ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

mami ta kalli hajiya mai gado
”diyata ce ita din ma,amma surukar naku na zuwa insha Allahu,don shekaran jiya yaron naki ya min albishir,ya gama ruwan idon nashi da bani kunyar gun iyayen yara”
”a’ah,a qyale yaro na,ai lokacinshi ne a barshi ya zaba ya darje,ai ya cancanci yin hakan”
”um um kada ka ki fasa masa kai”
”ba zancan fasa kai sai tsabar gaskiya”da daddan hirarsu irinta qawaye suka iso gurin da ka tanada don baqi na musamman irinsu
anyi kiran iyayen amarya suzo su nuna tasu karar don haka mami ta miqe,ta dubi abdallah dake ta faman shan qamshi idanunshi na kan waya tunda sukazo
”bari muje nida martmyam liqi yanzun zamu dawo,kaima ya kamata ka qarasa ku gaisa da amaryar”
”ina zan iya tashi an cika guri da sakarkarun ‘yammata marasa kamun kai,duk inda ka motsa suna kallinka kamar wasu mayu”
”kaji da shi dai,kallo kuma kayi abun kallin ne dole a kalleka,dukka abokan ango na gun stage suna liqi kaja ka zauna bayan kaima abokinka ne”mamaki ya cika maryam,yadda taji ana tababa da shi kan bazai je ba tayi zaton ma bai sanshi bane
”mami ni bazanje in kalli matar wani ba don nima babu mai kallarmin tawa”
”haka za’ayi naka bikin kenan kana nufin”
”ko za’ayi mami ba zata zo min da irin shigar da amaren yanzun suke ba,sai babballata in zubar”
hade rai mami tayi
”to ni kuwa bazaka balla ‘yar muta ne ba ka barmu da jidali ba ka canza tunani”
murmushi ya subuce masa ganin yadda mamin ta hade rai kamr ma ya riga da ya aikata
miqewa yayi ya karbi jakar hannunta yana dariya
”Allah ya barmin ke mamata ni daya,muje in rakaki,Allah ya huci zuciyar hajiyata”
”hutsu ne abdallah”maryama ta fada cikin zuciyarta,suna hada ido ya daka mata harara ya kuma hade rai qyam tamkar bashi yake murmushi yanzun ba
a baya suke binta har suka isa atge din,ya miqawa mami jakar yana fadin
”gashi mami,ayi liqi a hankali”
”haba handsome,girman mami ne ai ta liqa ko nawa take so,babu ji tunda tana da kai”maryam da abdallah suka kalleta lokaci guda don mami bata ji ba tuni da kutsa ciki,wani sakaran kallo yayi mata gami da jan tsaki,ita dai maryam gaba tayi tana qoqarin bin sahun mami tana fadin cikin zuciyarta
”kin debo ruwan dafa kanki”
ji tayi an riqo tsintsiyar hannunta gam ana janta,babu shiri ta waiwayo abdallah ne tuni har ya fara tafiya,tilas ta saita wa kanta hanya ta bishi a baya tamkar raqumi da kala,don idan tayi tirjiyar bin nasa zata iya zubewa a qasa don da sauri yake jan nata
bai saketa ba sai da suka iao teburin na su kana ya sakar mata hannu hadi da yi mata nuni da kujerar data tashi dazu a kai,tsareta yayi da idanunshin nan masu kaifi
”sit,dake aka hada kutingwilar zuwa na nan,shine kuma duka zaku fashe ku barni zaune ji daya kamar yaron mayu,ki zauna ki kula da ni har mamin ta dawo ta karbeki,daga nan ma idan club zaki wuce ke ya shafa”
Tuni hawaye sun cika idanunta,bata ce masa komi ba ta zame ta zauna,shi kuma yayi tsaye hannayenshi harde bisa qirjinsa yana qarewa gun kallo tamkar mai neman wani
matashin saurayi ne yake dosowa gurin,kallo daya zaka masa ka tabbatar da cewa ya gogu cikin duniyanci,sannu a hankali yake qarasowa har inda maryam din take,shigowarsa gurin kenan idanunahi sukayi tozali da ita,totally ta gama yi masa fatanshi daya ‘yar hannu ce,zai iya kashe mata ko nawa ne matuqar zai samu hadin kanta,ta bayan kujerarta ya zagayo yasa dukka hannayenshi ya dafe makarin kujerar
”hello babe…”
gabanta ne ya yanke ya fadi,har ta kasa jiyowa taga ko waye,ga zatonshi bata ji ba don haka ya ranqwafo bayan nata yana shirin sanya hannunshi ya dafa kafadunta
cafkar da yaji an yiwa hannunshi yasan bata wasa bace,tamkar tarko ya kama bera haka abdallah ya riqe hanun nashi tsam,bai gama qarewa abdallan kallo ba yaji saukar lafiyayyun mari guda biyu da suka gigita shi,
hannu abdallah yasa ya yaye dogon hannun rigar t shirt din dake jikin saurayin,take wasu yan qanan rubutu da suka fi kama da na ‘yan china suka bayyana a saman tsintsiyar hannunshi,a tare suka kakki juna ahi da mataahin tashin farko tsoro qarar ya bayyana idanun matashin,motsin da matashin ya fara yi da daya hannun nasa da abdallan bai riqe ba yana qoqarin cusa hannunshi aljihun bayan wandonshi ya ankarar da abdallan,cikin hanzari ya dunqule hannunshi ya daki hannun matashin take ya sagar masa da duk wata jijiya da zata taimaka masa ya iya motsa hannun,ya zura hannunshi aljihun matashin ya ciro ‘yar qaramar bindiga ya cillata cikin nashi aljihun,qarar da ya saki ita ta janyo,hankalin mutanen dake kurkusa da su,cikin zafin nama da qwarewa da hannu daya ya tsinke duk wani maballi dake jikin t shirt din matashin ya finciketa daga jikinsa hade da juyo da bayan matashin ya kalla,zane ne kala kala a jiki wanda ba lallai kai ka iya ganewa ba
”anaconda isnt it?um?yaron alhj hamza mai qusa”
Abdallah ya fada bayan ya zagayo gaban matashin sunyi face to face,hannunshi daya ya sanya a aljihub rigarshi ya ciro qaramar wayarahi keypad qirar samsung,cikin qanqanin lokaci ya bada order turo ma’aikata inda suke din kana ya maida wayar aljihunsa,idanunshi qyar cikin na matashin yake tambayarsa
”ku nawa ne agurin nan?”shiru ya masa babu alamun zai amsa masa,hakan ya bawa abdallah damar yin tsai yana karantarshi,ba tare da matashin ya masa nuni ba ya karanci tabbas akwai abokin tafiyarsa ahannun daman abdallah,sai kuwa akayi dace shima ya yunquro da niyyar kubutar da dan uwanshi,duka daya abdallah ya waiwaya ya masa a dokin wuyanahi ya zube a qasa yana malelekuwa.
minti goma kyawawa basu cika ba jami’an ss suka iso gurin ya damqa musu su yace su kira jamal hussain ya fara aiki a kansu kafin gobe ya iso office din,mutanen dake gurin kam kowa godiya yake ma Allah suna fadin Allah ne kadai yasan me zai faru badon zuwanshi ba,sai da koma cikin mota ya kira mami yace suzo su taci don baya son,jama’suci gaba da shaida fuskarshi
ko cikin motar tamkar kace ket maryam ta zura a guje take ji,tsoron abdallah ya kuma cikata,ya dubeta da madubin motar lokacin da yake goge hannunshi da handkherchief suka hada ido,hade rai yayi yaja tsaki
”mutum sai shegen tsoro,komai ma tsorataka yake”mami tayi zaton da jama’ar inda suka baro yake
”a’ah wannan lamari fa da tsoro,wannan aikin ai saiku,kawai dai Allah ya tsare mana ku daga dukkan sharri”
murmushi ya saki
”haba mami na,kema fa jaruma ce,kin manta ke ke fede mutum ki ciro abun cirowa ki,mai da na mai dawa ki hadeshi ki dinke ya tashi tsaf yaci gaba da rayuwa cikin ikon ubangiji’
”um um,wannna daban da naku abdallah,a’uzubika bi kalmaatillahit taammaat min kullu ainin lammah wamin kulli shaidanin wa hamma”ta mishi irin addu’ar neman tsari da annabi s a w kewa hassan da usaini r.a
”ameen mami”ya fada don kusan a bakinta ya haddace wanna addu’ar tsabar yi masan da take yi,kuma yasha ganin riba da fa’idar ta
????????????????????????
ana jibi za’a dauki azumi ta tafi gidan raliya don su tattauna,ba qaramin dadi raliyan taji ba dq jin fitowar abdur rahim da dukkan qarfinshi neman auren aminiyar tata,ta jira har nasir ya dawo tayi mishi bayanin abdurrahim da kwantancan anguwarsu,ya dauka mata alqawarin xaiyi tattaki da kanshi har unguwar ta qoqi don ya mata bincike a kanshi,sosai taji dadin kara da karamcin da hayi mata,sun rabu kan duk yadda ake ciki nan da sati zaya sanar mata,ta mishi godiya sosai,yace babu komai ai an zama daya ya zolayeta da don ma ta qishi ne,dukkansu dariya suka saka da tuno baya da sukayi