince,idan yaso itama musa a mata daurin baki idan ta amshi kwangilar ta yadda koda lamari ya baci zata gaza ambato sunansu kamar wadancan kukun”
ajiyar zuciya nenen ta saki
”hmmm,yaro yaro ne,duka tunaninku babu wanda ya kwanta min,wannan yarinyar tasha banban da wadancan kukun nasu na baya kallo daya na mata jiki na ya gaya min haka,abunda zai faru shine ni da kaina nake so ku bani lokaci zanyi tunanin mafita,na rantse da Allah wannan karon ko bata hanyar guba ba SAI NA SALWANTAR DA ABDALLAH
TOH FA????
????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:52 PM] 80k: ABADAN
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
daga abu hurairah yardar Allah ta qara tabbata a gareshi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace:ba zaku shiga aljanna ba har sai kunyi imani,ba zakuyi imani ba har sai kunso junanku,shin bana nuna muku abunda idan kuna aikatashi zaku so junanku ba?KU YADA SALLAMA A TSAKANINKU
cikin kwana ukun mami ta hana gidan sakat da shirye shiryen tarbar abida,ragowar daki biyun dake maqotaka da nata aka bude,kusan komai irin na nata dakin ne sai dan bambancin abunda ba’a rasa ba,ganin yadda mamin ta dauki zuwan abida da muhimmanci ya sanya maryam itama sake shirya kitchen
Ranar da zata iso din jirgin da yake sauka sha biyu na rana ne zai sauka da ita,tana jin mami na sanar da abdallah ya,haqura da fitar yau yaje a taro abidan da shi
”kai mami barta kawai,fita ta ta yau mai muhimmanci ce,driver yaje kawai ya daukota,ba dai tana gidan ba almost two to three months fa zatayi tare da mu”
qarfe sha daya maryam ta gama kintsa dining da kalolin abincin nijeria africa da kuma qasar da abidan ta baro wato turkiya,dakinta ta shige tayi wanka,don aikin bai barta tayi wankan ba,riga da zani ta zaba ta shirya cikinsu dukkansu normal dinki ne irin na riga da zani plain na asali,ba qaramin fidda sigarta yayi ba yanayin dakin akwai fidda shape din mu ba irin dinkin mu na yanzu ba mai tattara dake cika mace ya badda shape dinki,bata fito a dakin ba sai da ta jiyo surutu sama sama cikim parlour din mami qarfe daya saura kwata na rana
mutum uku ne cikin parlour din harda mami ta hudu,tashin farko zuciyarta ta bada abida cikin su ukun,sanye take da doguwar riga baqa mai azabar kyau da tsada irin mai robar nan dake bin jikin mutum,fara ce qal don har tafi maryam fari duk da dai akwai bambanci,farinta mai dau ne babu sirkin ja aciki ko kadan,zaka iya kiranta gajeriya don bata cika tsawo ba,tana da kyau kam ba laifi don kallon farko zaka kirata kyakkyawa,bata da qiba da yawa saidai jikinta acike yake babu lobawar rama
mami ce ta soma ganinta fitowarta
”yauwa maryam kin fito?”
”eh mami na fito baqin sun qaraso,sannunku da zuwa”
ta fada tana dubansu,daya ce kadai ta amsa sabanin biyun ciki harda abidar wadda ta dago kai ta dubeta,kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace
”nidai kam ba baqiwa bace ina tsammanin kece baquwar”
murmusho maryam din ta danyi
”eh to,kusan haka dinne”ta bata amsa tana kallon fuskarta wanda take bisa screen din tsadaddar wayarta
”maryam kuje da ita ki nuna mata dakinta”
”to mami”ta fadi tana yin gaba
”wa zai daukar miki trolly din?”abida ta ce tana hakimce a zaune tamkar ba ita za’a nunawa dakin ba
bata ce komai ba ta dawo,ta dubi akwatinan da kallo,qwaya biyu ne masu azabar kyau wanda ko ba’a fadi maka ba kasan cewa ba na talaka bane,ta daga dogon sandan dake jikin akwatin wanda zai bata damar janshi akan tayoyinshi ta kwantar da ita ta jata zuwa ciki
ta sake dawowa don daukar dayar,saura mami da abidar kawai yanzun cikin falon still abidan na hakimce,nuni ta mata da handbag dinta big mama tace
”shigarmin da wannan ma”
”barshi,maryam bari baba uwani tazo zata shigar miki da su,aikin maryam a gidan nan girki ne kawai”mami tace da abida,sai ta bar abinda take yi din ta dubi maryam sannan ta dubi mami
”ok,ai duka daya ne mami,dan aiki dan aiki ne da mai girki da mai shara duka ‘yan aiki ne”
”to kam anan gidan akwai banbanci,kowa matsayinshi daban”
dan tabe baki tayi sannan ta saki murmushi kana ta canza topic din
”gaskiya mami abdallah bai kyauta min ba,yaushe rabona da nijeria ammayau kawai ya gaza kashe aikin gabansa yaje ya dauko ni”
”kinsan dai halin abdallah sarai tun ba yau ba,aikinshi na da muhimmanci matuqa a gunshi,ba dan qaramin abu bane zai sanya shi qin fita aiki ranakun ayyuka ba”
maryam dake tsaye tana jiran tasowar abida duk ta qosa,ta dan gyara tsaiwarta
”mu qarasa na nuna miki dakin”
”jeki kawai gidan ba baqona bane”
bata kuma tanka ta ba tayi komawarta daki,saida da ta dqidaici lokacin da ya kamata tayi serving nasu sannan ta fito,saita taddasu tuni sunyi nisa da fara cin abincin,son haka ta qarsa ficewa daga bangaren gaba daya,boys quaters ta zagaya inda anan gidan baba uwani yake
da fara’a ta tarbeta
”maraba da maryamu,sai yau Allah yayi za’a zo mana”murmushi tayi har fararen jerarrun haqwaranta suka bayyana
ta gaida baba uwanin da baquwar da ta taras tayi
hirarsu suka sha sosai don bata baro bangaren ba sai da akayi sallar isha’i sukaci tuwon dawar da baban ta girka,don dama tana kewarsa matsalar su mutanen cikin gidan basa cinsa shi yasa ma bata girkashi
ita daya ta taho iskar damuna na kadata,cikin parking space ta jiyo motsi,ta dan juya kadan hisham ne abokin abdallah,a tunaninta basu ganta ba don haka ta kau da kai tayi gaba
”haba ‘yan mata irin wannan shan qamshi haka?,a qalla dai ai ko gaisawa kya tsaya muyi ko?,duk da cewa ma zuwan don ke nayi shi”inji hisham wanda ya sha gabanta,qirjnta ne ya shiga dukan uku uku,fatan ta kada Allah yasa ya furta mata kalmar so,don ita tsoro ma take bata,ta jita daga bakunan maza da yawa saidai babu abunda ta tsinana mata
a qagauce ta ce masa
”ina wuni”
”lafiya qalau maryam diya na ya gida ya aiki?”
kai ta dago ta kalleshi jin ya ambaceta da sunan da schoolmate da classmate dinta zuwa friends ke kiranta da shi
”lafiya qalau,ina son ganinki amma bari idan mun gama da abdallah zan kiraki,da fatan ba zaki qi zuwa ba”
”Allah ya bani iko”ta fada da gaggawa tana wucewa don ganin abdallah na isowa gurin
duk da haka bata kasa jin abunda yake fada ba kasancewar sun biyota ne a baya
”hisham,wlh hisham ka fita a ido na,kai me yasa baka jin shawara sai shegen taurin kai?”dariya ya qyalqyale da ita
”kai kuma mai yasa kake da girman kai da kafiya,Allah bai haramtamin harinya ba na gani inaso to kuwa ba zaka hanani ba”
”ok haka kace?”ya fadi cikin huci yana dubanshi
”yes,haka nace,idan kuma kai ke sonta ai sai ka fada sai in janye maka”
a zafafe ya soma fadin
”na rantse hisham zaka jawo mu samu sabani mai girma da kai,in rasa inda zanyi ajiyar soyayyata sai gun house girl kuku?,ina da dukiyar da zata iya bani duk kalar macen da nake so na aura,ko ‘yar wane kuma ko awanne qasa take,wanda nake tare da shi ma yafi qarfin auran house girl,indai ko zaka ci gaba kan qudirinka ka tabbatar cewa yana daidai ne da datse igiyar abotarmu”yayi gaba cikin hanzari abunka da qaqqarfan mutum
ko cikin parlour din ma dambarwar da suka dinga yi kenan sai da mami ta shiga maganar
”hisham ka qyale rigimar abdallah,maruam ta cika macen da za’a so,tana da dukkan halaye managarta,uwa uba kyau,don haka babu hujjar da abdalla yake da ita da zai hanaka neman maryama,ni na goyi bayanka saidai idan ita tace bata so”
”toh…nima haka na gani mami,nace masa ya fada idan yana so ne shima sai….”
”dakata hisham,don ina nema maka hanya mai bullewa kake cimin fuska?,to kayi na farko kayi na qarshe,duk lokacin da ka sake cewa inasn waccar abar wallahi sai na fasa bakinka”
ba hisham ba hatta mami abun ya bata dariya,abdallah mai rikicin gangan inji hisham,a haka abida tq fito ta taddaau,wannan karon ma cikin shigar doguwar riga take mai sulbi saidai armless ce,a mutunce suka gaisa da hisham don sunsan juna,ta juya ga abdallah
”soulmate,me yasa kamin haka don Allah,na diro naija da daukin ganinka sai kuna kayi tafiyarka aiki sai yanzu zan ganka?”
”da kika ganni yanzun ma ki godewa Allah,a tsare gobe ne haduwarmu,haka ne?”da sauri hisham ya shiga maganar ganin abdallah nason qarawa kwabar ruwa
”shareshi don Allah,kanshi ne ke hayaqi tun dazun”
tuni abida ta rudevta dawo kukerar da abdallan ke kai tana tambayar wa ya taba mata ruhinta,tsam mami ta miqe ta basu guri,banza ya bawa ajiyarta don haka kawai yake jin ransa na zafi
”wlh abdallah nan naki rigimamme ne sai kinyi da gaske,haka kawai ya haqiqance wai bazan auri maryam ba?”
”wace maryam?”ta tambaya tana duban abdallah
”mai shirya masa abinci kullum yana dirkewa”
ido ta,zubawa abdallan,lokaci guda wani kishin maruam din ya dirar mata,take taji ta tsaneta
”amma soul mate mene hujjarka na hana hi….”
a fusace ya miqe
”ke dakata min,kinsan banson titsiye ko?”yaja tsaki ya juya zai fice a sashen
kuka abida ta saki,wannan wane irin jaraba ce,daga dirarta a qasar ko kwana batayo ba abdallah ya aona bata mata rai,lallai abunda kake so shike wahalar da kai
kukanta bai dameshi ba ya juya ya fice,da sauri hisham yace
”kiyi haquri bari,na sameahi ranshi ne a bace”cikin hanzari ya bi bayanshi
amma da yake gwanin sauri ne tuni ya miqe balcony yayi sashensa
bai damu da hade girar sama da ta qasa da ya sakeyi ba duk don kada ya masa qorafin abunda ya yiwa abida ya hau masa fada tare da cewa yaje ya lallasheta
”wa?,ni?Allah ya tsareni,bani da lokacin lallaahin mace wallahi,ruwanta ta ci gaba da sona ruwanta tace ta haqura,amma babu lokacin rarrashin mace a rayuwata indai ba mahaifiyata ba”
karab cikin kunnen maryamu dake kwance saman gadonta don sun iso saitin window dinta,miqewa tayi ta zauna saman gadon,wani irin haushi da tsanar abdallah suka kamata
wanne irin nau’in mitum ne shi?
taqama da gadararsa sunyi yawa,dukiya?ita ke rudarshi ko kyawun da yake da shi?,haushi da takaici suka kamata tamkar da ita suke maganar,haushinsa ta dinga ji sosai,da tana da iko sai ta masa dukan tsiya ko zata samu sauqin abunda take ji
haushinsu abida ya kuma kamata
don me suna mata da Allah ya yiwa baiwa da ado da kunya su dinga watsi da baiwar,so hauka ne?,ta godewa Allah da bai dora mata wannan masifar ba,gwara da Allah ya bar zuciyarta wankakkiya kuma kubutacciya daga dukkan soyayyar wani
kusan awanni biyu da shigewarsu mami ta turo qofar dakin ta shigo fuskarta qunshe da murmushi
”maryamu diyata,jeki harabar gida hisham abokin abdallah na son magana da ke,duk abinda ya tambayeki kada kiyo nauyin baki ki sanar masa da gaskiya kinji ko?”
ba zata iya musu da mamin ba tilas ta amsa da to sannan ta fito
yana jingine jikin motarshi ta isa gareshi,da fara’arsa yake fadin
”barka da isowa,tun dazun nake jira har ma na fidda rai?”
”uhmmmm”kadai ta iya cewa taja bakinta tayi shiru tana sauraren bayanan hisham,ya rufe da fadin
”ina son inji gaskiyar abunda yake ranki”
tayi shiru kamar ba zata ce komai ba,bata jin ko dis a ranta zata iya hada dangatar aure da duk wani abu da ya shafi abdalla, MUTUNCI shi take nemawa kanta, DARAJARTA itace mafi muhimmanci fiye da komai a gurinta,har sai da hisham ya sake maimaita tambayarshi
”ya hisham na gode da mutuntawa da karramawar da kamin har ka furta kana sona,saidai ina mai baka haquri tare da addu’ar Allah ya baka wadda ta fini komai da komai,amma bani da ra’ayin soyayya,kayi haquri idan hakan ya bata maka rai”
shiru yayi na wani dan lokaci da alamu baiji dadin,amsar da ya samu daga gareta ba
”babu komai maryam,ita dama harka ta soyayya babu batuntilas,na gode nima da yadda kika mutuntani,amma ina nan ina jira har zuwa lokacin da kika ji jin aminta da soyayya”
murmushin yaqe tayi,ita kadai tasan me take ji cikin zuciyarya,wani irin qunci take mata,kyautar dubu goma hisham din yayi mata,da ta doje tace bazata amsa ba yace shina kam yayi niyya bai fasawa,dolenta ta amsa ta masa godiya sanna ta juya don komawa ciki
tuni an kashe qwayayen waiting parlour babu haske sai wanda ke fitowa daga sashen mami da nene,tazo tsakiyar parlour din taji an fincikota baya,razana tayi matuqa,tuni idanunta suka fito wajevta bude bakinta da niyyar qwalla qara saidai bata samu damar hakan ba,sakamakon hadata da bango da kayi aka saka wani lallausan tafin hannu aka danne bakin nata,qamshin daddadan turare ya mamaye hancinta,qirjinta ya shiga dagawa da sauka numfashinta ya soma tsere,minti kusan daya sannan taga haske kadan ya bayyana atsakninsu ,haaken screen ne na waya,fuskarsa ta fara gani abdallah ne,sanye da t.shirt fara sol cotting mai gajeren hannu wadda ta fito da murdadden damtsensa,kauda da qwayar idanunta tayi ta daina kallon fuskarshi sakamakon yadda take babu alamun rahama ko kadan a cikinta
murya a kausashe kuma qasa qasa yake fadin
”kin taimaki kanki da baki amsa masa kina sonshi ba,wallahi koda wasa kika amsa kina son wani da ya jibanceni kin shiga uku,baki kai ajin da zaki shiga rayuwar abokan huldata ba,ki qara gaba zaki iya samun wanda ke muradinki acan wata rayuwar ba tamu ba,bana aon cusa kai cikin lamura na da katsa landan tun ba yau ba na gaya miki,ki kiyaye don samun zaman lafiyarki da ci gaba da aikinki cikin gidan nan”
kamar jira ake ya kammala maganarshi haske ya mamaye falon,jdanun zubaida suka sauka kansu yayin da nashi idanu suka sauka kan fuskarta da hawaye ya aoma gangarowa,wani abu ne ya riqe mata maqogaro wanda koda an bata damar maida masa martani ba zata iya ba alokacin,saboda baqincikin da ta hadiya ba kadan bane,tsanarsa da tsanar halayensa uka sake linkuwa cikin zuciyarta
”kai din banza,abokan mu’amalar taka ma din banza,baka isa maryama ta soka ba,saboda daraja mutunci da karamci take bida ba tarin dukiya ko kyau ba”abunda take ta son ta amayar masa kenan saidai abundaya tokare tan ya hanata fada
cikin zafi baqinciki da kishi zubaida ta iso gabansu
”abdallah”abunda ta iya ambata kenan cikin karyar da kai hawaye ya soma mata zirya,sam bai damu da ganinta agun ba,duba daya ya mata ya maida idobsa kan maruam ya cire hanunshi yana jan tsaki,ya ja mayafinta ya goge hawayen ta da ya soma taba masa hannu
”indai bakiji abunda na gaya miki ba yanzu kika fara kuka”ya kewayeta da,zafinsa ya fice asashen,ita dinma gyalenta ta ja kawai ta shige sashen nasu,abida ce kawaia falo da tayi zaman kallo tana kuma dakon dawowar abdallah don yace ta zauna ta jira shi batasan gatse ya mata ba lokacin baccinshi yayi,dakinta ta wuce ta danna qofar ta rufe kana ta saki kuka,me tayi masa?,ita tace tana son hisham ne ko kuwa,ahikeban talaka ba komai bane agun wasu masu kudin,talaka bai cika mugum ba,ko talaka baisan ciwon kanshi ba,taqamarshi ta isheta,tana jingidansu zata bar masa shi yafi mata sauqi,ga fargabar yanayin gidansu ga taqama da gadararshi da wanne zata ji?
mrs muhammad ce
[9/17, 12:52 PM] 80k: ABADAN
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Daga abu hurairah yarda Allah ta qara tabbata a gareshi yace:manzan Allah s.a.w yace:yana daga cikin kyawun musuluncin mutum,ya bar abunda babu ruwansa
a wani hadisin kuma manzan Allah s.a.w yana cewa:jibrilu bai gushe ba yana min wasiyya da maqoci,har sai da nayi tsammanin/zaton maqoci zai iya gadon maqocinshi(saboda girman haqqin dake kan maqoci akan maqocinsa)
washegari a makare ta tashi saboda rashin baccin kirki,kitchen ta shiga ta shirya musu breakfast,adana kebabi,tavouk koftesi a abincin turkia sairuwan shayi chips da soyayyen qwai,cikin lkkaci qanqani gidan y game da qamshi,bata bar kit hen din ba baba uwani ta shigo
”af,makara kikayi ne yau maryamu”murmushi tayi tace ”wlh kuwa baba uwani”
gaisawa sukayi sannan ta bar mata kitchen din ta koma dakin
sha biyu na rana ta fito tayi sarving nasu mami ce da abida,cikin mamaki abida ke cin abincin tana tantamar yinsa akayi ko restaurant aka je aka siyo?,abincin yan turkey a nijeria,kusan ma har yafi nasun dadi sakamakon banancin spices da muke da shi
so take ta sanarwa mami qudirinta na barin gidan saidai ta gaza,nauyinta take ji sosai,alkhairan mamin a gurinta na da yawa,da haka har suka kammala cin abincin ba tare da ta ce mata komai ba
kafin ta bar gurin mamin le sanar da ita gyaran gida da canza kayayyakin da suke duk shekara idan ya rage saura kwanaki bakwai azumi
”akwai ma’aikatan dake,zuwa,suna aikin nan da jibi zaki gansu,abunda kawai nake so kimin alfarmarshi shine zaku shiga kasuwa kiyo soyayyar kitchen dukkan abunda ya kamata wanda za’a buqaceshi”
ta dan saki murmushi”diuarki ce ni mami kamar yadda kike fadi,ba alfarma bace umarni zaki bani kawai na bi”
”na gode diyata Allah yayi miki albarka”
wanna halaye na mamin na daya daga cikin abinda ke sata sake jinta cikin zuciyarta
koda ta kammala abincin dare,sashen ta sake bari,gurin baba uwani ta kuma wuni,kiran wayarta da mami tayi da daddare shi ya fiddota ziwa,sashen mamin,a hanya suka ci karo da zahariyya na shirin fita cikin motarta,wani kallo ta jefi maryam din da shi wanda ya tilasta maryam neman tsari da ita
cikin shirin fita ta samu mamin
”maryam yau kwanan asibiti zanyi bazan dawo ba sai gobe idan Allah ya kaimu,ga gidan nan na barshi hannunki”
”to mami”ta fada tana amsar jakar hannunta don yima mamin rakiya zuwa motarta
daidai lokacin abida ta fito sanye da riga da wando,kunnenta maqale da earpiece
”mami ina zuwa?”
”af,na mamce kina cikin gidan”
hara rar maryam abida tayi
”mamee kika manta da ni amma wannan ki kasa mantawa,da ita”bata lura da hararar da take ma maryam din ba tayi dariya
”to ai kece din sarkin kwanciya,klum kina kwance a gado kamar ruwa,zan tafi asibiti ne ina kuma tsammanin kwana zanyi”
”q’nnnn,si kin dawo”ta fadi tana kwanciya saman doguwar kujera yayin da suka fice ita da maryamu
mami na shirin shiga motar taga shigowar abdallah gidan,hakan ya sanya ta dakata har ya iso inda suke ta sanar mishi fitarta ta dora da
”am….abdallah,inason in ganka daman”
”to mami ai gani”
janye jikinta maryam tayi ta koma gefe don basu damar ganawa,daidai duk da hakan tana jiyo abunda mamin ke cewa
”har yanzu banga alamun jituwa tsakaninka da bida ba abdallah me yake faruwa?”
”mami ba komai kawai dai rawan kanta ne yake bani haushi,azarbabi rashin aji da kamun kai,kuma ma ban samu zama bane kinga soaai,kwana biyin cases sun mana yawa a office,bainciken wadanda suka saci kudin talakawa”
”duka naji,saidai inaso ka ajjiye dukka wani uzirinka,ka tabbata kun fahimci juna kai da ita,maganar halayenta kuwa kana da damar canza ta tunda tana sonka,ya kamata ace i yanzu ka ajjiye iyali,don nima ina da buqatar ganin qana nan yara suna gilmawa,ina fata ka fahimceni da kyau abdallah?”
”na fahimta mami,saidai koda jikokin sunzo ta yaya wadan nan patient,naki zasu barki ki sake da family dinki,suna qwace min ke kina kwanan office”ya qarashe maganar cikin sigar zolaya
murmushi tayi don ta san dama sai yayi qorafi,haka take fama da shi duk lokacin da zata kwanan asibiti
‘?idan na biye maka abdallah sai ka makarar da ni”ta dan daga murya kadan ta kira maryama,cikin nutsatstsen takunta ta iso,gidan baya mamin ta shige sannab maryama ta miqa mata jakar tana cewa
”a dawo lafiya mami”
”Allah yasa maryama,a kula da gida”
”insha Alahu mami Allah ya bada sa’a”
mamin ta juya ga abdallah dake tsaye yana jinsu,hannayenshi harde saman qirjinshi,har ga Allah yaji dadin yadda ta nuna caring wa mahaifiyarshi
”abdallah sai na dawo,banda tsokane tsokane?”mami ta fada tana dariya
”mami sai kace yaron goye,zaki jawo a raina abdallahnki fa”ya fada yana shigeqa ahima gidan bayan
”a’ah,ya haka?”ta tambayeshi
”zanje na rakaki ne mami”
”yabzun fa kaima ka dawo daga aiki,na uafe ka shiga ciki ka huta,abida na parlour tana jiranka”
”idan ina tare da mami mancewa nake da duk wata mace,a naje asibitin naja masu kunne duk wansa ya barki kikayi aiki duka dare baki runtsa ba ni da shi ne,driver muje”haka drivan yaja sauran securitu dinshi suka dafa musu baya maryam ta dawo cikin gida tana jiniina yawan qaunar dake tsakanin mamin da abdallah
a inda ta bar abida anan ta taras da ita,bata tanka mata ba,tana gab da shiga dakinta taji tace
”ke zonan,”tayi kamar ba zata kula ta ba don ta tsani irin wannan kiran sai kuma taga baquwar mami ce ko ba komai taci darajarta
”wai me kika dafawa mutane?”kafin ta kai ga bata amsa kuma sai taji tace
”jeki kawai,sai abdallah soulmate ya iso kyazo kiyi serving namu”
ta gama shirin kwanciyarta tsaf ta tuna ta manta da littafin addu’o’inta cikin kitchen,hijabinta ta zura ta fito don ta dauko
abdallah ne cikin falon gefanshi abida ce zaune ta sanya ahi a gaba tamkar zasu hade,magana auke qasa,qasa,son bata iya jiyo me suke cewa,tayi kamar ta koma sai kuma ta fasa tayi ahigewarta kitchen,tana qoqarin komawa taji tace
”ke zokiyi serving mutane,kin shige daki kin zauna sai kace baki san aikinki ba”
bata tanka mata ba sai da suka isa teburin,a sanyaye cikin jerartun maganganunta masu cike da nutsuwa
”idan baki sani ba sunana maryam don Allah ba ke ba,aiki kuma ba naki aka umarceni da inyi ba,ba don ke nazo gidan nan ba,so please don Allah mu girmama juna,tunda dukkanin mu ‘yan adam ne,halitta mai qima da daraja agun Allah”
”naqi na kirakin da hakan,kuma ni ba sa’arki bace kada ki kuma hada kanki da ni,ki dubeni ki dubeki mana,tundaga sutura ai kinsan da banbanci,kada ki kuma gigin hada kanki da ni”
shiru tayi mata domin ta fuskanci abidan tayi nisa,gwana ce itama gun girman kai,amma bata jin zata iya jurewa shararta ba sam,da iliminta itama da shekarunta,ba jahila bace bare tace zata dinga shiga gonarta tayi mata kashi ta qyaleta,ta kammala zuba musu tuwon semo miyar kubewa danya sai farfeaun kan rago a plate daban,a yatsine abida ke duban abincin
”meye kuma wannan?”tayi tambayar tana duban maryam,banza tayi mata tamkar bata jita ba,don,kanta da ta gaji da shirun tace
”ni wlh soulmate bazan ci wanna abun ba,na manta wanne lokaci ne na qarshe,da na cishi,kinga malama ki ahiga kitchen ki dafa min wani abun”
”awoyin shiga kitchen dina na yau sun qare,amma babu damuwa idan zaki iya jira zuwa gobe”
daga haka ta miqe tabar musu teburin,ahi kansa abdallah dan binta yayi da kallo ganin yadda yai take maida raddi babi kinkiri,fana iya jiyo ihun abida na zage,zage da hausa mixs da,harshen nasara wani lokaci harda turkanci
”oh god,pls don Allah ki yiwa maqogoronki afuwa,baki gajiya da fada?”abdallah ya fada bayan ya tallafe kumatunta ya sanya zazzafar qwayar idanunshi cikin tata,laqwas jikinta yayi,farinciki ya maye gurbin bacin ranta,tuni ta sanya hannu ta aoma kwasar tuwon sai gashi qarshe ta bige da santi
ta cusa kanta cikin pillow ta sake rubtse idanunta akaro na barkatai,har yanzun dai bata daina jiyo tashin hayaniyar ba daga dakin abida
muryar abida ce wani lokaci data abdallah,kuka take tun kusan rabin awa das,uka shuhe,sun hanat a bacci,ta kuma gaza fahimtar meke faruwa
”wallahi abdallah ko baka aureni ba indai ka kwanta da ni burina na duniya ya gama cika,don Allah abdallah ka amince wallahi zan iya rasa raina ayau idan ban samu cikar muradina ba,muna da dama abdallah muna da lokaci isashahe,mami bata nan daga ni sai kai kawi abdallah,pls ka taimaka min”
mamaki baqinciki da takaici suka sake cikashi,gumi ya kuma karyo masa,kimanin awanni biyu yana fama ta rabu da shi amma ta qiya,tun yana lalashinta yana qoqarin fahimtar da ita har ta soma bashi haushi,da ya miqe ta yago shi,har ta rabaahi davtshirt din jikinshi sai singlate kamar tsohuwar mayya,bayason gwada mata qarfi ne amma ya fuskanci sai ya biyo,mata ta hakan
cikin zafin nama ya miqe ta sake yunqurin kamoshi,tuni ya watsar da ita ya fice kana ya maida maqulli ya rufe dakin,dai dai da fitowar maryam kenan wadda tayi niyyar barin dakin nata ta canza makwanci sakamakon hayaniyar da ta hanata sakat tasu
a tsorace ta dubeshi idanunta cikin nashi,ganinshi a jargitse ga sautin kukan abida dake fitowa cikin dakin da ya kulleta,sai ta dan ja baya kadan zuciyarta ta soma harbawa,shi din ma ita yake kallo
mrs muhammad ce
[9/17, 12:52 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
???? ▶2⃣7⃣