ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

kwanki shida kacal ba’a cika na bakwai din ba nasir ya kirata ya mata bayanin abdur rahim bashi da matsala,dukkan abunda ya fadi din haka yake,saidai abu guda bayan kasuwanci da yakeyi din yana da damara wato ma’aikacin tsaro ne,ta masa godiya mai qima sannan suka rabu,data tambayi abdur rahim din dariya kawai yayi yace yana tsammanin bata son auren mai unifoarm ne ya boye mata,bata dauki abun wani seriousd ba duk da ta nuna masa rashin jin dadinta ya kuma nemi afuwarta maganar ta wuce

azumi na da kwana goma ta sanar da abdur rahim ya shirya yazo ya gaida mami,bai musa ba ya amince,ta shirya masa girki na musamman,cikin wani dan kebantaccen gu dake harabar gidan ta ahirya komai,guri ne mai kyau davtsari cike da shuke shuke tamkar qaramin lamvu,duk da cewa daga can bayan gida akwai lambun amma wanna hakanan aka yishi darumfar bunu qwaya daya,qasanta shirye da fararen kujerun roba

mintina goma sha hudu ya rage akira magariba ta shiga wanka,ta ahirya tsaf cikin baqar doguwar riga mai sulbi data wadatu da dutsuna masu sheqi saqar qasar oman,mai kawavta shafa hoda ta zizara kwalli da man lebe,ta taje gashinta tayi acuci da shi daidai lokacin da masallatan garin kano suka soma kwarar kiran sallar magariba dabinonta dan madina dake cikin qaramin fridge din dakin ta ciro ta ciri uku taci ta ciro ruwa tasha sanna tayi add’ar buda baki,bandakinta ta koma tayi brush hadi da alwala ta yi sallar magaribar,kusan tunda aka fara azumi tare suke yin buda baki gaba dayansu,don haka bakwai na qarasa cika ta sauko qasan

tuni har mami da abida sun hallara don haka ta gaida mamin da yi mata sannu da shan ruwa ta soma sarving dinsu,ta kammala ta ja nata ta zauan,bata kai ga fara ci ba abdallah ya shigo ya ja kujera kusa da mamin yana fadin
”mami ke daya zaki ci ki bar autan naki”
”hmmm su auta manya”abida ta cafe zancan,harararta ya danyi
”kinga bansa da ke ba,wanna magana ce tsakanin d’a da mahaifiya”
hannu yasa cikin plate din chips dinta ya soma kaiwa baki dadin na ratsashi,bai ko kalli farantinsa guda biyu da cup da maryam ta shirya masa ba

sai teburin yayi shiru kowa na harkar gabanshi,cakula kawai maryam keyi don bata qaunar zaman cin abincin nan tare,sam bata sakewa
mami ta dubeta tana goge hannunta da ya dan baci da maiqo da tissue
”amma dai maryam ba wanna ce shigar fita zancan ba ko”
tayi murmushi har dimple dinta na lobawa kanta aduqe
”itace”ta fada kanta asunkuye,kallonta abida tayi ta sheqe da dariya kana tace tab,kallonta take kwaia wadda kanta yake cikin tukunya
”ban me yasa baki wa fuskarki makeup ba ko don kinsan ke din mai kyau ce,kyanki yana qara……”
bata iya qarasa zancan ba sakamon ciko pork da abdallah yayi da chips ya cusa ma mamin a baki
tilas ta karba sai davta fara taunawa ta dubeshi
”meye haka abdallah,dure zaka min”
ya marairaice
”mami baki qoshi ba fa,kuma idan ana cin abinci ba’a magana,ki qyale koma mene sai kin qoshi”
dauke kanta tayo ta dubi maryam
”ki duba kan mirrow dina akwai makevup kit ki dauko min yau da kaina zan miki kwalliyar

raka’a shida kacal ta samuyi sallar tarawih a maimakon raka’a goma sha uku davtakeyi,cikin awa daya saiga fuskar maryam din ta canza,zama mamin tayi sosai ta mata make up,abida kanta mamaki ta dinga yi,haka mami ta iya make up mai ma’ana?haka maryam ke da kyau,tun usuli ita din ba maison cika tarkace bace ta makevup a fuska,wannan kaye kayen sai hindatu,kyan da ta yiwa mamin yasa ta ta gaza barinta sai data mata hotuna,ta yi azabqr fita kuwa ahoton

aka gama kuwa a daidai,don gamawar tasu bai wuce da minti uku ba abdur rahim ya kirata gashi a compound din gidan ya samu shigowa bayan tarin tambayoyi da waya da mami ta yiwa securities din kan su barshi ya shigo
”jeki maza diyata ki shigo da shi”mami ta fada tana maida hijabinta data idar da sallar asham
tana qoqarin fita saqo ya shigo wayarta ta zaro tana dubawa,number din abdur rahim ta gani wanda hakan ya sanyata sakin murmushi ta soma qoqarin duba abinda ya turo mata

”ya subhanallah”taji ance bayan taga inuwar mutum a gabanta,da sauri ta daga kanta kana ta duba abinda taji ta taka
qafafan abdallah ne,taja baya kadan da sauri a tsorace,dawowarshi kenan daga sallar asham,sanye da jallabiya fara sol mai gajeran hannu wadda hakan ya sanya dukka gargasar hannunshi bayyana da hular tashi ka fiya naci itama fara,sai ya koma tamkar wani balarabe,kallonta yake kawai wanda har hakan ya bata tsoro,sexy eyes dinshi ya lumshe bisa fuskarta na aecond biyu ya bude

murya qasa qasa yace
”wacce iriyar makauniya ce ke,ki hau qafafun mutum ki taka saboda rashin kunya,idan baki wasa ba zan targada qafafun”tuni idanunta suka kawo qwalla
”kayi haquri ban kula bane”
ya janye shanyayyun idanunshi ya motsa zai wuce,har ta gifta shi yace
”wannan wane irin sakarci ne kwalliya cikin ramadan a irin wannan time din”cak ta tsaya zuciyarta na bugu
”ina zaki?”
”waje zanje…..baqo……”
bai bata damar qarasawa ba ya daka mata tsawa
”oya,wuce ki koma wannan iskancin ba’a gidan nan ba,idan zaki tara mazan ki bari sai a naku gidan”
jikinta na rawa ta wuce ya take mata baya

mami data hangota tace
”a’ah,ina baqon?”kasa cewa komai tayi sai satar kallon abdallah da yayi kicin kicin da fuska ya kuma basar kamar bashi ya korota ba,ya samu gefan mamin yayi zamanshi yana shan ruwan bunun da yasha kayan qamshi wanda mamin ta zuba tana jira ya huce ta sha

”kai abdallah,kai ka dawo da ita ko?”
”eh mami dare yayi me zata fita waje tayi taje ta dauko mana magana?”
”kaga malam baqo tayi yana nan compound ba wani gu zata ba”
”ok,wannan stupid din ita yake jira?,to ki fita mu gani,mami baza a ja mana magana ba agia,ta kwatanta mishi gidansu suje can su hadu”

”kai dakata!banason iskancin banza iskancin wofi,uwarta ne kai ko ubanta da zaka hanata fita ga mutumin da zai aureta,ina cewa jiya kasa bacci kayi sai da ka tasheni ka gayamin rana ita yau akai maka kudin aure?shine zaka hana wasu saboda tsabar son kai,to wallhi ahir dinka ka fita daga sabgar maryamu indai kanason zaman lpy”
saukowa yayi qasa ya sanya gwiwoyinshi a qasa ya kama hannayen mamin
”kiyi haquri mami,wannna ne karo na qarshe insha Allahu da zaki sake samuna da irin wannan laifin,ki yafe min banason shiga fushinki,cikin wata muke mai alfarma”

Sai da ta juya tace da maryam taje ta ahigo da baqon sannan ta kalleshi
”idan kana haka abdallah sai ta dinga jinta daban acikin mu,yin hakan tamkar takura ne agareta,ka gyra pls my son”
”insha Allahu mami”ya fada sannan yayi kissing bayan hannunta

shigowar abdur rahim ya sanya abdallah fita,a nutse suka gaisa da mamin,sosai ta yaba da hankalinshi,shi yake sanar mata maryam tace ita zata fadi ranar da za’a kai kudin aurenta gidansu,ya zabi kwana bakwai tace yayi kusa
murmushi mamin tayi
”maryam manya,kwana bakwai din yayi,Allah ya nuna mana”cikin farinciki walwala da mutuntuna juna suka rabu da mamin ya nufi inda maryam tayi masa masauki

”me yasa abdul kaqi cin komai ne”murmushi ya saki kana ya miqe tsaye yana duba agogon hannunshi,ya dauke idonshi daga agogon ya dan kalli bayanta kadan yasake dauke idonsa
”zan wuce ne maryam,lokaci yayi sai wani jiqon”ya fada agaggauce,a hankali ta waiwaya ta maida idanunta inda taga yana kalla din,abdallah ne tsaye saidai sam ba sashen da suke yake kallo,tuni har abdur rahim ya soma tattakin barin gurin,ta bishi a baya don masa rakiya,ya tsaya cak kana yace
”na gide,bana buqatar ki wahalar min da kanki ki koma ciki,sai haduwa ta gaba?”ya fada cikin sigar tambaya yana daga gira,kafadarta itama ta daga sukayi sallama ta juya don komawa mazauninsu na dazu ta kwashe kayan data shirya masa duk da bai taba komai ba face ruwan,duk da ya bata uzirin cikinshi a cushe yake baya iya cin komai sai da sahur amma bata ji dadi ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button