ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

”ina fata zuwa yanzu mutanen gida sun san da zama na?”
”tun yanzu abdul,duka duka jiya fa muka hadu”
”ke kika hadu da ni jiya,nikam ba tun jiya ba kika zama wani bangare daga jikin zuciya ta,so inason asan da ni maryam,aure nake so nayi da,wuri idan da ina da iko ma cikin watan nan banqi ki zama tawa ba”
tilas abdur rahim ya bawa maryam dariya
”gaskiya na baka sarkin zumudi na duk duniya”
”na amsa tunda sonki ne ya ja min”

cikin qanqanin lokaci ya cika zuciyarya da farinciki ta mance duka abinda take ciki,ba dadewa da gama wayar tasu bacci yayi awon gaba da ita don tuni mami ta yarje mata tayi kwananta a gida washegari taa dawo

????????????????????

qarfe tara na safe ta gama shirinta tas,a falo ta taradda hindatu na shirya musu abun kari kan center table daya daga cikin abunda jiya ya zama mallakinsu
cikin girmamawa hindatun ta gaidata ta amsa mata tana tambayarta mama
”mama na gurin baaba”
”ya dawo ne?”
”eh ya dawo dazu da sassafe,kin sanshi da tafiyar asubanci,yauwa tace idan kin tashi ki shiga ku gaisa”
”yanzu kuwa”ta fada tana ciro wayarta dake tsuwwar shigowar saqo tana dubawa
saqon barka da asuba ne aga abdur rahim,zaqaqan kalmomi da suka sanyata mirmushi ita daya tamkar wata zautacciya,tana mamakin yadda zuciyarta ta nutsu wa abdur rahim lokaci guda,sai da ta kammala karantawa ta masa reply sannan ta koma bedroom ta ciro dubu goma cikin kudin da mami ta bita kyautasu jiya dubu goma sha biyar

mamanta inna haule baaba hadiza sai lubabatu jamila da shamsiyya su ta tarar cikin dakin,kallo banza uka suka bita da shi,gefan binta ta matsa zata zauna,cikin rashin mutunci bintan ta janye jikinta tana wani harare harare da kumbure kumbure
gaida su ,bata da isar da zasu amsa mata har gara inna haule ta ama din sama sama,cikin girmamawa ta gaida baaban nata,ba laifi a sake ya amsa mata har yana tambayarta gun aikin nata,shiru ne ya biyo baya na wasu mintina sanan baaban ya dubi jamila
”inatambayarki tun dazu kun min shiru,yaro yace shi baisan lokacin da ya aureki ba,to inason in san ta yaya akayi ya aurekin,tunda shi ya rantse ya mayq bai san ke matarsa bace kuma bazai dawo dake ba”
cikin fitsara da rashin tarbiyya ta zumburo baki
”toni baba….ka tamvayi hadiza mana”
ya juya ga inna hadizan
”to kimin bayani tunda tace a tambayeki”
cikin borin kunya da haqiqancewa tace
”haba malam,wannan wane irin abu ne,ya zaka zo kasuwa ka dinga kwance min zani,sai da ka tara min idon duniya ni da diyata zaka hau bin qwaqwafinmu”

”ke hadiza dubanni nan da kyau,na gaji da iskanci da rashin mutuncin yaran nan,jiya tunda naje qauye fita ta daya na gaza fita,zance na ake ko ina,ance na kasa kula da yaya matan da Allah ya bani,dukkansu babu mai zaman aure ko wacce rabi aure rabi zaman gida,ga wasu kuma sun kasa auruwa”
zuciyar mafuam ta kada don tasan maganar qarshen tata ce
”to wallahi ya isheni haka,kun gama mai da ni mutumin banza ko,baku isa ba wanna karon na gaji ko masu auri suyo zaman auresu marasa aure suyi aure ko inci uban yarinya wallahi”
ba inna hadiza kawai ba hatta da su maama sunyi mamaki,yau baane ke ja in ja da inna hadizar?,lallai a dade anayi sai gaskiya,komai yayi farko qarahensa na zuwa babu shakka,a bangaren inna hadiza kuwa ta gama qullatar huwaila ne dadi bisa dari kan dukkan bala’in da taga ya afko,mata babu shakka ita ta qulla zuwanshi

qasa mama tayi da kanta tana fadin
”Allah ya huci zuciuarka malam,a yi mana afuwa”
sai yaji zuciyarahi ta dan rage zqfihar ya juya ya dan dubi maman,sannan ya maida idonsa gasu hadiza wadanda sjka zuba masa iddo qir babu mai cewa komai,baba hadiza na huci tana jiran ya gaya mata cuta ta fada masa mutuwa
”ke jamila ki tsaida hankqlinki,mahaifinki ne wanna,ki fada masa ya aayi hakan ta kasane don,samun bakin zaren,so ake a gyara lamarin ki koma gidanki kuci gaba da zama,mutuwar aure gun diya mace ai faduwar daraja ne,saidai kuma idan na qaddara ne”cewar mama

jin an sako maganar komawarta gidan jabir ya,sanyata cikin rawar jiki ta bude baki zata yi bayani a wautarta da jahilcinta za’a maidata din,don a yadda ta dandana zaman daula bata jin zata iya zaman gidan nasu kona wata daya ne bare na dindin din
tuni inna hadiza ta katsi numfashin jamilar
”uban me zaki gaya musu,cin fuska yaso yi miki kawai,ya aureki da kansa sanna yace baisan ya aureki ba,kujimin da,ke kuma aminatu banason munafurci da gilma,ina ruwanki?,ina cewa dai jamila bake kika haifa min ita ba,ai na dade da sanin cewa abunda kike nema kenan saboda har yau baqincikin qin aurar diyarki da baiyi ba yana nan cikin zuciyarki,to ahir dinki ki fita sabgata data yara na”
tsawa baban ya daka mata ya kuma ce ta ta shi ta fice masa adaki,koda ta ficen da yake ta riga da ta rainashi sai tayi tsaye abakin window tana eqa dakin tare da kallon jamila tana mata gargadi

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????✍????
[9/17, 12:53 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
???? ▶3⃣0⃣

HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

dauke kanta tayi tamkar bata ga gargadin nata ba,domin burinta kawai a maidata ga gidan jabir,don ba jabir dinne ma yafi damunta ba tunda bashi daman take aure ba dukiyarshi take aure,tana da abokanan holewarta a waje
a take ta warware musu yadda tayi amfani da sihirtaccen kwalli da turare har sau biyu ta dauke hankalin jabir ya aureta cikin gushewar hayyaci

gumi ne kawai ke ketsatstsafowa maryam,bata sake jin tsananin tausayin jabir ba sai a lokacin,shikam baban nasu shiru yayi ya kasa furta komai,kimanin mintina biyar sanna ya dubi su binta yace su fita adakin,sumi sumi suka fice ya dubi huwaila da tayi tsamo tsamo
”duk abinda kukayi huwaila don kanku,amma ku sani dole ne ku nemi yafiyar maryama don an zalunceta”
ya waiwaya ga inna hadiza dake labe yace
”kije Allah ya isa tsakani na dake,tarbiyyar yara da kika bata min,haqqin maryam kuma ke da ita,kya sake samowa jamilar wani mijin,ku taahi dukkanku ku bani guri”

dama a qagauce suke saboda kunya da nauyi tuni suka fice,saura maryam da mama,miqewa itama maryam din tayi ta ajjiye masa kudin hannunta
”ba wanna babu yawa amana addu’a,kuma kayi haquri Allah ya huci zuciyarka,insha Allahu zamu gyara dukkan abinda baka so”
”na gode,Allah yayi miki albarka,baki gaji ba maryam baki dade da yi mana hidima ba,har yanzu abincinki ake ci a gidan nan”
”ba komai baba,kunfi qarfin haka ai”

tana shirin ficewa mama tace
”dawo ki zauna ayo maganar yaron nan a qareta”
cikin rashin fahimta baban ya dubeta
”au ta samu wani mijin ne?”
”eh,gata nan ta maka bayani”inji mama bayan ta miqe tana tattare kwanukan da ya karya
kanta a duqe ta gaya mishi iya abinda ta sani game da abdur rahim din
”to,madalla,sai a sanar masa ya turo kawai,ai babu wani bincike da za’a tsananta tunda kina sonshi kuma ma kada muje ya subuce mana garin binike,kinsan wani baya son tone tone”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button