ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

”me ya hadaku kuma yau maryamu?,ban sanki da fad ba fa”hankali kwance ta gaya mata abinda ya faru,girgiza kai kawai mamin tayocikin takaici tace wuce amaryamu”
cike da takaici ta isa dakinta,tayi imani a lokacin da abidan ta taba jikinta ko siyar wace ce ita ba zata daga mata qafa ba,bata ga amfanin alkunya ga mutumin da baisan darajar dan adam ba,cikin ikon Allah abdul ya kirata,shi ya ebe mata kewa har bacci yayi awo gaba da ita

????????????????????

cikin bacci ta dinga jin yunwa na rage mata dadin baccin wadda ta tilastata farkawa,wayarta da ke gefan pillow dinta ta dauka ta duba lokaci,shabiyu da arba’in da takwas na dare,cikin mutuwar jiki da kasala ta sauko daga adon ta shiga toiket ta dauraye bakinta ta daura alwala ta fito ta tayar a sallah,raka’a hudu ta samu tayi tayi addu’oo’inta ta shafa

a hankali ta bude qofar dakin nata ta fito don samawa kanta abinci a dining,tayi mamakin ganin qwayayen falon duka akunne,ganin laptop da waya kusa da ita yasa ta bayar salma ce qarshen tashi tabar falo a haka

jingine yake da bango falon hannayenshi harde a qirjinshi,idanu kawai ya zuba mata fuskarsa qunshe da qaramin murmushi,yayin ita kuma take gaf da ahi har tana iya sheqar hucin nashi numfashin,hannayenta dafe da bangon kusa da kafadarshi
”fyaden kema zakimin?”ya tambayi salma kanshi tsaye,cikin lumshe idanu ta kada kai
”ko kadan,kawai ina da buqatar inji dumin jikinka ne,dubi kwalliyarnan duk kai na yiwa amma tun dazun nake jiran dawowarka,na hana idanuna bacci don kada ta tashi a tutar babu”
murmushinsa ya qaru fiye da na dazu,yasan kalma daya zaiyi amfani da ita wadda zata sata taji haushi
”sai ance mutum kaska ne yace shi bashi bane”
a maimakon yaga taji haushi kamar kullum sai yaga ko a jikinta,murmushi ta kuma yi
”to meye idan ma kaskar ce,duk akan sonka ne,nidai ko hugging dina ayi kawai na wuce dumin da naji da qamshin turarenka ya isheni”

ya janyeta ya bada nisa tsakaninsu yana fadin
”saboda tsabar raini ma naga sai da kika nemo irin turarena da shi kike amfani ko”
”idan zan kwanta na fesa jina nake kamara qirjinka nake kwance”ta fada tana sake matsowa daf da shi,hannunta ta dauke daga kan makunnin da takeson kashewa wanda hakan ya haddasa motsin awarwarayenta da suka jawo hankalin abdallah,jiki na rawa ta juya zata bar gurin,tuni ya saki briefcase dinshi da ya dawo da ita daga office ya biyo bayanta da sauri,ganin tana niyyar takawa a aguje yasanya shi dada hanzarinsa don ya fuskanci idan ya qyaleta zatq sake masa irin fassarar da tayi masa kwanaki,taku uku ya cimmata tare,da fusgota baya,tayi taga taga ta fadi jikinsa cikin tsoro da daukewar numfashi

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????✍????
[9/17, 12:53 PM] 80k: ABADAN31
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
© HASKE WRITERS ASSOCIATION
home of expert and perfect writers
jikinsa ta fada qeyarta ta samu masauki a tsintsiyar hannunshi fuskarta na facing tashi fuskar,yabi oily eyes and golden eyes dinta da kallo wadanda suka dada sheqi saboda hasken farin qwai daya mamaye falon ya haska cikinsu,ya kalli dan qaramin bakinta da yake motsi yana tattara kalmomin kayi haquri cikin rudewa
Ranshi ya baci,wai me yarinyar ta maida shi ne?,dan iska?,haka wancan karon tayi masa fa?,tana so tace masa a age dinta bata taba ganin romance tsakanin mutum biyu ba saboda tsabar rainin hankali?idan ma hakanne yau zai koya mata hankali,a hankali ya soma kusantar da bakinsa zuwa nata,numfashinsu ya soma gauraya,tsoro da rawar jikin maryam ya dadu,don tuni zuciyarta ta gama ayyana mata abinda abdallahn ke shirin yi
karon farko tattausan lips dinsa suka taba haduwa da na wata diya mace kamad yadda yake haka a gurinta,baisan yadda akayi ya tsinci kanshi da tsotson lausasan lebunan nata ba cikin rashin sani
”hasbunallahu wani’imal wakeel”kadai take ambata cikin zuciyarta,gudun zuciyarta ya dadu har numfashinta na qoqarin janyewa,hawayen dake malala kan fuskarta ne ya soma taba fuskarshi da sajen bakinsa na quater millon
”abdallah!,meye haka kake yi?”salma ta fada cikin qaraji da wani irin yanayin baqin kishi da bata taba shiga irinshi ba,a nutse ya saki bakin maryamun ya juya yana kallon salmar wanda hakn ne ya bawa maryam qwarin gwiwar hada ragowar qarfinta don ta tsere masa,saidai tana tashi taji ya cafko dantsenta idanunsa na kan salma,kallon ‘yan sakanni ya mata ya maida idonsa ga maryam
cikin fada da tsawa yaso yi mata maganar amma sai ya gaza,kasala ce ta saukar masa lokaci guda tamkar mai jin tsananin barci
”gobe ma idan kinganni tsaye da wata kimin kallon dan isaka,zaki ga yadda ake iskanci ra’ayil ain”ya fada yana kallo tsakiyar qwayar idonta da hawaye ya cika yake zuba kana ya cikata,da gudu kuwa ta bar gurin sai ya bita da kallo yayin da salma ita kuma ta tsare shi da idanunta wadanda suma tuni suka kawo qwalla
”haba,haba abdallah,irin wannna cin fuska haka da me yayi kama?cook dinka?”ta fada tana nuna hanyar da maryam din tabi da yatsa ”abdallah ka rasa bakin da zaka tsotsa sai nata,ni me na gaza da shi?just hugging dina kawai nace kayai ka kasa sai gashi ka buge da kissing house girl”
”hey!stop”ya tsaidata cikin hade girar sama data qasa,ya qara taku biyu ya iso gareta ya tsaya agabanta
”kada ki sake ambatar nayi kissing yarinyar can,kaifi tayimin nayi punishing dinta,ina fata kun fahimta”
murmushin takaici ta saki sannan takama qugunta da hannu daya tana girgiza kai
”kada ka maidani jahila mana abdallah,sau nawa ina maka laifi ka taba punishing dina ta wannan hanyar”
har ya juya vaya taba dauke briefcase dinsa sai ya waiwayo
”ita tana showing kanta a matsayin kanta a matsayin mai nutsuwa tana min kallon abinda ban taba aiwatar da shi ba,kinga gwara nayi mai dalili ko?”
girgiza kanta ta sake
”ko jikina kunne ne bazan yadda ba,kayi ne da manufar wulaqantani da nunama duniya iyakata”
”well,idan hakan kika zaba shikenan daidai ne”ya fadi yana kewayeta ya fice daga sashen bayan yasa key dinshi ya kullesu ta baya kamar yadda yazo ya tarar da su,dama abincinshi ya shigo yaci ya sameta zaune ita daya afalon
kamar ta dora hannu aka tayita rusa ihu haka ta ji,hawaye shabe shabe ta shige dakibta bayan ta qudiri abinda zata aiwatar musu a gobe
Qarfe goma ta gama breakfaat di gidan ta shiryashi a dining,Allah Allah take ta kammala komai ta shige dakinta don bata son haduwa da kowa uwa uba abdallah da take masifar jin haushi tsoro da tsanarsa,ta yanke ma zuciyarta abdallan yana layin ‘yan iskan maza ne kawai,tuni ta bashi wannan sunan
tana gefan gadobta tana shafa mai bayan sanya doguwar rigar atamfa da tayi mai dogon hannu taji wayarta na b’urari,sunan mami ya soma yawo saman screen din,haka kawai gabanta ya fadi,cikin rashin kuzari ta sanya robar lotion din dake hannunta a gefanta kana ta daga wayar,tana qoqarin gaidata taji tace
”ki sameni yanzun a sama”
”to mami”ta fada cikin rawar murya,kasa ci gaba da shiryawar tayi sai ta zaro blueblack din hijabibta ta ware shi daga gugarsa ta sanya ta miqe ta fice a dakin
kallo daya ta yiwa mamin gabanta ya fadi don zata iya cewa a iya saninta da ita bata taba ganin yanayin fuskarta haka ba,gefanta salma ce zaune fuskarta jazur idonta a tashe,a salube ta qaraso,qasa ta zauna daga can gefe tana fadin
”barka da safiya mami”
”matsonan”tace da ita tana nuna mata gabanta ba tare da ta amsa gaisuwar tata ba
”maryam,me ya faru jiya da misalin daya da wani abu na dare tsakaninki da abdallah?”wata mummunar faduwar gaba ta ziyarce,tsoro da fargaba suka mamayeta ,bata raba dayan biyu wani abun salman ta gayawa mami mai muni a kanta
kimanin minti uku mamin na saurarenta babu amsa,don bata da bunda zata ce din
ta fadi gaskiya?,bazata iya ba,tasan mamin mai yarda ce da gaskiyar abunda ta fada din amma bata burin shiga tsakanin soyayyar da da mahaifiyarsa don ta dan dana hakan ba lamari ne mai dadi ba kona second guda
ta musanta kuma ya zamo mata zunubin qarya,idanun mamin na kanta tana jin babu dadi cikin zuciyarta,don har ga Allah ‘yar cikinta take kallib maryam,dan yanzu ba’a shaidarsa duk da ta shqida da nagartattun halayen abdallah,amma yaran zamani koda yaushe yana iya sauya halayyarsa,tsoronta daya kada ya yaudari maryam din ya bata rayuwarta,hakan idan ta tuna shike qara hasalata da sa mata suya cikin zuciya
”dake nake magana kinhi shiru”
shirunne ya sake biyo baya,tuni hawaye ya soma ambaliya cikin idanunta tana sa gefan hijabinta tana sharewa
”to tunda kinqi magana bari na kira ahi shi mai gayya mai aikin yayi bayani”
”a’ah mami,tun farki na gaya miki ba laifinshi bane”
salma ta fada da sauri har tana kamar zata dafe hannun mamin da ya dauko waya don kiran abdallah
wani kallo mamin tayi mata
”bana hukunci da ji daga bakin bangare daya ba tare da dayan ba,koma mene da nashi laifin kuma tilas ya bayyana nan,”
mami ta qare maganar tana kara wayar a kunnenta
shiru ne ya biyo baya har ahigowar abdallah,sanye yake da kayan training ajikinsgi wanda da alama yana filin motsa jiki ne,hannunahi daya handkhercief ne yana tsane gumin suma da fuskarshi,daya hannun kuma gorar ruwan swan ce dake fidda gumin sanyi bisa dukkan alamu a falon qasa ya daukota
da zolayar mamin ya shigo falon saidai yanayin fuskarta kawai ya bayyana mishi ba lafiya,shi sam bai kula da su ba cikin falon ba sai da mami ta jeho masa irib tambayar data yiwa maryam sannan ya kuka da salma
cikin ko in kula yace
”nothing happened,nasan dai sha biyu da rabi na dawo gida,so ina jin yunwa sai na bude nan na shigo naci abincina,sai waccan da na hadu da ita zaune a falo tana game”
”ita kuma maryamu a ina kuka hadu da ita?”ta fada tana nuna masa ita wadda kanta ke duqe
yatsan bata yabi da kallo har zuwa gun maryam,sai ya yamutse fuska
”wace kuma maryamu?”ya fada yana shanye ragiwar ruwanshi,sai ran mamin ya baci,ita zai bunne,tasan waskewar abdallah sarai tunda ita ta haifeahi,kadan daga aikinshi ma yace bai tabajin sunan ba sai yau
”ni zaka ninke a baibai?,ko ka manta cewa ni na haifeka na raineka?, a hannuna kayi wayo?,naci kashinka da fitsarinka?,yaushe abdallah ka sauya hali?,ita da na tambayeta ai tasan baku da gaskiya shi ya sanya tayi shiru bata ce komai ba,amma kai da yake madainiyar wayonka ta tambayeta sai ka nemi raina mata wayo ko?”
ya danyi qasa da ido dob sam kalaman mamin basu yimishi dadi ba,bazai iya yaushene na qarshe da rayi masa irin wanna fadan ba
muryarshi a sanyaye yace
”idan ita ta gayamiki ai sai ta bude baki mami ta fadi abunda na mata ko?”
”ta gaya min ne tunda tare kuka aiwatar,mai kishina binda ya faru ne ta fada salma,har yaushe ka farq neman yaran jama’a,ko kunyar ina cikib gidan bakayi ba?,kasan illar da girman zunubin abinda kuka so aikatawa badan Allah ya kawota ta hana afkuwar lamarin ba,mai makon kuma ka gode mata sai cin mutunci ya biyo baya?”
sumewa ne kadai maryam bata yi ba a zaune kukan da take aboye sai ya koma na fili,ran ‘yan maza yq baci take idanunshi suka sauya kala,ya zubawa salma ido wadda runi dana sanin abinda ta aikata ya mamayeta,ita so tayi aci mutuncin maryam ita kadai a kuma koreta ta bar gidan,kasa daukar irin kallon da yake matq tqyi tqyi qasa da idanunta
muryarsa a kausaahe cike da sautin fushi yace”wanne la’a nannen Allahn ne ya mana wanna qazafin,ko da yake mami kince salma ce,amma nayi mamki mami,kin san halina ciki da bai,kinsan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya ba,me yasa lokaci guda wata can zato ta rushe kyakkyawar fahimtar da mukayi shekara da shekaru da gina ta,kai cina da har yau,ban kubuta daga zarin zan aikata zina ba daga gun mahaifiyata”ya fada yqnq girgiza kai jijiyoyin kansa na tashi,sai jikin mqminyayi sanyi,tabbas babu kyau gaggawar yarda da abunda baka da yaqini,balle abdallah da maryam,babu wana bata san halinsa ba,dukkansu tasan ne zasu aikata da wanda,ba zasu aikata din ba
ganin da salma tayi mami na shirin yarda da abdallan ita ta tashi a tutar kunya ya sanyata sake,zaqalqalewa
”ni ba la’a nanniyar Allah bace,kuma na gani din ne da ban gqni ba ai da bazan……”
bata qaraahe maganar ba taji quma abakinta,abdallah ya jefeta da ruwan robar dake hanjunahi wanda ko rabi bai sha ba,aka kuma yi sa’a ya sauka a bakin nata,ta dafe lebunan nata wani azabar zugi na ratsata,take lebunan suka fashe,bayan sun kumbura sunyi suntum cikin daqiqar da bata wuce talatin ba
hakan baiwa Abdalla ba ciki fushi ya yo gunta,da sauri mami ta shiga tsakaninsu tasa hannunta tana tokare qirjinsa don iya inda tsawonta yake kenan tana turashi da baya
”ki barni mami na lalata shashan bakin da bai iya komai ba face sharri da qazafi wa mutane”
”ka dakata abdallah,nutsu don Alla banason shashanci”mamin ke cewa,tasan halinshi sarai,bai fiya sairin fuahi ba amma idan ya fusata din komawa yake kamar mahaukacin zaki
kusan minti biyar mamin na artabu da shi
”na nutsu mami,amma na bata minti goma ta tattara dukkan wani abu nata tabar gidan nan,wallahi wallahi ta sake muka sake haduwa da ita sai na nakasta ta,banza shasha sha kawai,don ina rufa asirinki,sau nawa nake kamaki da syrup da capsule cikin jaka,shine har kike da bakin yiwa wani qazafin zina,to idan baki bar gidan nan ba nan da minti goma ba nine zan zamo mutum na qarahe da zaki tiwa qazafi a rayuwarki,bindigata zansa na harbeki ki mutu kowa ya huta”
cikin huci ya juya a sukwane ya fice,da sauri maryam tayi gaggawar jaye qafafunta badon tayi hakan ba kadan ya rage ya take mata dogayen yatsunta
bibbiyu ya dinga hada matattakalar har ya gama sauka daga benan,abida ce da saddiqa tsaye kowacce cikin sleeping dress tayi tsuru tana sauraron abinda ke wakana a saman,zuciyar kowaccensu tayi fari jin an kori salma suna ganin tamkar aiki aka rage musu
wani banzan kallo ya bisu da shi ba tare da ya furta komai ba ma suka watse
cikin mintina qasa da goma salma ta hada komatsanta tana kuka wiwi mami na lalkabrta ta shiga motarta ta fice agidan,ranar sai gidan ya wuni shiru kowa na dakinsa,mamin ma haqura tayi da fita asibitin ranar don tsoron kada ta tafi wata fitinar ta taso,jin shirun yayi yawa abdallah bai sake shigowa ba ya sanyata tattaki da kanta zuwa bangatenshi,don ta san cewa ba lafiya,don komqi akayi bazai iya fita bai gqyq mtq ba,to tabbas yana cikin dakinshi ne
A qurya ta sameahi kwance daidai yayi rigingine kan gadonshi,shigowartaya sanya shi miqewa ya zauna
”me kake haka har yanzu baka fito ba ko karyawa baka yi ba ga azahar ta gota biyu da rabi fa yanzu”
”bana jin yunwa mami”ya fada cikin rashin walwala,sai kuna ya dago ya dubeta
”mami ina fatan bakiyi fushi da ni ba,na kasa sukuni tun dazun”
dama ta sani a runa,yanzun haka bacin ran da ya gqni kan fuskarta ne ya sashi kasa fita,tun yana qarami haka yake,baya juriyar ganin bacin ranta
”zan iya yin fushin da kai dai na haqiqa matuqar baka gayan gaskiyar abunda ke faruwa ba”
”zan gaya miki mana mami,mami kiss ne kawai,wallahi bayan haka babu komai,kuma ko shi din ma haushi ta bani,kallon dan iska take min”ya fada bayan ya riqe hannayen ta cikin marairaicewa
dariya yaso bawa mamin amma sai ta gimtse don ba muhallinta bane
”don tana maka wanna kallon idan banda rashin dabara da wayo ta hakan zaka wanke kanka ta fahimci na gari ne kai?”
”am sorry may mami,nayi kuskure”
a nutse ta dinga masa fada sanna ta rufe da fadin
”idan irin hakan ta sake faruwa raina zai baci fiye da bacin ran daka gani yanzu,don ban yarda asabi Allah ba,duk son da nake maka zan iya ajjiyeshi gefe na hukuntaka hukunci mai tsanani,kada makamancin hakan ya sake faruwa akan ko wace ma indai ba matarka bace”sai maganarta ta qarshe ta bashi kunya ya dan sunne kai
dariya ta danyi
”da nema yau kuma nice akejin kunya”dariyar shima ya tayata
sai kuma ta hade cikin seriouse tone
”sannan abdallah,lallai lallai ya kamata kayi aure indai kana son hankali na ya kwanta yadda ya kamata,ka fidda mata cikin masu qaunarka”
qasaitaccen murmushin nan nashi ya saki
”relax mami na,insha Allahu kwanan nan zan sanyaki farincikin da kika dade kina fata,zan kawo miki mata ta har gida nan kusa,amma fa abida da saddiqa kowacce ta wuce gidansu,don wlh mami bazan iya auran kowaccansu ba”
”naji,saddiqa dama gobe tace zata tafi,abida kuwa dole ayi haquri sai an samu visa,zata sake ko sati uku ne tare da mu”
”shikenan mami,zan wa abokina magana harkarsu ce”
qememe yaqi fita yace zai je ko ina ba sai ya tabbatar ta gama hucewa haka suka wuni a gida gaba dayansu
mrs muhammad ce
[9/17, 12:53 PM] 80k: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button