ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

a kasalance take nunawa ma’aikatan irin kayan da suke so su kuma suna cirowa suna sanyawa cikin keken tura kayan,qarfin hali kawai take,batason nunawa mami wani abun na damunta,duk da tana jin kamar zazzabi na shirin kamata

sannu a hankali suka qurewa bangarwn electronics dake cikin makeken shagon zamanin nan na shoprite dake ado bayero mall,suka juya bangaren warmers da plates cups da sauransu,daya bayan daya take bi tana zaban sababbin design

”subhanallah”suka fadi a kusan tare suka kuma ja da baya,tuni cups din da ta dauko sukayi nasu guri a qasa sakamakon karon da sukayi,a tare suka duqa suka soma kwashewa

”kiyi haquri madam don Allah ban kula bane”ya fada yana miqa mata guda ukun da yayi nasarar kwashewa,sai a lokacin ta dubeshi,baqi ne ba can ba zaka iya kiranshi da chaculet,dogo ne maras qiba,ya mata kama sosai da mutanen qasar habasha ko kuma baqaqen fulani
”ba komai” ta fada tana amsar kofunan,kana ta rabeshi ta wuce

”ko am min izini na taya madam din zabar kayan duk da ba bangare na bane?”taji an fada daga bayanta,da sauri ta waigo mutumin dazun ne,tamkar tace a’a sai kuma taga babu buqatar ta fadi hakan
”bismillah”tace da shi
cikin hikima da dabara yake bayyana mata ko shi waye

”ni sunana abdur rahim tasi’u alhasan,ina zaune a unguwar qoqi dake tsakiyan birnin,ni dan kasuwa ne kamar yadda mahaifina yake,ina fata kin gamsu da dan taqaitaccen bayanin da na miki”ya qarashe magana lokacin da yake tura kwandon yana kuma kallon fuskarta
dan qaramin murmushi ne ya subuce mata
”to ni kuma meye nawa da sanin kai waye,daga taya ni siyayya?”

murmushin shima yayi bayan ya tsaida basket din
”ke kuwa kike da ruwa,saboda ina sa ran zamowarki uwar gida na,bazan boye miki ba tunda na ganki naji kin kwanta min,da gaske nake sonki maryamaurenki kuma nake so inyi anan kusa”
a mamakance take kallonshi,to ko addu’ar da ta kwana yi jiya ne Allah ya amshi roqonta?,babu shakka Alkah maji roqon bayinshi a kurkusa ko a nesa
”yaya akayi kasan sunana,bayan a iya sanina ban gaya maka ba baka kuma ji wani ya ambata ba?”
murmushi ya sakeyi
”maso dan tsuntsu shike binsq da jifa,sonki nake bada wasa ba hakan yasa nasan komai game dake kafin na iso gareki”

cikin wani mamakin ta kuma dubanshi
”kana nufin ba yau ka fara sani na ba?”
ya dage girarsa sama
”eh,kusan haka dinne”cike da mamakin shigowar abdur rahim cikin rayuwarta lokaci guda suka kammala dukkan siyayyrsu ita da abokan tafiyar tata,har lokacin abdur rahim din na biye da su hqr suka kammala,a bakin motarsu ya dubeta
”yaushe zanzo mu tattuna a nutse”ya tambayeta yana murmushi,dan jim tayi tana tunani a lokacin taji wayarta na ringin,da sauri ta cirota,ta duba,atsammaninta hindatu ce don tace zasuyi waya sai kuma taga baquwar number
”ga number dina nan kiyi serving zan kiraki naji lokacin da zanzo din”

da mamakin karona uku ta sake dubanshi,mamakin ina ya samu num dinta,kamar yasan me take tunani yace
”nasan mamkin inda na sami number dinki nake ko,kada ki manta na gaya miki dazu,na shigo sonki ne bada wasa ba hakan ya sanyani sanin komai game da ke tun kafin na iso gareki”murmushi ta sakar masa,sai taji abdur rahim din ya burgeta karo na farko,wannan wane irin so ne haka?

ko cikin motarma tunani abdur rahim din ta fada,tana gaya wa kanta ta samu mijin aure tabbas,tana kuma qarfafawa kanta gwiwar wannan karon zata shiga dakin aure kamar kowacce mace

bayan mami ta gama ganin kayan ta yaba sosai,don tace basu taba siyan kaya new fashioned and durable haka ba kamar wannan shekarar,kai tsaye dakinta ta wuce don tayi sallar la’asar su fara rage koda gyaran kitchen ne tunda taga da time,biyu daga cikin daki hudun dake rufe ta sake gani a bude,bata ce komai ba don ga tsammaninta baqi mamin ta sakeyi

da taimakon ma’aikatan harda baaba uwani cikin qanqanin lokaci suka fidda tsoffin kayan kitchen din suka fara shirya sababbi,aiki na yiwa maryam dadi sakamakon yadda yake tqfiya cikin tsari,sunayi kuna suna hiransu abinsu,kada ma baaba uwani taji labari,akwai abun dariya
”lamarinku na yaran zamani na bani mamaki”baba uwani ke fadawa maryam qasa qasa
”me mukayi baaba uwani?”maryam ta tambayeta tana fiddo da wani foodflask daga cikin kwalinshi
”mata su dinga biyo maza gida suna neman aurensu?”
”kamar yaya baaba?”
”hmmm,yaran nan mana dake son yaron gurin hajiya abdullahi,dazu daya yarinyar nan itama tazo da kayanta na satittika,ummm…….salamatu,mu a da ba sai an kaiki daki ba ma kike sanin waye mijin?,idan ma kuwa har kinsan waye shi din kafin a daura aurenku to ko hanyar da yabi baki iya bi saboda kunya,idan kuwa tsautsayi ysda kuka hada hanya to sai kinkusa qamewa a tsaye vaki iya motsi har sai ya wuce”

dariya ce ta kubcewa maryam
”baaba kin iya bata suna,salma ake cewa ba salamatu ba”
”kome me take ne barta,abun nasu sai addu’a,ko kunyar hajiya basa ji,ko fada ne ya kama yi suke a gabanta,abunda mu ko abinci baka iya ci gaban suruka,wannan zamani wannan zamani yazo qarshe,fatan Allah yasa mu gama lafiya”
”ameen”maryam din ta amsa mata da shi,daga haka bata ce komai ba,ita kanta mamaki take,saidai babu ruwanta don bata shiga shirgin da ba nata ba

ana kiran sallar magariba suka kammala aikin duk girman kitchen din yayi kyau ya sake haske,lallai sabon abu akwai kyau inji baaba uwani,ita kanta mamin ba qaramin mamaki tayi ba,ta sallami sauran ma’aikatan tana yabawa qoqarinsu

dakinta ta kuma komawa sanda tafito daga kitchen din abida ce zaune gaban makekiyar t.v plasma tana kallo sanye da matsattsun riga da wando,kusan duka shigarta kenan ta fidda tiraici ko doguwar riga zata sanya sai ta samu mai tighting jiki,wanka tayi ta sauya kayan jikinta,ta daura alwala tayi sallah,tana saman dadsuma tana lazumi ta tuna zata kira fa hindatu,ta laluba wayar bata jita ba hakan ya bata tabbacin ta manto ta a kitchen,ta gyara zaman ijabin jikinta ta fice ta nufi kitchen

su uku ta tadda yanzu a falon abida salma da abdallah da suka saka atsakiya,kallo daya zaka musu ka tabbatar daga abidan har salman ba jin dadin zaman suke ba,shi kuwa hakimin na tsakiya zaune yana ta aikin amsa waya,bisa dukan alamu wani aiki yake shiryawa don taji bada order din yayi yawa cikin fada da fushi

ilai kuwa cikin sabuwan kitchen wear din ta ganta,missed call goma ta taras,hudu na hindatu hudu na abdur rahim daya na raliya,murmushi tayi don dama ta sani bata da masu kiran nata sai su,sai ta rasa wanda zata soma kira a cikinsun,cikin haka kiran mami ya shigo
”kina ina ne maryamu,na shiga dakinki ban tadda ki ba”
”mami ina kitchen”
”baki gajiya ne maryam aiki sai kace inji,already baaba uwani tayi abinci ki huta haka nan don Allah”
tana jin dadin qaunar da mami ke nuna mata qwarai da gaske
”wayata na manta ma nazo in dauka”
”ok,ki sameni a parlour na”
”to”ta amsa mata ta cire wayar daga kunnenta ta fita daga kitchin din

”ke mero”taji an fada lokacin da take qoqarin hawa matattakalar benan
kamar kada ta juyo sai kuma ta waiwayo din don ganin mai mata kiran,abida ce
”meye kika tsatstsareni da idanuwankin nan kamar na?,shawarma nake sonci,ki shiga kitchen yanzun kimin idan kin iya”
rausayar da kai maryam tayi
”batun iyawa na dade da wuce babinshi,saidai lokacin aiki ya qare,zaki iya barwa gobw idan Allah ya kaimu,tunda majority utensils din duka sabbi ne bamu bude su ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button