ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

       ▶3⃣2⃣

Allahumma ya imada man la imada lahu,ya sanada man la sanada lahu,ya giyasa man la giyasa lah,ya karimal afwu,ya hasanat tajawuz,ya khaahifal bala’a,ya azimar raja’a,ya aunaddu’afa’ah,ya munqizal garqa,ya munjiyal halka,ya muhsin,ya mujmil ya mun’im,ya mifdil,antal lazi sajada laka sawadul laili wa nurun nahaar,wa dau’ul qamar wa shu’a ushshams,wa da wiyyul ma’i wa hafifushshajar,ya Allahu la sharika lak,ya rabbi ya rabbi ya rabbi,Allah ka shiga lamarin mutanen qasar burma,Allah ka shiga lamarin jama’ar musulmin duniya baki daya don sayyadis saqalain????????????????????????

Qarfe goma saura na dare mami ta shiga dakin nata,har ta gama shirin bacci tana kwance tana jiran wayar abdur rahim da yace ta jirashi kada tayi bacci zai kira ta,da sauri ta miqe tana maida hularta da santsin gashinta ya sa ta sabule,mamin ta dan bita da kallo qauna da tausat
yinta suka lullubeta ganin ta takure ta kasa hada ido da ita

gefan gadon ta qaraso ta zauna kusa damaryam don ta dafa gadon bayanta
‘.dago ki kalleni maryamu,mamanki ce fa”sai taji qwalla na shirin zubo mata nauyi da kunyar mamin takeji,gefe daya hauhi da tsanar abdallah na takura zuciyarta
”ki kwantar da hankalinki abdallah ya yimin bayanin gaskiya,ba laifinki bane laifinsa ne,kuma nayi masa gargadi insha Allah bazai sake faruwa ba kinji,ki i gaba da kame kanki maryam kamar yadda kike,daraja mace da mutuncinta yana tqfin hannunta,ruwanta ne ta riqesu su zame mata abun alfahar ruwanta ne ta wargaza,bazan so wani abu ya shafi mutuncinki ba maryamu don tamkar amana kike a hannu na,ko bayan haka ma unajinki har cikin zuciyata,haka za bazan iya yafewa abdallah ba idan ya maki wani abu da ya sabawa shari’a da mutuncinki,duk abinda kuma nayi nayi ne saboda kare martabarki,ina fata kin fahimce ni?”
gayada kai tayi tana share hawaye
”na gane mami,na kuma gode Allah ya qyara girma da lafiya”

wayar abdur rahim ta katse ‘yar hirar da mamin ta fara janta da shi don ta saki jikinta,ganin maryam din taqi dauka yasa mamin ta dago wanda ke kiran
”bari in abku waje kinga ma shikenan ya fanshe ni sai ya qarasa lallashin,ki gaisheshi sai da safe”ta fadi tana miqewa cikin dariyar zolaya,kasa amsawa tayi ta sunne kanta saboda kunya mamin na dariya ta fice

hira suke abinsu sosai irn ta masoya kamar sun shekara da sanin juna
”maryam ya kukayi da abban,nasan dai an bani dama ko?”
ta dan zaro ido tana fadin
”wa ya gaya maka,abdul irin wannan zumudi haka”ya marairaice murya
”maryam bani so in rasaki ne inaso a bani dama koda kudine a kawo”
ajiyar zuciya ta saki
”abdul dole dai ai mu danyi haquri ko,tunda yanzun dai kaga azumi saura kwana bakwai,mu bari bayan sallah idan Allah ya kaimu sai ayi dukka abinda za’ayi”
”wa ya gaya miki azumi na hana kai kudi,akwai cousing dina safiyya hudu ga azumi aka kai kudin aurenta,so pls maryam ki barni na kawo kudin idan yaso bayan azumi asa mana ranar aure na qagu ki zama tawa,baki san ya nake ji ba duk lokacin da na kalleki ko naga kin fita a matsayin budurwa ba mata ta ba,bani da wani iko a kanki”

dariya ta saka
”yaushe ma kake ganin nawa ne abdul”
”ina iya ganinki mana da idon zuciya”
”shikenan yanzu mu bari zan sanar da mami na,duk yadda ta kama zaka ji”
da qyar abdur rahim ya barta bayan ya cikata da dad’ad’an kalmomin qauna

????????????????????????

Su hudu ne cikin lafiyayyar motar da idan ka shiga ba zakayi tsammani tafiya akeyi ba sai idan kaga kuna wulga gurare,mami ce da maryam a baya sai Abdallah da driver a gaba
mami cikin shigar leshi dinkin buba orange wanda yasha adon lemin hreen,takalmi jaka da mayafi dukka toomatch masu dan karen tsada da kyau,ba qarya mami gwanar iya ado ce,ko cikin mata masu shekarunta da wuya ka samu irinta goma,shi yasa sam sai ka rantse bata haifi abdallah ba,zakayi tsammani yayarsa ce kawai
maryam ma cikin cikin kwalliyar take amma zamu iya cea kwalliyar jiki don babu wani make up a fuskarta,material ne pich da kwalliyar sea green,tayi adon takalmi mayafi da fashion na dan kunne duka kalan sea green,ba gwanar jaka bace hakan ya sa wayarta ce kawai riqe a hannunta,abdallah dake gaban mota yake ta faman zuba mitar shi kam da an barshi bazaya je ba,ba gun zuwanshi bane idan ba kamawa tayi ba,sanye yake da shadda light blue dinkin tazarce da yaji aikin hannu na maza dan ubansu da baqar hula,takalmi sau ciki baqi da agogo,kallo daya zaka masa ka tabbatar kudin da jikin nashi ya lanqwame ya ishi mai qaramin qarfi jari

”ayita aure gab da azimi barna tayi ta afkuwa”ya fada yana yarfar da hannunshi wanda ke daure da agogon ruwan gold”nikam dai wallahi kam duk wanda yamin aure a irin wannan lokacin alhakin a kansa”

”baka da kunya ka maidani kakarka,yaro duka ka gama mitarka,dinner ce dai si kaje,minti nawa anyi an gama,hajiya mai gado idan da halacci ba zaka mata haka ba,ita tayi yayenka abdallah,ba qaramib sonka take ba”
ya dan waigo yq dubi mamin
”ayyah mami me ya kawo maganar yaye na”ta dago shi qwarai wai shi baya son raini,dariya ta saka
”to meye kowa ma an masa yaye har ni kaina”kadan kadan take bashi labarin quriciyarsa gidan hajiya mai gadon,yana son ji amma baiso wani ya ji masa ya raina shi don haka ya canza topic din

”mami,cikin kwankin nan nake son kawo miki dear ta gaidaki,so kuma bata nan sunje umarar azumi,ni kuma na qagu mami in yi wani motsi”
murmushi ne ya subucewa mami
”ummm,abdallahhh……,yaushe ka zama haka?yaushe sonta ya maka irin wannan kamun?kai har naji ina sonta data iya sato zuciyar birkitaccen yarona haka ta farat daya”
murmushi yayi hadi da lumshe idonsa,ya jinginar da kansa jikin seat din motar yana tunata yana jin wani yanayi na shigarsa,mami ta sosa masa inda yake masa qaiqayi
”dis luv inside of me is strong mami,there ar no boundaries that it can hide”

Kasa daurewa mamin tayi har sai da ta dan daki kafadanshi ta baya dariya ta kamata,ringin din wayar maryam ya katsesu,abdur rahim ne,kamar ko yausheta kasa dagawa saboda kunyar mami shi kuma bai fasa kira
tsaki abdallah yaja yana fadin
”du Alla a kaahe wannan culculator din ya damemu haka nan”
mami ta kalli maryam
”daga kiranki maryam,ba mai jinki hirar mu muke”
tsaki ya kuma j”idan ba zata daga ba asauketa ta kammala wayar ta biyo mu daga baya kota koma gida”
”shut ur mouth,oya ina jinka,muyi maganar dake gaban mu”cewar mami

Minti ashirin tsakani suk iso gun dinner din,ita dai maryam rava idanu kawai take don bata saba zuwa ire iren guraren ba,bata da wannan rawar qafar sam,da dai su jamila ne su lubabatu tof babu na biyunsu
uwar taron dakanta ta fito ta taresu
”masha Allah hajja bintu ina kika samu kyakkyawar diya haka,ko surukar taki ce”
murmushi tayi ta wauwaya ta kalli maryam da abdallah dake bayanta,sai taga sun mata kyau din kuwa tamkar wasu couples,abinda bata taba kawowa a ranta ba ta jishi lokacin,sai taji tana fadi cikin zuciyarta ina ma da gaske ne haka dinne,ya waiwaya ya danqarawa maryam harara sai akayi sa’a suka hada ido,ya dan matso gab da ita har tana sheqar qamshinsa kana yayi qasa da murya kamar mai fada mata abun arziqi
”yi gaba mamalama,kin wani jera da muta ne kamar sa’anninki,salon ‘yan jarida su ganmu tare ki samu daukaka ni kuna ki bani kunya”,itakam tsoronshi take don neman tsari take da shi hakan ya sanya batare ce masa komai ba tadan ja da baya da yake ya fita sauri tuni ya dan zar tata

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button