ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

ubangiji madaukakin sarki yakanyi duba izuwa filin arfa,sai yace da mala’ika jibrilu,me bayin nan nawa suke nema haka(duk da cewa shine mafi sani),sun fito cikin tsananin zafin rana da qasqantar da kai?,sai mala’ika jibrilu yace”rahamarka da gafararka,sai ubangiji yace na gafarta musu”
haka ubangiji s.w.a yake rabon irin wanna garabasar a filin idi,annabi muhammad s.a.w yana cewa”kada ku hana bayin Allah mata zuwa masallaci”
sannan yayi umarni da a fita sallar idi maza da mata yara da tsofaffi
yake ‘yar uwa,kada ki bari wanann garabasa ta wuceki wadda baki da tabbas din ganin wata kamarta,Allah yasa mu dace,ya yafe mana kurakuranmu,yasa mu cikin bayinsa da za’a gafatarwa Allahumma ameen

wannan shafin sadaukarwa ne ga dukkanin al’ummar musulmi,Allah ya karbi ibadunmu

ci gaba yayi da lallonta kamar yadda take kallonshi,tuni oily eyes dinta suka qara sheqi da sakamakon tsoro da qwalla da ta tarar mata,zuciyarta na raya mata mummunan abu abdallah ya yiwa abida,cikin hanzadi ta juya da nufin komawa dakinta ta banke saidai taku daya biyu ana ukun ya cafkota ya maidota baya,take jikinta ya soma bari,bakinta na rawa ta soma fadin
”don…..d….don Allah kayi haquri,ka fufamin asiri”

galala yake binta da kallo,tuni ya gano manufarta,ganin taqi nutsuwa ya sanyashi daka mata tsawa
”me zayi dake da har kike tsammanin wani abu zan miki?,koyin ma zanyi kin min kadan ‘yar tsakuwa,abinda nakeso dake kada ki kuskura wani yaji abinsa kika gani?,ina fatan kin fajimceni?”
kai kawai take gyadawa babu qaqqautawa,burinta kawai ya saketa ta samu ta tsere,yana sakin nata kuwa ta shige dakin jiki na rawa ta murza key

binta yayi da kallo cikin mamkin mummunar fassarar da tayi masa tashi guda,koda ya koma daki sai yaji abun ya tsaye masa a rai,ta tuhumeshi da laifin da bai taba sha’awar aikatawa ba,hasalima ya tsani mai aikata shi,gefe guda kuma tsanar abida ce fal cikin zuciyarshi,yaci alwashin koda zata rasa rayuwarta bazai iya aurenta ba,yana da tsananin kishi ya tabbatar koa ya aureta din bazaya samu kwanciyar hankali ba

????????????????????????

kusan dukkaninsu kwanan zaune sukayi babu wanda ya runtsa,kowa da abunda ke yawo cikin rai da zuciyarshi,duk da hakan maryam bata kasa tashi yadda ta saba ba ta hada breakfast,saidai babu wanda yaci,bata san da hakan ba sai da mami ta dawo ta hau sama ta kintsa kana ta sake dawowa qasa don yin karin safe,abida qunar zuciya ta hanata fitowa,abdallah yayi sammakon zuwa ofgice saboda wani taron gaggawa da zasuyo wanda shi kansa bai san da shi ba sai da asubahin ranar his excellency mr presdent ya sanar mishi,saboda haka kiegin qarfe shida yabi zuwa abuja

maryama kuwa tsoro da fargabar haduwa da abdallan ne ya hanata fitowa bayan ta samu ta kammala aikin ba tare da sun hadu ba
”shi kam abdallah ai ya jima yanzun a abuja,jeki kiramin abidar dai ta karya,ya zatayita zama bata ci komai ba”
kamar tace da mami ba zata iya zuwa ba don tana fargabar halin da zata je ta taradda abidar,bata da amsar tambayar da mami zata yi mata game da abunda zata ga ya samu abidan

ba zata iya qin zuwan ba don haka ta miqe jiki a sanyaye ta nufi dakin,sai da tayi knocking sau biyar kafin a bada izinin shiga cikin qaqqarfa kuma kausa sashiyar muryar abidar
ga mamakinta sai ta tadda abidar ta fito daga wanka ras da ita,babu wasu alamu dake nuna wani mummunan abu ya faru da ita
”meye kika tsaya kikatsaya kika zuba min idanun kin nan masu zubi da na mage?”
sai a lokacin ta ankara da tsayawa tayi kallon abidar
”mami ke kiranki”tana jinta tana tambayarya ta dawo ne tayi mata banza ta wuce

da daren ranar ta sake shiga wani rudanin,a hanyarta ta dawowa daga sashen baba uwani zahariyya ta sha gabanta ,tace taje nene na kiranta

zaune take gaban nenen cikin falonta na can sama,daga ita sai nenen sai zahariyyar
”maryamu kike ko?,nasan zakiyi mamakin irin wannan kira na bazata,ba komai bane yasa na kira ki wata buqace da ni wadda nake neman taimakonki gurin cikarta,ina fata kuma zan samu hadin kanki gun cikar buri na”
”zan iya taimaka mikin indai bai kauce addini na na ba”
wata dariya nenen ta kece da ita
”idan banda quruciya irin taki ai yanzu kowa ma ba bin qa’idar addinin yake ba,biyan buqata kawai ake nema”nene ta sake qasa da murya kana ta kuma matsowa kusa da maryam
”ba wani abu nake nema agunki illa poising da nake buqata kawai ki diga a abincin abdullahi”
a firgice ta miqe har jiri na shirin kayar da ita lokacin da nenen ta gama zayyana mata buqatarta,bari kawai jikinta yake,addu’a duk wadda tazo bakinta yi take

halin da ta shiga kawai ya ishi nene amsa
”kinga zauna ki nutsu,sai kace wadda aka ce ta diga a abincin ubanta,aikin nan fa ba a kyauta zakimin ba,biyanki zanyi kudi masu yawa da nauyi,zan dauke miki dukkan wani quncin talauci da kike ciki,zan wadata ki zan yalwataki”

hawaye ne ya shiga bin kuncinta,girgiza kai kawai take cikin takaici
takaicin ha’intar managarciyar mace kamar mami
takaicin cin aman ada yaudara da sukewa mamin
takaicin son dasa baqincikin da qunci na har abada da mutanen keson dasawa a zuciyar mamin
wannan cin amana da me tayi kama?,haka mutanen duniya suke

”bazan iya ba,bazan iya cin amanar mami ba ko duniua da abunda yake cikinta zaki bani”abunda ta iya fada kenan ta juya a guje zata bar sashen
”ke,dakata”mamin ta tsaidata,har ta iso gabanta ta kasa motsawa,cikin huci take dubanta
”rashin karbar tayi na yarinya daidai yake da tangal tangal da rayuwarki,arziqi na binki tsiya ta hanaki ki ganewa,kije….ko babu ke sai na cika burina,hanyoyin nada yawa,amma ki tabbata rayuwarki na cikin hadari,kuma wallahil azeem kika bari maganar nan ta fita sai na batar dake”

a sukwane ta bar sashen,da qyar ta kai kanta dakinta cikin mawuyacin hali,fadar irin halin data tsinci kanta bata baki ne
tabbas ta kuma gasgata cewa nene na iya aiwatar da duk abinda ta fada din,ta gani,cikin qwayar idonta
mafita daya take hangowa a gareta shine ta nemi miji tayi aure,ba zata iya kallon qwayar idanun mami ba tace tabar aiki,wata fuskar tafi gaban mari,aure shine zai rabasu salin alin

dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki

ina taya daukacin al’ummar annabi murnar zagayowar babbar sallah da fatan za’a gudanar da bukukuwan sallah lafiya

insha Allahu daga yau zamu je hutun sallah,littafin abadan zaici gaba da izinin Allah bayan qare hidindimun sallah

subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la’ilaha illa anta,astagfiruka wa’a tubu ilaika

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????✍????
[9/17, 12:53 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
???? ▶2⃣8⃣

HASKE WRITERS ASSOCIATION????

wannan page din naku ne,wato mata iyayen gida,ku huce gajiyar sallah,Allah ya qara mana himma da lafiya,ya bamu ladan kula da iyali

material ne a jikinta mai baqi da fari,skert din baqine sol babu digon komai,rigar kuma fara ce mai adon baqaqen fulawoyi,irin dinkin nan ne da muke kira three quater iya gwiwa,skert din simple ne mai tsaga a baya,baqin mayafi ne tayi rolling da shi sai farin plate shoes mai igiya data sanya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button