ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

cikin izza isa da gadara tace
”ke,wai mai kike taqama da shi ne,ki fadi nawa ne albashinki duka a nunka miki bama iya kudin aikin yau ba,ban mance ba rannan haka kika mana wani abu tuwo sunanshi ko me?nace kimin wani kalar girkin kika ban banzan answear irin wannan,kinsan wace ni kuwa?”

sakin makarin silver din da maryam din ta riqe tayi ta juyo ga abidan sosai
”ni ba kowa bace kuma bana taqama da kowa face Allah,kudi kuma ba zaki bani yanke talauci ba har abada,matsayin da Allah ya ajjiyeni ya gamsar da ni sosai na kuma gode masa,gaskiyata na fada tsarin siki na kenan cikin gidan nan,baquwa ce ke ina zato shi yssa kike mantawa,sannan ke din ma ba kowa bace face baiwar ubangiji kamar yadda nike kowa kuma yake”

a hankali abdallah ya dago kanshi daga kallon wrestling a tashar mbc action da yake ya dubeta,sai yaji amsarta ta burgeshi,babu hayaniya cikin raddinta,cikin calmnesses and cool voice,sai ya dan tsaida abunda yake yaga yadda za’a qare
tuni fuskar abida ta canza,cikin bacin rai ta dubi abdallah
”mu sugar kana gani da jin abunda yarinyar nan ke gaya min ko”ta fadatana nuna maryam wadda tuni har ta kusa kaiwa qarshen benan

murmushi ya saki mai hade da yar dariya
”duk bakery din dake garin kano kin raina,kin rasa inda zaki ci shawarma ne?”
”zaka iya kaini ne?’
”a lissafin lukuta na babu wannan,idan kina so akwai direbobi sai wani daga ciki ya kaiki ya dauko”sai ta sake tunzura,ya yrfata gaban salma kenan?,abunda madyam din ta mata ya hadu da wanda abdallah ya mata ya zamar mata zafi biyu
a zafafe ta miqe tana cewa
”tunda kai bazaka iya daukan matakin komai ba to ni zan daukarwa kaina,bazan zauna talaka ‘yar talaka wulaqantacciya ta dinga taba mutuncina ba”

wani murmushin ya kuma saki ya kima kashingida
”eh kuma fa,gaskiyarki nima na goyi bayanki,kamarki diyar ambassador guda bai kamata a dinga samun iein haka ba,jeki dauki mataki”
sai ya kuma tunzurata don ta fuskanci kamar gatse yake mata ko kuma jirwaye mai kamar wanka,a haukace ta haye saman

kujera ta samu ta zauna tana fadin
”gani mami”
”yauwa maryam….cewa nayi”maganar mamin ta katse sakamon kiran da ya shigo wayar maryam din,screen din ta duba,sunan abdur rahim ya bayyana,sai ta maidata silent taqi dagawa
”ki daga mana maryamu”inji mami
murmushi tayi ta dan sadda kanta
”um um mami,ina jinki”
cikin murmushin da salon zolaya tace
”kodai suruki na ne maryam?”

sai kunya duk ta kamata tayi qasa da kanta tana murmushi
,ganin tayi shiru yasa mami cewa
”Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa,shawarata gareki ki riqe mutuncinki,ka kame kanki,mutuncin mace kunya da kamun kai,duk da nasan duka halayenki ne,idan na samu lokaci zan miki magana yazo inganshi mu gaisa”cikin jin dadi da gamsuwa da maganganun mamin take gyada kai,sai ta kuma tsokanarta
”bari nayi sauri na sallameki kada surukin nawa ya qosa da jirankin ko”sai ta sake bawa maryam din kunya

”kaya ne wadanda aka fitar da kayan firniture da za’a fitar gobe nake son ki zazzabi dukka abunda kike so ki kaiwa mamnki ko zatayi amfani da wasu wadanda bata so ta bada”
tayi mamakin yadda mamin ta bada kayqn,don kaya ne da babu abunda aukayi tamkar yau aka zuba su espicially kayan furniture din,ta wani fannin kuma ba abun mamaki bane saboda halayen mamin ne karamci da kyauta
sabanin wasu masu hannu da shunin da sun gwammace su saida kayan maimakon ‘yan uwanau su amfana furniture ne ko kayan sawa,ko me zasuyi da kudin oho,bayan Allah ya wadata su ya basu arziqin amma suna maida kansu baya

”na gode mami qwarai,Allah ya qara girma”
murmushi mamin tayi
”bakin maryamu ya saba da godiya,nasha fadi miki ba haka tsakani na da ke”
kafin tace wani abu an banko qofar an shigo,abida ce kanta tsaye ta tafi gurin mami
”mami,ki shiga tsakanina da house girl din nan,hala bata san koni wace ba,ta raina ni matuqa,wallahi idan bata kama kanta ba zanyi sanadiyyar qulle danginta kaf babu wanda ya isa ya fito da su,batasan ba’a raina ni ba,bana daukar raini?”
kama kai mami tayi tana kallon abida
”qara kika kawomin ko mataki kika zo dauka?”cikin rashin iya magana tace
”duka mami”
ta riga da tasan abida rainon tabara ce,ta san ita har zuciyarta magana ta fada mai kyau,ta bar ta tata ta juya ga maryam ta tambayeta mai ya faru,a nutse ta gaya mata
”tashi kije maryam,sai da safe Allah ya bamu alkahairi”
”ameen mami”ta fada tana ficewa,yunqurowa abida tayi gurin maryam mami ta dakatar da ita

mamaki ne ya ishi maryam,tana shiga daki kiran abdur rahim ya shigo wayarta,murmushi ta saki ta isa gefan gadonta ta zauna sannan ta daga

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????✍????
[9/17, 12:53 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
???? ▶2⃣9⃣

HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

Kimanin awanni biyu suka shafe kan layi ita da abdur rahim din,ta fuskanci ya dan san wasu abubuwa game da ita wanda hakan ke qara mata amanna da qaunar da yake iqirarin yana mata din,tuni ta yanke ma ranta abdur rahim na daya daga cikin batutuwan da zasu tattauna a gobe ita da mamanta,bai barta ba har sai da ya fuskanci ta soma jin bacci tukunna ya mata sallama cike da qauna da bege mai yawa

????????????????????????

Abu na farko da ta fara cin karo da ahi cikin gidan nasu bayan yin sallamarta shine dambe tsakanin huwaila da haduza abinda zata iya cewa bata taba gani ba,daga gefan huwaila lubabatu ce da binta ke zuga uwarsu,yayin da kuna gefan hadizar kuma shamsiyya da yasira ne suma ke nasu aikin sai jamila dake zaune bisa dakalin qofar dakin mahaifiyar tata da uban akwati a gaba,idanu jajir wanda ke nuna bisa dukkan alamu kuka take sharba ko kuma take kan sharba din,mamanta ta hango na shirin fitowa daga dakinta hannunta ruqe da dankwalinta tana mai qoqarin daurawa hindatu na biye da ita tana fadin
”don Allah mama ki barsu”

Da sauri maryam ta taya hindatu tarar maman nata
”mama wanna ba sabgarki bace,kin taba ganin suna dambe?,to ki qyalesun kamar yadda hindatu tace Allah ne yasan me ya hadosu,babu ruwanki mamana tunda koma mene lokacin da zasu qulla basu nemi shawararki ba,kiyi addu’a kawai Allah ya warware musu ita ta ruwan sanyi”

da dadin baki suka sanyata a tsakiya suka koma cikin dakin abinsu,har aka gama shigowa da kayan suna bala’i basu sani ba
”amma maryama gini irin wannan namun ai bai cancanci kayan gado na alfarma irin wannan ba”
dariya ma maman ta baiwa maryam
”haba mama,tunda Allah ya baki sun cancanta din kenan,yanzu aikin kawai zamu shiga yi har kitchen din”
hindatu dake tsaye wadda farinciki duka yabi ya cikata tace
”yauwa adda maryam,kinga zuwa gobe mun gama zama ‘yan gayu,babu raini wallahi,don duk cikin gidannan babu mai arziqin siyan irin wadan nsn kayan”
dadiya duka ta basu don har yau hindatu shirmen auta bai saketa ba

sai da suka soma fidda na dakin maman suna shigar da wadancan sannan suka ankara,lubabatu ce ta fara gani ta zunguri uwarta dake riqe da habar zaninta daketa kwancewa saboda azabar bala’i tana qoqarin daurawa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button